← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 58

Sashe 48

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbaa ma bayani ya yi wa polisawan, suka samu likitan shi ma ya musu bayani, sannan ya faɗa musu Soja ne ya shiga lamarin shiyasa ya amshe ta ma, samun Bunayd suka yi, cikin girmamawa suka gode masa, amma Bunayd gyaɗa musu kai kawai yayi bai ko kallesu ba, sannan a gadarance ya ce, "Ku tabbatar kun mata duk wani hukunci yan da ya kamata dai-dai, she attempt to commit a murder, dan haka idan na ji ba'a mata hukuncin da ya kamata ba, ku ne za ku yi facing na hukuncin" yana gama magana ya miƙe ya yi gaba.

Polisawan amsawa suka yi, sannan suka tafi, tare da yaya babba da Abbaa suka koma aka ɗau Umma da ta farka zuwa lokacin da mugun ciwon kai, daman tana gidan yaya babba ne, tana kallon su ta miƙe tana muzurai, Abbaa staki kawai ya ja, ya ce, "ki je na sake ki, kuma aure ki sani ba gudu ba ja da baya, ke kin fita a banza, ita kuma za ta shigo hankali kwance."

Umma za ta yi magana, polisawa suka tisa ƙeyarta sun ƙi bata daman magana, yaya babba gaba-ɗaya yasan Umma bata kyauta ba, abin bai masa daɗi ba, amma dai uwa-uwa ce, sai ya ji ba daɗi sosai, har ya ji haushin Danish dan shi ya ja komai, ya stani yarinya kuma ya dawo ya ce yana son ta, bayan shi ya ƙara ingiza Umma har ta musu mugun stana, yanzu ga shi abinda ya faru."

Abbaa gida ya koma, ya faɗa wa Ummu abin da ke faruwa, Ummu hankalinta yayi mugun tashi, Abbaa ya ƙira ya Sadeeq akan ya dawo da Banafsha gida, tun da dare ta yi, kuma ana kula da Mami, ya Sadeeq ya amsa.

Banafsha na tsugunne gaban É—akin da Mami take, sai ga ya Sadeeq, yana zuwa ya ce, "sistor ki zo mu je gida ko, zuwa safiya sai mu dawo."

Tura baki Banafsha ta yi ta ce, "Ni dai ina nan da Mamina ba in da zan je."

Ya Sadeeq yayi-yayi ta ƙi, dan haka dan dole ya ƙyaleta, dan ko da ya faɗawa Abbaa ma cewa yayi a ƙyale ta.

Bunayd ma an yi da shi ya koma hotel tun da Abeed É—in na huta wa, amma ya ce yana nan kawai, ba dan sojojin sun so ba, haka suka mara masa baya kwanan asibiti ya same su.

Bunayd shi ba kwanciya zai yi ba, dan haka zama yayi kawai a É—akin da Abeed É—in ya ke, idan ya gaji kuma ya tashi ya fito.

Banafsha kuma likita ya faɗa mata ta shiga ciki ta kwanta, tun da daman Mami ita kaɗai ce a ɗakin, yau Banafsha ta ga daren da bata taɓa gani ba a rayuwanta, don kuwa baccin ma gaba ɗaya ta kasa, ya ƙauracewa idanuwanta, haka ta dinga juyi, ƙarshe alwala ta ɗauro ta ta da sallah, sai da ta yi nafilfiulunta sannan ta miƙe ta fito.

Mutumin da Banafsha ta gani a tsaye shi ya storitata, za ta koma ciki sai ta jiyo daddaÉ—an muryansa na faÉ—in, "storita kika yi?"

Banafsha tana jin muryan ta gane mai yin turanci ɗazu ne, tura baki tayi ta ƙarisa fitowa ta zauna, Bunayd ma ya ƙariso wajan ya zauna ba tare da rata sosai stakaninsu ba, wayansa ya fidda yana lastawa ya ce, "scared girl."

Cunna baki ta kuma yi ta ce, "Ni ba mastoraciya ba ce, ni bana storon kowa sai Allah, sai na yi kokawa da aljani ma lafiya lau, duk wanda ya mini rashin kirki nima masa zan yi ba storo."

Taɓe baki Bunayd yayi ya ce, "Kuma kina gani aka yi wa Mom naki wannan abun ba ki ɗau mataki ba, ashe kina da kirki."

Banafsha da ta tuno abinda Umma ta yi, ai a masifance ta ce, "wallahi na buga mata abu a kai ita ma sai da ta suma, sam-sam ban da kirki ban san shi ba, bani da mutunci idan aka mini rashin mutunci, ni sai na stigewa mutum gashin mugun waje ma ba ruwana."

Murmushin gefen baki Bunayd yayi, bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da danna wayansa, Banafsha sai mita take ita ɗaya, da ya gaji sai ta ɗago ta leƙa fiskan Bunayd, zaro idanuwa Banafsha tayi tana faɗin, "Mutum ko aljan", a ranta, ganin irin kyawun Bunayd.

Bunayd a jikinsa ya ji tana ƙare masa kallo, yastine fiska yayi kaman wanda ke yi wa General shagwaɓa, ya ce, "Bana son kallo da yawa."

Banafsha banza ta yi da shi, tana ta satan kallonsa, ita ba ta shiga harkan maza, amma dai wannan ta kasa É—aure masa fiska ma, ga shi kyakkyawa kaman Malam Abbonta.

Bunayd haɗe fiska yayi a zuciyansa ya furta, "wannan yarinya ta ci sa'an condition da nake ciki, if not da ita ma ta amshi nata rabon na abinda nake yi wa masu mini kallon ƙurilla, da masu taɓa ni babu sadaki" yana gama magana a zuciyansa ya ja guntun tsaki tare da miƙewa ya shige ɗakin da Abeed ya ke.

Banafsha taɓe baki tayi, ta ce, "Allah kai mu safiya za ka san ni ka ja wa tsaki", tana gama faɗa ita ma ta miƙe ta shige ɗakin da Mami take, tana kwanciya kuma ba jimawa bacci yayi gaba da ita, a ɓangaren ACM Bunayd kuwa idanuwansa biyu haka ya kwana, dan ƙarshe ma alwala ya ɗaura yana ta nafilfiulunsa har asuba ta yi.

Su Umma a police station, tun cikin dare aka mata statement da komai na attempt to commit murder, da yake tana cikin haushi har lokacin tuni ta amsa musu ita ta yi kuma da saninta ta yi, duk da dai ta amsa amma ta jibgu, kamun aka bar ta sai gari ya waye.

Abbaa yan da ya ga safe haka ya ga dare, gaba-ɗaya abun ya damesa ba kaɗan ba, shi ji yake sakin da ya yi wa Umma bai wadatar ba, da ace ya sani da ya haɗa mata Juni da majina tukunna, ƙwafa kawai ya kwana yi, Ummu ta ba sa baki amma ya ƙi sauraranta ma, dan ko da ta nuna a bar maganan auren banafsha da Danish, Abbaa kaman zai dake ta haka ya hayayyaƙo mata, dole taja baki ta yi shiru tana faɗin Allah ya huci zuciyansa.

Umaima tun da ta ji labari hankalinta ya tashi, kwana ta yi tana kuka har ciwon kai mai stanani ya rufe ta, tausayin Banafsha da haushin halin Umma su suka dame ta, gaba-ɗaya ji take ina ma ana sanja uwa da wallahi sai ta sanja nata uwar, ita sai yanzu ma take ganin ƙoƙari da tawakkali irin na Banafsha, ashe haka ake ji idan mahaifiyar mutum na aikata ba dai-dai ba, ji take kaman ta kashe kanta ta huta, sai ɓarawon bacci ne ya samu nasaran yin gaba da ita, washe-gari kuma ko ta kan magana makaranta bata bi ba, tana taya Ummu aiki, ta shirya ita ma za ta je asibitin.

Abbaa da Ummu da Umaima suka kama hanyan asibiti, aka bar gida ba kowa, dan Nana bealkysou ta fi zama a gidan yaya babba ita kam yawanci, tana taya Hindatu aiki saboda cikin jikinta da ya girma.

Yaya babba sammako yayi a police station amma an ƙi barinsa ya kalli Umma, tun da ta amsa laifin ta shikkenan aka killace ta, dan gudun kada ta yi yunƙurin kashe wasu ma, yanzu haka ma shirye-shiryen kai ta prison suke kamun a fara shari'anta a yanke mata hukunci.

Ya Danish da yake can bai san wainar da ake toyawa ba, babu wanda ya ƙira sa, babban yaya na fushi, Abbaa kuma ba ya son ya sanar da shi dan kada ya ce ya fasa, saboda yanzu yan da Abbaa yake ji ko Danish ya fasa, muddim yarinyar ta amince to sai ya aureta ko zai mutu, dan yafi son ya nunawa Umma bata ita ba.

Da sassafe Bunayd ya sa aka yi arranging na komai yanda ya kamata dan da wuri yake son su wuce, amma so yake kamun ya tafi ya bar wa Faɗima rabonta, na kallon ƙurillan da ta masa jiya, shi ka'idansa ne, mace ba za ta kula stabgansa ba dai-dai da ƙwayan zarra.

Banafsha kuwa saboda ba ta yi bacci da wuri ba, sai da ta makara, gari yayi haske fayau ta tashi, lokacin shida da rabi ta yi ma, a gurguje tayi alwala ta yi sallah, azkar nata da komai, tana idarwa kuma su Umaima suka shigo, Umaima ƙarisawa tayi jikin Banafsha ta ce, "Dan Allah Masoyiya ki yi haƙuri, ni ma ban ji daɗin abinda Umma ta yi ba, amma tun da tana hannun hukuma da sauƙi, Allah bai wa Maminmu lafiya."

Hawayen da ya zubo wa Banafsha ta share, tare da amsawa da Ameen, gaishe da Abbaa ta yi ya amsa cikin tausayinta, Ummu ma sai ɓoye nata hawayen ta yi, sannan ta amsa gaisuwan Banafsha ta ce, "zo ki ɗiba abinci ki ci ko yarinyar Maminta."

Banafsha ɗan Murmushin yaƙe ta yi kawai, ta ce ba yanzu ba, suna zaune cikin jimami har sai wajan ƙarfe tara na safe sannan ta karya, bayan ta cika cikinta ta ja hannun Umaima suka fice a ɗakin.

Umaima dai bin Banafsha tayi har ta ga sun nufi wani É—aki, dai-dai za su shiga sai ga likita nan ya fito ga Bunayd a bayansa, shi likitan yana kallon Banafsha sai ya murmusa ya ce, "good morning annoying doctor."

Banafsha murmushi ta saki tare da amsawa, Umaima ma suka gaisa da likitan da fara'a.

Bunayd da ke bayan likitan, haÉ—e fiskansa yayi ya fidda wayarsa yana lastawa, Banafsha a yanayin rashin kirki ta ce, "Sannunka bawan Allah ya mai jiki?"

Banza da ita Bunayd yayi bai ce komai ba, ta kuma magana shiru bai ko ɗago ya kalleta ba, sai da ta yi na uku sannan ya ɗago rai a haɗe ya wasta mata kallon banza ya ja guntun tsaki, Banafsha idan ran ta yayi million to ya ɓaci, saboda masifa har vibrating take yi, Umaima na gefe na ganin ikon Allah ita da likita.
Chapter 48 · 0% Book details