← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 58

Sashe 9

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya halicci Rayuwa da kuma mutuwa dan ya jarabce mu, a cikin wannan rayuwa akwai abubuwa da yawa waɗanda ya ɓoyesu akan gaibu gare mu, dan sanin su ba ƙaramin masifa bane gare mu, akwai farinciki kuma akwai baƙin ciki, akwai aure kuma akwai mutuwan aure ko rashin aure, akwai samu kuma akwai rashi, akwai haihuwa kuma akwai rashin haihuwan, abubuwa da yawa da Allah ya halitto su yayo kishiyoyinsu dan jarabtar mu, kaman dai yanda yayi mace Nana Hauwa'u kuma yayo namiji Annabi Adamu AS, a wannan lokacin kuma ya sanya wa Annabi Adamu AS kwaɗaituwar keɓancewa da Nana Hauwa'u, wannan ma jarabawa ne tsakanin mace da namiji, Acikin mutuwa kuma Allah yayi jarabawa da yawa wanda shi ma duk imaninka zai jarabce ka, akwai zafin fitan rai, akwai kwanciyan kabari, akwai tambayan kabari, akwai tashuwa bayan Mala'ika Israfil ya busa ƙaho, akwai tsayuwan hisabi, akwai bawa Kowa littafinsa, akwai duba ayyukan kowa, akwai hawa siraɗi da dai sauransu, abubuwa da yawa dan mu sani mu gaba ɗaya a kewaye muke da jarabawa, har sai munyi haƙuri mun kuma aikata dai-dai tare da ƙaunar Manzon Allah SAW, in muka shiga aljanna nan kuma sai Allah da kansa yace ga gidan da ya mana sakamako na haƙurin da muka yi da jarabobin sa akanmu, to sai fa nan ne ba jarrabawa in an shiga aljanna dan kuwa magana ta ƙare, tunda idan aka shiga aljanna ba wani abu da za'a yi mai siga da ibada, to jarabawar da Allah ke jarabtar mu da shi ai idan muka yi haƙuri duk cikin ibada ne, ki amshi ƙaddaranki hannu bibbiyu masoyiya,
Banafshaty ba ta inda Allah baya jarabtan bawan sa, wani akan mahaifa, wani akan 'ya'ya, wani akan matan auren sa, wani akan kasuwancin sa, wani ciwo, wani kuma Allah ya bawa wani bawansa daman yin mugun nufi akan ɗayan bawan dan jarabtan su dukan su biyun, wani kuma akan maƙwabtansa, wani kuma akan abokanansa..etc
Duk wanda bai yarda da abu biyunnan ba, waɗanda ke ƙidaye a sharruɗan Addini da kuma Imani, to kina tunanin ya cika musulmi kuma mai son Rahamar Ubangiji?
Banafshaty wannan ita ce jarabawan ki kuma ƙaddaranki, sannan haƙurin da zaki yi shi ne Zakkan ki, a ko da yaushe kalman haƙuri ita ce kowa zai faɗa miki dan kuwa ansan kina kan stakiyan dandamalin gadon jarabawa, kuma duk wanda aka cewa KAYI/KIYI HAƘURI to tabbas ki sani wannan bawan Allah ko baiwar Allahn ansan ya/ta taka wuta, yanda haƙuri ke kai mu aljanna to haka tun a duniya haƙuri ke kai mu stibirin farin ciki da ɗimbin nasarori wanda bamu taɓa zato ko tsammani ba a rayuwa.
Duk wanda ya faɗa miki wata kalma a rayuwanki bayan kiyi haƙuri da kuma ki ci gaba da addu'a, to ki binciki wannan wanda ya faɗa miki kalma saɓanin biyun nan, dan kuwa baya miki kwaɗayin shiga rahamar Ubangiji, ya tabbata ba mai sonki da ƙaunarki ba, domin kuwa addu'a da haƙuri sun isa su miki maganin ko wacce iriyar jarabawa ta rayuwa, duk tsanani yana tare da sauƙi muddin ba wai ka riske makwancinka a wannan halin ba ne, kuma ko da ka riske makwancinka a wannan halin jarabawan bai wuce ba, to shi ɗin ma wani babban nasara ne dan baka san abinda Allah ya shirya maka ba idan ka koma gare sa.

Banafsha ki dage da addu'a, duk da dai na sani kina yi, amma ki ƙara dagewa kuma ki duƙufa sosai ki kai kukanki ga mahaliccinki, musamman cikin sujjadanki, a wajan kina tasbihi ga Allah tasbihi ne na yabo, kuma babu mai son yabo irin Allah, kina tasbihinki ki karanto kukanki Insha Allahu komin nisan rayuwa Allah zai amsa miki, don babu inda bawa ya fi kusanci da mahaliccinsa irin sujjada, dan haka ki dage sosai, in Allah ya hukunta ya yarje ya ƙiramu ɗakinsa mai starki sai mu baje dukkan tulin addu'oenmu ga mai amsawa, in kuma Allah bai nufa ba, to daga nan ɗin ma Alhamdulillahi, don kuwa muddim bawa zai tsarkake zuciyansa da jikinsa sannan ya tunkari mahaliccinsa da buƙata, to ko da kuwa a kwance a gadonsa yayi wannan addu'an Insha Allah sai Ubangiji ya amsa, kiyi haƙuri Banafshaty komai zai wuce kuma zai zama labari kaman ba'a yi ba.
Batun ki shiga duniya ma wannan butulci ne da kuma rashin nuna amincewa da ƙaddaran Allah, dan kuwa na tabbata duk iya yawan starewanki da kamewanki muddin kika shiga duniya to abinda kika tsana kika sa damuwa a ranki dan shi tom ke ma shi za ki jarabtu da shi ko da kuwa bakya so ne, mutanen duniya ba duka ne na kirki ba, kuma ko da kika ce za ki kashe kanki, to ki sani wannan ya fi komai muni dan kuwa duk storon Allahnki, Addininki, iliminki, soyayyan ki ga Manzon Allah SAW, to duk sun tafi a iska domin duk wanda ya kashe kansa to ya mutu kafiri, wanda direct makomansa wuta ne, mu kuma bamu fatan hakan, muna al'umman Annabi SAW wuta ba namu bane, dan girman Allah Banafshaty kiyi haƙuri ki kuma ƙara haƙuri ki duba maganana kin ji masoyiya" Umaima ta gama maganan tana hawaye.

Jikinane yayi mugun sanyi, dan zuwa yanzu ko banu komai to naji sassauci da kuma sanyi a zuciya ta fiye da tunanin mai tunani, kukan ma na neme shi na rasa, dan kuwa duk abinda na sani ƙawata Umaima ta tunatar da ni wanda dama Allah subhanahu wata'ala yace:-

**Ka tunatar domin tunatar wa yana amfanan mumini**

Ajiyan zuciya na sauƙe na dubi Umaima cikin ƙaunanta da naji ya ninku a zuciyata na ce, "Nagode sosai Umaima, Allah ya saka miki da alheri, Allah ya kuma bar mu tare, in Allah ya yarda zan yi haƙuri, zan ci gaba da addu'a, kuma zan rungumi ƙaddarata hannu bibbiyu domin kuwa kasancewa '𝗬𝗔𝗥 𝗞𝗔𝗥𝗨𝗪𝗔 shi ne babban ƙaddaranta, Alhamdulillahi! Na gode Allah na yabi Annabi, kuma na amsa ƙaddarata Insha Allahu ya Rabbi.

Murmushi na sakar wa Umaima na ce, "Masoyiya Umaima dole na dage da karatun musabaƙan nan, dan nima ina kwaɗaice da zuwa ƙasa mai tsarki, mahaifina tun da nake ba'a taɓa bani labarin sa ba sai kawai ni marainiya ce abinda Mami ke faɗamun kenan, ga shi yau har an buɗe baki ance mun ƴar cikin shege, bayan sunan ƴar karuwa, to Alhamdulillahi ni dai ina yiwa mahaifina addu'a, amma ina da buƙatan ƙarawa in ba shi da rai Allah ya masa rahama, idan kuma yana raye to Allah ya haɗa fuskokinmu ko da kuwa gaskiya ne ba ta hanyan halal aka same ni ba, to na yafe musu Duniya da lahira Allah ya yafe mu duka.

Ƙiran sallahn Magrib da aka yi shi ya kaste mu muka miƙe duka muka ɗauro alwala muka koma ciki muka bi masallaci sallah, Ummu na ganinmu taji sanyi a ranta ganin damuwan dake kwance a fiska na ya dai-daita.

Muna idar da Sallah Umaima ta miƙe ta fice, ni kuma karatun Alkur'ani nake yi har dai aka ƙira isha'i, Umaima ta shigo muka ƙara gabatar wa muna idar wa muka yi lazumin mu muka shafa addu'a sannan muka fito duka.

Ummu ta ce, "yauwá yaran albarka ga abinci nan ku zauna kuci ko."

Zama muka yi muna ci muna kallo, duk da dai nikam hannu kawai na saka dan kar Ummu tayi magana, amma Umaima duk tana sane da abinda nake yi, sanin halinane na rashin cin abinci ya sanya bata ce mun kala ba.

Can muna zaune sai ga kuma sallaman Abba da Umma sun shigo, wani irin bugawa zuciyata tayi da na tuna halin Umma Sabeera ga kuma ya Danish a gida.

***
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja, a rahusa mai sauƙi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM

07015870735
WhatsApp ko call

Ko Gmail nawa
[email protected]

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

Dr seeyath (besty lurv)
Heartbeat (ukhtynh)
Deejatou na Marubuciyar sarauniyar kyau.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤

🅿️ 21 _ 25

Lumshe idanuwana nayi, muka haÉ—a baki duka wajan amsa sallaman su Abbaa.
Nana dake zaune a gefena tashuwa tayi da gudu ta nufi wajan Abba ta rungume sa tana faÉ—in, "Sannu da dawowa Abba na."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Yauwá maman Abbaa sannunku ko", mayar da kallonsa yayi kan mu ni da Umaima ya ce, "Ummul-khultum da Faɗimah babu yiwa Abbaa oyoyo ko? Yanzu kam yarana sun girma sun zama budurwaye, an daina mini oyoyo" ya faɗa yana sakar mana murmushi.

Cikin jin kunya nayi ƙasa da kai na ina murmushi, Umaima ma murmushin tayi muka haɗa baki wajan cewa, "Abbaa sannu da dawowa."

"Yauwá ƴan biyun Abbaa, ƴan albarka sannunku ko."

Ummu idanuwanta akan mijinta ta ce, "Alhaji in dai ka biye musu ba za ka huta ba fa."

Murmusawa Abbaa yayi, ya miƙe ya nufi ɗakin Ummu ita ma ta tashi ta mara masa baya, Umma Sabeera taɓe baki tayi ta bi Ummu da kallon banza, sannan ta juyo kanmu, amma kamun tayi magana muka haɗa baki har da Nana muka ce, "Umma sannu da dawowa."

Umma wani dogon tsaki ta ja ta ce, "mstwwww! Iyayen kalen dangi, Allah ya rufamin asiri na zama uwarki tun da dai ni ba karuwa ba ce" ta ƙarishe maganan kaman tana yi da sa'arta ba sa'ar ƴar cikinta ba.
Chapter 9 · 0% Book details