← Book details Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 128

Sashe 88

Abin Da Ka Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Mustapha yayi fiye da 20 minutes a zaune a inda Maryam ta barshi, koda ƙwaƙwkwaran motsi beyiba, saboda yanda yakejin wani feeling na bijiro masa, se sassauke numfarfashi kawai yake a wahalarce. ganin zaman baze ƙaresaba ya mike da kyar, yana taune lips dinsa ya wuce bedroom ɗinsa. Rage kayan jikinsa yayi ya shige toilet yasakarwa kansa ruwa, kozeji sauƙin abunda yakeji ajikinsa. Suna cikin cin abincin suhailat ta dubi Aunty tace, "Aunty wai nan gidan wa mukazo" batare da Aunty ta kalletaba tace, "gidan freind ɗina ne" da mamaki suhailat tace, "Amma me ya kawo yaya gidan?" Kafin Aunty ta bata amsa mustapha yashigo falon da sallama. a tare suhailat, umaimah da Maryam suka kallesa zuciyar kowaccensu cike da kaunarsa. Maryam ce ta fara janye idonta daga kansa ta maida kan wayar dake hannunta tana amsa masa sallamar da yayi. mikewa suhailat tayi da sauri, cikin daka tsawa Aunty tace mata. "Dawo ki zauna ki ƙarasa cin abincin ki" cikin sangarta suhailat tace, "Aunty nina koshi da abincin kibarni naje naga yaya, nayi kewarsafa over wlh" tabe baki aliya tayi tacigaba da cin abinta. Aunty na ƙara haɗe rai tace, "nace ki dawo ki zauna ko?" Suhailat kamar zatayi kuka, ta koma ta zauna tana kunkuni aranta. becewa kowa ƙala ba, se Maryam dayabi da kallon ƙasan ido ya nufi gurinsu Aunty. Aunty na kallonsa da fara'a tace, "son manya, nayi zaton zakuzo mana yawan sallah ai" murmushi yayi ya kawar da zancen da faɗin. "Kun zo lafiya" "lafiya ƙalau son, ya al'amura dafatan anyi sallah lafiya?" Shafa kansa yayi yace, "lafiya" atakaice yana kallon suhailat data kura masa ido kamar zata cinyeshi ɗanye. Aliya cikin nutsuwa tace, "yaya ina wuni" batare daya kalletaba ya amsa mata, yana jan kujerar kusa da Aunty ya zauna. Mikewa suhailat tayi tsama ta nufo gurinsa da niyyar hugging ɗinsa, wani mugun kallo ya watsa mata saboda gane nufinta da yayi. sanin halinsa da tayi yasata tsaya kamar zatayi kuka tace, "yaya baka kulaniba" kallonta yayi yana ɗan sakin fuskarsa yace, "how are you" "fyn and you" ta bashi amsa da haka cikin farin cikin ganinsa, banza ya mata bebata amsaba. Komawa tayi ta zauna cikin karayar zuciya, fargaba da tsorone suka cika mata zuciya, dan batasan matsayin soyayyartaba yanzu a gurinshi, amma dayake tasan halinsa na miskilanci ko a da canma haka yake mata, seta dauka yanzumma hakane........

Bayan sungama cin abincin suka koma cikin falon, hira suka shigayi da Aunty, gabadaya akan kasuwan daddy ne da kuma ciwon Sadiq, har mustapha yacewa aunty yaso zuwa dubashi amma daddy ya hana, Aunty tace masa. "Ai jikin Sadiq ɗinma yayi sauƙi, a satinnan zasu dawo seyaje ya dubashi a gida." suna cikin hirarne aunty ta dubeshi tace, "karka nunawa suhailat Maryam matarkace a yanzu, kayi duk yanda zakayi karta gane, na gargadi Aliyama tun daga gida akan haka." da mamaki yake kallon Aunty amma bece komaiba. Aunty ta cigaba da magana da faɗin, "saboda banaso Aunty Atika ta sani yanzu, kuma idan suhailat ta sani kamar ta sanine, Allah shine abin tsoro, amma kaji tsoron sharrin mutum ma, kuma ko badan Aunty atikaba, suhailat ɗinma idan tasani hauka zata mana a gidan mutane kasan halinta dai sarai." gyadawa Aunty kai yayi amma yasan dole se suhailat ɗin ta sani ko a bakin su ammi ne. suka cigaba da hirarsu cikin kaunar juna. Niko part ɗina naja Aliya muketa hirarmu cikin nishadi, aliya dabata gajiya se zuzuta kyan dana ƙara takeyi. Suhailat kam tana dakin da suka sauka tana shan baccinta.

Da daddare muna daki nida aliya a part din ammi, wani littafi nake karantawa me daɗi a wayarta, dazu take bani labarin book ɗin, shine nace tabani nakaranta. tanatamun hira Bama saurarta nakeba. Aunty ce tashigo ɗakin, bayan tayi sallama mun amsa mata tace. "Maryam ki tashi ki koma part dinku dare yayifa har goma saura." Batare da tunanin komaiba nace, "Aunty anan zan kwana yau" "nan ina?" Aunty ta tambayeta haka. "Aunty anan tare daku" wani kallo Aunty ta mata fuskarta babu wasa tace, "tashi ki wuce ni, banason shiririta" tashi nayi daga kwancen danake badon nasoba, sedan bazan iya musu da Aunty ba na dubi aliya nace, "taso muje mu kwana tare" kallon Aunty aliya tayi taga ta harareta. girgizamun kai aliya tayi alamun a'a. Nace "dan Allah kizo muje kinji kawata" "Aunty ce tace. "Akanme zata biki, kizo ki wuce ki tafi ke kaɗai" mikewa tsaye nayi da wayar aliya a hannuna. Aliya tace, "ke karki tafarmun da waya mana" ina cigaba da tafiyata nace, "ki bari da safe na baki, na matsu na ƙarasa labarinnan" mikewa tsaye Aliya tayi zatabi Maryam ta kwato wayarta. Dakatar da ita Aunty tayi da faɗin, "bar mata mana, idan dan wayane ga wayatanan kikira, keda baza ki iya hakuraba na dare ɗaya" komawa aliya tayi ta zauna tana faɗin, "to bani wayar taki" mika mata Aunty tayi. Maryam kuwa harta fice daga ɗakin. A falo na tarar da ammi na mata sallama na fice, suhailat ma tana falon tana bacci akan kujera. Tun dazu Aunty tace taje daki ta kwanta, taƙi ita setaga shigowar yayanta sannan zata koma daki, be shigoba kuma bacci ya ɗauketa.
Chapter 88 · 0% Book details