Sashe 39
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bunayd taɓe baki yayi ya ce, "Ina ruwana da Mom balle dan za'a mata kishiya ya dame ni, ni ai so nake mu yi maganan da Papi naji idan gaskiya ne to ni na ɗau nauyin kayan aure da sadaki da komai ni zan masa, Allah sa ya samu wacce ta fi Mom hali mai kyau."
"To me damuwanka da ka ce Majeeder ce ta ɓata maka rai" faɗin Abeed yana murmushi.
CAS ya ce, "Wai ƙawar da za'a zo mata da ita ne take cewa da sai na auri yarinyar dan ita ma har musabaƙa suke kuma ta ɗaya ta zo, ni ina ruwana da Ustaziya, ai Ustaziya sai ustaz, mu dai da muke ƴan jagaliya sai mata ƴan irin mu."
Dariya ishashshe Abeed yayi ya ce, "To me abin damuwa a nan? Ai naga kai ma ɗin haddan ƙur'ani ne a kanka, Kuma abin addini babu wanda ba ka ƙoƙari a kai, to kuma duk da hakan ga ka ɗan jagaliya, ja'iri ɗan gidan General ba, to dan tana da ilimin addini mai zai sa ta zama ba yanda kake so ba, ni har naji haka kawai ta shiga rai na, ba dan ina da tawa ba, ai da na yi wuff ta ita."
Staki Bunayd ya ja, ya ce, "Sai kuma ka yi ai, ni dama ji nayi na staneta ma, dan haka sai ka yi ta biyu da ita."
Dariya Abeed ya saka, Bunayd ya taɓe baki ya ce, "sunan wani wai sallau, wa ya ga saliha da ta zarce, ni wayayyiya nake so wacce dai ba jahila ba, amma dai addini bata mata overdose ba, dan haka idan ta so ma zan juye mata na kai na, kawai ta zama ba nistasttiya ba, kuma ba ta gari ba, ba saliha ba, kuma ba kamila ba, indai ita musulma ce mumina shikkenan, kai ni fa tun da Allah bai haramta auran ahlul kitab ba, to zan iya auren alhul kitab indai ta waye yanda ya kamata, kuma ta san rayuwa."
Dariya Abeed yayi ya ce, "Gaskiya Musulmin É—an jagaliya É—an gidan General, kana abinda kake so, to wa ya ce maka yanzu akwai nagari? Ai kowa tafiya haka kawai yake kaman É—an iska a gantale, ai duniyan yanzu ba'a niste take ba balle a samu wani na gari, kowa É—an iskan kansa ne kawai shiru ake, yanda rayuwa ta zama ai kowa ba dan storon Allah ba sai ya koma bariki iskanci ba mai yin aure, ko kuwa a fara fashi da rana tsaka, kai dai addu'a za ka yi dan ba'a hijabi kamila take ba, sai ka dage baka son salihar mace kuma sai ka ga wacce ka samu É—in duk da a zahiri ba saliha ba ce, amma ba lallai ta maka abinda kake so É—in ba, kuma sai ka ga salihar ta maka dunuyancin da kake so."
Bunayd murmushi yayi ya ce, "Na dai gane me kake nufi, wato dai so kake ka ce kamilarka tasan rayuwa, to ba dai zan sauya maganana ba, atou tantiriya nake so."
Abeeb murmushi yayi ya ce, "Ko ma menene kai ka jiyo, ni dai na ce Allah baka mace tagari saliha mar'atussaliha" ya ƙarishe yana dariya.
Bunayd ya ce, "Ba Ameen ba dan uban mutum."
"To yaushe za mu haÉ—u ne? Kada na zo ka ce kana hutawa na san ka da renin hankali" faÉ—in Abeed.
Bunayd ya ce, "Yau ba inda zan je kuma ba wanda zan saurara hutawa zan yi muna hiranmu da Majeeder, Papinmu zai ƙara aure, za'a yi wa Mom tamu kishiya ka ga sai mu fara shiri."
Dariya Abeed yayi ya ce, "ka ji É—an banza yaro mara taya mamansa kishi ba.."
Hiransu suka yi suna ta kwalala dariya, har suka yi sallama Bunayd ya kwanta baccinsa.
Kowa hutawa yayi ba wanda ya je ko ina, su Suhail da Nabeel suna sashinsu, Bunayd kuwa yana maƙale a sashin Affa General hankalinsa kwance, ko sashin Papi bai je ba, shi kuwa Papi ya bari su huta tukunna, bai je sashin Affa ba kuma bai nemi su zo ba, ita kuwa Hajiya Sa'adatu tana cike fam kaman za ta fashe, mutum da yaronsa an mallake masa shi, yaro yana Lagos yana wajansu, ya zo ma yana sashinsu, ko zuwa ya gaisheta bai yi ba balle ya nemi albarkan ta, sai mita kawai take yi, kuma ga Majeeder ma ta je wajansu ta maƙale, Papi kuwa ko ta kanta bai bi ba yana yin abinda ya damesa ne kawai, dan shi akan haka ba ya ganin laifin Bunayd, ko me yayi ita ta nema tunda tun farko ita ma bata sauƙe nata haƙƙin na mahaifiya ba.
Sai washe-gari bayan sun karya kowa ya yi wankansa ya ci kwalliya kaman masu zuwa dinner, sannan dukkansu suna nufi sashin Papi, CAS da farko ya ce ba inda zai je, sai da Affa General ya nuna za su ɓata sannan ya yarda zai je, amma dan Papi zai je ba dan Mom ba.
Bayan sun shiga kowa ya samu waje ya zauna, Papi sai murna yake ganin dukkansu da iyalansa ga su, sai yake ji a ransa ina ma har da Ramlatunsa da sai ya fi haka farinciki.
Mom sai wani shan ƙamshi take, tana kallon banza wa Momsee, ita dai Momsee ko a jikinta dan bata san ma tana yi ba.
Taro CAS Bunayd ya buɗe musu da addu'a, duk suka gaggaisa, shi ma ya gaishe da Mom, ta amsa a daƙile tana cewa, "tunda an mallakeka ai dole ka dinga gaishe ni kaman ba ni ce na stugunna nayi naƙudanka ba."
CAS bai ce komai ba, kuma hakan ya yiwa Papi da Affa daÉ—i, Papi ne ya kalli Mom ya ce, "Sa'adatu ki iya bakinki."
Mom kawar da kai tayi kawai.
Papi faɗa ya yiwa yaran sosai, ya musu nasiha, Affa General ya faɗa wa Papi abinda Suhail yayi na ƙin aikin soja, sannan ga Nabeel ma yana son bostarewa.
Murmushi Papi yayi ya ce, "Wannan ai stakaninsu da mara jin yayansu ne General ba sai ka sako ni ciki ba."
General ya ce, "ai my Man ya musu magana sun ƙi ji."
Bunayd shafa kai yayi yana kallon Papi yana danne dariyansa, su Nabeel kuma dariya suka yi dan sun san indai dan Affa General ya kare yayansu ne, to ba abinda ba zai ce ba.
Papi ya ce, "To Shikkenan tun da sun ƙi jin nasa maganan, sai a ƙyale su kawai su yi kasuwancin, shi Bunayd ɗin ai yayi soja ya gajeka sai ka godewa Allah, nima a bar mini yarana su yi kasuwanci irin nawa su gaje ni."
General murmushi yayi ya ce, "Shikkenan ai tunda ka ce haka yaya, Allah taimaka ya basu sa'a."
Duk suka amsa da Ameen, Nabeel farinciki kaman yayi stalle, ya ce, "Papi Allah bar mana kai."
Affa General ya ce, "Ni kuma Allah ya kashe ni ku huta ko?"
Bunayd miƙewa yayi ya ce, "Ai General kai ne ma mai lasting ɗin, Allah bar mana ku ya ƙara girma ya saka muku da aljanna, Allah bar mana General da Momsee kawai, Papi kuma ni zan masa gudumawa" yana gama faɗa ya fice.
Papi dariya yayi, dan yasan ba zai wuce Majeeder ce ta shafawa yayan nata ba, su General dai dariya suka yi ba su gane nufin CAS ba, Mom kuwa ƙwafa tayi kawai, duk da bata shaƙu da Bunayd ba, amma yanzu ƙaunar yaronta take yi, bata jin za ta iya faɗan wani mugun abu a kansa balle ya shiga wani hali tunda ta haife sa komin yaya bakinta zai iya kamasa, sai dai idan mugun fata yake mata ba kishiya to zata nuna masa ita ce mahaifiyarsa tana da iko da shi kuma.
Wuni suka yi cikin nishaɗi, Papi da Affa sai ƙara tattaunawa suka yi akan abinda ya kamata.
Sai da su General suka yi sati guda, sannan suka tattara suka koma Lagos, Bunayd ma ya bi su dan sun gama maganan komai na bikin da Abeed, yanda komai zai tafi, dan a ranan da suka koma Lagos a ranan Abeed ma ya wuce Adamawa.
Papi sai sati na sama zai yi tafiya nasa, amma kuma busy ya ƙi barinsa ya je ya kalli masoyiyarsa kamun ya tafi tunda har wata biyu zai yi, sai waya kawai suka yi ya tura mata duk abinda ya kamata, kaman yanda ya faɗa dai bai ƙara mata maganan aure ba, sai dai ya mata faɗan ta kula.
Majeeder ta bi su Affa General sun koma tare, Hajiya Sa'adatu kaman za ta haÉ—iye rai dan masifa, Alhaji kuwa ya ce tunda yarinyar sa ce shi ya ga daman ta bi su, idan abun bai mata ba ta yi zuciya ta haiho wata yarinyar ko wani yaron, Hajiya cikin masifa ta ce ita ta gama haihuwa da shi idan ya ga dama ya sayar da yaran.
Papi ko sati guda bai yi ba saboda ɓaci ran da Hajiya ke cusa masa, haka ya tattara ya tafi tafiyansa abunsa, Suhail ma bai kai sati ba ya koma Turkish ɗin sa, Nabeel kuwa Bunayd ya masa komai da ya kamata a Spain ya ci-gaba da karatunsa a can, shi ma yana zaune a gidan Bunayd.
Rayuwa na tafiya ta ko wani ɓangare lafiya sai godiya ga Allah inda yanzu haka auren Abeed saura sati guda, kuma CAS Bunayd ya shirya tare da su Suhaila, Ramla, Majeeder da Nabeela duka ya taho da su, sun ce su ma za su zo da bikin.
Suna isowa yayi magana da Abeed ya kai su Majeeder gidan su Nusaiba Amarya, ta tarbe su hannu bibbiyu, duk anko da ake da komai Bunayd ya yi musu, ana fara shagalin biki kuwa kullum da kansa yake kai su wajan event É—in da za'a yi kuma ya basu kuÉ—i a hannunsa, duk abinda ya ke yana zuwa da sauran abokanansu da suke gari, idan ka ga shungullan da Bunayd ke yi za ka É—auka shi ne Angon, sosai Bunayd yake da kirki kuma ba shi da girman kai.