Sashe 43
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe-gari asabar sai da muka shirya muka je tahfiz sannan da muka dawo muka wuce College, yau class É—aya kawai muke da shi, dan haka da wuri muka dawo, duk da mun ji ka-ce-na-ce akan za'a manna result ranan, Umaima ta ce mu jira, ni ko na ce bata isa ba gida za mu dawo, haka ta biyoni muka nemi mashine muka nufo gida.
Muna tafiya a mashine na ce, "Masoyiya ban faÉ—a miki yanda muka yi da Malam Abbo ba."
Umaima hararana tayi ta ce, "Daman ai iya gudun ruwanki na staya gani, za ki faÉ—a mini ne, ko har yanzu bata yi stami ba balle na ji."
Murmushi nayi na ce, "faɗa miki ai kinsan dole ne, ni bana miki ɓoyel-ɓoyel....." Nan na kwashe duk yanda muka yi da Malam Abbo na faɗa mata.
Umaima murmushi kawai ta yi ita ma, ta ce, "Yanzu haka kika ce masa masoyiya?"
ÆŠaga kai nayi na ce, "eh ai gaskiya ce, ni ba maganan aure a gabana, haka kawai za'a aure ni a dinga faÉ—a mini magana ko miji ko Æ´an uwansa, to ba zan ma fara ba, daman aka ce da gabar na bayar gwanda gabar na hana."
Murmushi Umaima ta kuma yi ta ce, "To Allah ya kyauta, tun da dai bakyajin shawara ta Allah da Manzonsa, to ni ba abinda zan ce, Allah rufa mana asiri kawai, amma dai aure ai abin so ne, kuma mutunci ga ko wacce ƴa mace kema kin sani, to stakani da Allah ma wa ya ƙi ni'imar aure? Ai ko ba dan ci da sha ba kana samu a gidanku, to ko dan John-thomas ai ka yi, indai Allah ya nufa kuma ya kawo miji to aure shi ne rufin asirin ko wacce ɗiya mace, ni wani gulma na ji ma nake son miki ke ma, bansan ko kin ji ba dai."
Yau ba mu ce mashine ya kai mu ƙofan gida ba, sauƙa muka yi muna tafiya muna kan hiranmu, cewa nayi, "Gulman menene haka?"
Umaima ta ce, "kinsan ashe dukan da Umma ta mini wai har da kishi, tana dukana tana surutu ni bana fahimta da yake na jibgu, sai ranan nake jin Abbaa na magana wai saboda ya ce zai auri Maminmu ne, kuma sai ya aure ta."
Ajiyan zuciya na sauƙe dan na tuna abinda Mami ta yi ranan dan na mata wannan maganan, kallon Umaima nayi na ce, "To ke kina goyon bayan auren kuwa? Dan ni gaskiya ina jin ta Ummu kaman dai bai kamata ba, kar ta ce Mamina ta ci amanarta, dan nima na ji gulman."
Murmushi Umaima ta yi ta ce, "chaɓ! Ai ba ki sani ba masoyiya, Ummu kam ta amince kuma kaman ma har da shawaranta, nidai wallahi zan so haka, shikkenan mu koma zama gida ɗaya, ba wanda zai hanani zuwa gidan Mami ko miki magana tun da mun zama ƴaran baba ɗaya, kin ga ko aurenmu ma sai Abbaa ya mana tare."
Murmushi nayi na ce, "ta kwana gidan sauƙi, Allah taimaka ya tabbatar da alkairi, nima zan dage da damun Mamina ayi ma da wuri kowa ya huta."
Dariya muka yi dukkanmu cikin farin ciki muka cigaba da tafiya, yau ma dai kaman jiya a ƙofan gida muka samu Ya Danish a zaune, ba tare da na kallesa ba na yiwa Umaima sallama na juya na wuce gidanmu, Umaima gaishesa ta yi a storace, amma sai ya amsa bakomai kaman bai ganta tare da ni ba, hamdala tayi ta shige gida.
Ya Danish ci-gaba yayi da kallona har na ɓacewa ganinsa, sannan ya sauƙe nauyayyan ajiyan zuciya a fili ya ce, "jarabawa kenan, ko iya haka Allah ya saka miki abubuwan da nake miki, tun da ga shi kin hanani sukuni kin hana zuciyata nustuwa."
Ni kuwa ina shigewa gidanmu na samu ba kowa a palourn, ina ƙoƙarin shiga ɗakina aka yi sallama, juyawa nayi na amsa jin muryan namiji, wani ɗan matashi ne, a mutunce muka amsa sai na ce, "wa kake nema bawan Allah?"
Matashin yana murmushi ya ce, "Ko kece Hajiya Ramla?"
Kallonsa nayi da kyau, har zan ce a'a sai na ce,."Eh! ni ce, na faÉ—a ina murmushi dan kada yayi kokonto.
Washe baki matashin yayi ya ce,."Daman layinki aka bani, aka ce kina ji da al'amuran lalura tamu ta maza,. shiyasa na zo" ya faÉ—a yana murmushi.
Murmushi nayi inajin kaman na ɗura masa ashar, amma na haƙura dan naci riban zance, na ce, "To fatan da nauyinka ka zo, ina nufin maganan kuɗi."
Matashin murmushi yayi ya ce, "Hajiya dubu goma ce da ni a taimaka mini."
Wani irin gululun baƙin ciki ne ya turnuƙe ni, wani irin kallon banza na zabga masa, tare da fara zaginsa tass!tass!, haka na mishi na faɗa masa baƙaƙen maganganu sannan ba shiri ya juya, nima juyawa nayi ciki kaman taƙaici zai hallaka ni.
Wucewa ɗakina nayi da haushi kaman ya kashe ni, nasan da yasan ni yarinyarta ne, to da shima ƙira na da sunan da na tsana zai yi, duk wani mai zuwa wajan Mami nasan mai zan masa yanzu, dan insha Allah Mamina aure za ta yi.
Abubuwan da zan yi na yi na kwanta, dan haushi ko zuwa gaishe da Mami ban yi ba, balle kuma na kula abinci, baccina nayi ishashshe sai da lokaci ya tafi na tashi, alwala nayi tare da yin sallahn la'asar, fitowa nayi na samu Mami na aikinta, ina tura baki na mata sannu ta amsa.
Mami ta ga yanda nayi kicin-kicin da fiska, sanin halin rigima irin nawa sai bata ce mini komai ba tun da bata san abinda ya faru ba, haka ni kuma na gaji dan kai na naje na É—iba abinci na ci, ina ci Mami ta murmusa ta ce, "yunwa ai ba pendon mutum ba ne ko gwaggonsa."
Tura baki nayi ina gamawa na ce, "Mami, ashe Umaima bata da lafiya ne shiyasa bata je makarantar ba, kuma har kwanaki suka yi a asibiti."
"Ashsha! Subhanallahi! Allah ya bata lafiya, ai ba mu da labari, in Allah ya yarda zan shiga na duba jikin nata, kwana biyu ma Ummunku bata leƙo ba, tun da ta zo ta duba jikinki" faɗin Mami tana aikinta.
"Ameeen Mamina, yauwa Mami mun ji labarin wai za'a manna mana result, a taya mu da addu'a Mami Allah sa mu ga alkairi, daman Alhaji ya ce zai mini kyauta ma" na faɗa ina murmushi dan jira nake kawai ya tambayi abin da nake so, ni kuma na faɗa masa abinda na jima da ƙudurcewa a rai na.
Mami ta ce, "To Allah ya sa ku ga alkairi, mu kuma Allah sa mu ji alkairi, Alhaji kam yana can wata ƙasar ma ai."
Tura baki nayi na ce, "Ai dai zai dawo Mami, kuma nasan zai mini kyauta na."
Murmushi Mami tayi ta ce, "To Allah dawo da shi lafiya."
Da, "Ameen na amsa."
Hira muka dinga yi da Mamina, amma ko sau É—aya bata ambato Malam Abbo ba, balle na ji ko ya faÉ—a mata wani abun, ganin haka sai na share lamarin nima, sai da na taya Mami aiki sannan na shirya tafiya makarantar yamma.
Æangaren Ya Danish dai aiki ya kallesa, bai ankare ba sai ga shi wankin hula na neman kai sa dare, yanzu gaba-É—aya baya da aikin da ya wuce zama a waje yana jiran ganin giftawan Banafsha, ga shi tun zuwansa bata je ko Æ™ofan gidan su ba balle kuma a kai ga ta shiga, shi abin ma damunsa yake yi, ga shi Abbaa ya tuna masa saura musu sati biyu su kawo mata su yake jira ko ya aura musu ko ma wacece, Umma tun zuwansa ta bi sa da maganan tun da yana da budurwa yayi magana sai a tura, ko kuma ya koma Camaroon ya dubo a cikin yaran yayyunta ko akwai wacce ta masa, amma nan ma Danish yayi shiru abinsa, shi damuwansa kawai rashin sukunin da zuciyansa ke ciki game da Banafsha.
Umaima ta fito a gida ta samu Ya Danish zaune a ƙofan gida, ganinsa sai ba ta yi gigin ko bin hanyan gidan su Banafsha ba, duk da bata kalli ta fito ba, ta juya za ta tafi sai ya ƙira ta, juyowa Umaima ta yi ta ce, "Ga ni yaya."
Ya Danish ya ce, "Ita mara kunyar ƙawar taki ba za ta je makaranta ba ne?"
Umaima dai a storace ta ce, "Nima ban sani ba yaya."
Staki Danish yayi, ya buɗe baki zai yi wani maganan sai ga Banafsha ta fito, a ɓoye kada Umaima ta gane ya sauƙe ajiyan zuciya tare da cewa, "To sai ki tashi ku tafi ai tun da ba kya ji, kuma ki tabbatar kin kula sosai."
Umaima miƙewa tayi a storace ta bar wajan, suna tafiya da Banafsha ta sauƙe ajiyan zuciya ta ce, "Masoyiya ba za ki ce mini sannu ba."
Taɓe baki nayi na ce, "akan me?"
Hararana Umaima tayi ta ce, "Ba ki ga ya Danish da ya stayar da ni bane, wai tambayana ya ke ba za ki je bane, na ce su ya Danish an fara dawowa hanya, ya fara gane Annabi ya kafu, yanzu zan samu peace of mind, dan yanzu ya zama miskilin dole ma."
KafaÉ—a na É—age irin ko a jikina É—in nan, na ce, "shi ya jiyo " daga haka ban kuma cewa komai ba, har muka isa muka yi karatunmu muka dawo.
Mun dawo ma a ƙofa muka samu Ya Danish, nan kowa ya kama hanyan gidan su.
Da dare muna zaune muna kallo da Mamina sai ta dube ni ta ce, "FaÉ—ima."
Hankalina na kan kallo na ce, "na'am Mami."
"Ina son ki bani hankalinki, za mu yi magana mai muhimmanci."
ÆŠauke idanuwana akan TV nayi, na ce, "Ina sauraranki Mamina."
GyaÉ—a kai tayi ba ko alaman murmushi a fiskanta ta ce, "Ina son ki faÉ—a mini ya kuka yi da malaminki, da ya faÉ—a miki tasa maganan ke me kika faÉ—a masa?"
Ni tun da naga Mami bata mini maganan Malam Abbo ba, tun jiya sai na mance da kashinsa ma, amma jin tambayan da ta mini yanzu sai na cunna baki na ce, "Ni ba abinda na ce masa."