← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 58

Sashe 40

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau take Thursday wanda a washe-gari juma'a za'a É—aura aure, kuma sai washe-gari Ango zai zo, yana can Adamawa a wani daji gaba da Michika kamun a isa Mubi, shi da abokanan aikinsa suna fama da Æ´an ta'adda masu addabar mutane sai dai mu ce Allah ya É—aura su a kan su.

Ɓangaren Amare yau walima ake yi, Bunayd ya kai su Majeeder da suka sha Arabian gown's suka shuka yi kyau Masha Allah, yana sauƙe su ya miƙa musu kuɗi ya ce, "Ku ji wa'azi mai kyau kuma ku yi aiki da shi."

Suhaila ce ta yi dariya ta ce, "yaya dama ai indai ka ji wa'azi dole ka yi aiki da shi, musamman idan ka zo dan wa'azin ne."

Bunayd girgiza kai yayi ya ce, "wa ya faÉ—a Miki? Ai da yawa mutane suna jin wa'azi ne kawai ba aiki suke da shi ba, a cikin malamai wasu masu yin ma ba wai suna yin abinda suke faÉ—an ba ne, shiyasa aka ce ka yi abinda Malam ya ce ba abinda ya yi ba, dan haka ku É—auka kuma ku yi aiki da shi."

Nabeela murmushi tayi ta ce, "Inshà Allah yaya za mu ɗauka mu yi aiki da shi."

"Good! Nabeela my love" Bunayd ya faÉ—a yana murmushi.

Majeeder ta ce, "yaya ka zo da wuri ka kai mu yawo."

Bunayd ya ce, "ku mastalanku kenan ba'a haÉ—a hanya da ku, yara sai son yawa, to driver ne ma zai zo ya É—auke ku ba ni ba" yana faÉ—a ya yiwa motansa key ya tafi.

Duk tura baki suka yi suka shige, sannan suka samu waje suka zauna, wa'azi ne ake mai kyau mai kuma rasta jiki, wanda ba iya Amarya zai amfana ba, duk wata mace da ta ji ta yi aiki da shi to zai amfane ta duniya da lahira, dan misali ake mana da rayuwan da Nana Faɗima AS ta yi a gidan mijinta sayyadina Ali AS, dan haka mata wannan kyakkyawan tunatarwa ce gare mu, ki duba Allahn da ya ce a zauna a gidan miji a yi haƙuri, ki kuma aro halayyan Nana faɗima AS za ki ji daɗin zaman gidan miji, kuma za ki yi alfahari da hakan duniya da lahira, Allah ya sa mu dace, ya ƙara mana zaman lafiya a dakunanmu, ƙannenmu da yayunmu, da yaranmu, da iyayenmu marassa aure duk Allah ya haɗa su da na gari ya kuma ba su haƙurin zama.

Duk kwanakin nan da Bunayd yayi a gidansa na Kano yake kwana, iyakacinsa da gidan Papi idan ya zo ɗaukan ƙannensa ko ya dawo da su, Hajiya Sa'adatu ita haka ya mata ko babu komai tunda dai ya baro su General, bata san biki ne ma ya kawo sa ba, shi kuwa idan ya zo zai gaisheta zai mata ladabin da ya kamata, kawai dai baya sakewa da ita ne, dan Bunayd na da ilimi kuma yana aiki da iliminsa, ya san ita mahaifiya ce kuma yasan haƙƙinta da ke kansa, sannan ya san hannunka ba zai ruɓe ka yankesa ka yasar ba, uwa ta wuce wasa.

Bayan Bunayd ya baro wajan su Majeeder, yana cikin driving ƙira ya shigo wayansa, ganin layin Abeed sai ya ɗauka yana murmushi ya ce, "Palace is loading, Ango mai jiran gado, Dragon za'a sha aiki" ya ƙarishe yana dariya.

A maimakon ya ji muryan Abeed sai ya ji muryan wani daban, hankali a tashe yake magana ya ce, "Bunayd an samu mastala fa."

Bunayd ya ce, "Me ya faru? Ina shi Captain Abeed É—in?"

Wanda ke maganan ya ce, "Wallahi a tarzomansu da Æ´an ta'adda shi ne aka samu akasi, duk da mun gama da su amma dai an harbesa, mummunan rauni ya samu kuma daman ya ce, duk abinda ya faru kai kaÉ—ai za'a kira kar a faÉ—awa iyayensa."

Hankali a tashe Bunayd ya ja wani wawan birki ya ce, "Yanzu kuna ina?"

"Muna babban asibitin cikin Mubi."

Bunayd bai jira ƙara jin komai ba ya kashe wayansa ya juya sai airport, hankali tashe yayi duk abinda ya kamata, jirginsu ya ɗaga sai Adamawa, jirginsu na sauƙa daman ya riga ya gama magana da sauran abokanansa da ke nan a air force base na cikin jimeta, mota aka turo mata da drivern da zai kai sa har cikin Mubi, ba ɓata lokaci suka kama hanya, suna tafiya amma Bunayd gani yake basa isa da wuri, tun da yake bai taɓa wuce cikin Adamawa ba, ba local government da ya sani, bai san nisan Mubi ya kai haka ba, ji yake kaman ya fire ya gansa a gaban abokinsa.

⭐
Yau Lahadi Banafsha ta warke daga cutan period ta yi rass abinta ta gama, wanka ta sha sharr da ita suna zaune da Mami suna hira kaman ba komai, sallama suka jiyo, wanda daga ji Banafsha ta gane muryan waye ne, zuciyanta ne ya stinke sai kuma ta saki murmushi lokaci guda, Mami dubanta tayi ta ce, "amsa sallaman mana, ki je ki duba waye ne."

Miƙewa nayi na shige ɗakina na sako hijabi sannan na fito na wuce, kaman yanda na zatan kuwa shi ne, Malam Abbo ne, murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na tare da masa sannu da zuwa, amsawa yayi, na ce masa ina zuwa, sai na koma cikin gida na faɗawa Mamina Malam Abbo ne, murmushi tayi ta girgiza kai kawai ta ce, "Sai ki ce ya shigo ko."

Komawa nayi na masa iso, muka shigo palourn lokacin Mamina ta riga da ta shige É—akinta.

Malam Abbo zama yayi ni kuma na wuce na kawo masa ruwa da abinci duka, yau ma kaman ranan murmushi yayi ya ce, "Lallai ni É—an gata ne kullum har da abinci, ki ce idan zan zo zance za daina cika cikina da tuwon Ummina."

Murmushi nayi tare da yin ƙasa da kai na ban ce komai ba.

Ƙara gaisawa muka yi bayan ya sha ruwa, sannan na ce, "Malam a yi haƙuri wannan satin ban samu zuwa ba, na faɗawa Umaima ta faɗa banji daɗi ba ne."

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "To ai ni yanzu ba abinda ya shafi makaranta bane ya kawo ni, batu ne akan rayuwata, farincikinka, cikar burina, muradina, maganar soyayyata da ƙauna ce ta kawo ni Sayyadata Roohi ta."

Wani kunya ne ya rufe Banafsha da ya sanyata kulle fiskanta da tafin hannunta, wani irin soyayyan Malam Abbo ne ya stirga mata duk wani sassa na jikinta lokaci guda ba zato ba tsammani, sai dai kaman daga sama take jin maganganun Maminta na dawo mata, sai kuma wani damuwa ya maye gurbin farincikin, wanda har Malam Abbo sai da yayi mamakin ganin yanayinta ya sauya sosai, ba tare da ya ankara ba ya kuma jin tana cewa, "Malam Abbo ka yi haƙuri, abinda na faɗa maka da farko shi ne har yanzu, ba zan iya aure da mugun tabon da ke tare da ni ba" ta na ƙarishe maganan kaman zan yi kuka, saboda ni da kai na ina jin ciwon abinda nake faɗa.

Malam Abbo murmushi yayi ya ce, "Ni ma kuma ina kan baka na, ina ƙaunarki har gobe, duk wannan amsa naki ban gamsu da su ba Roohi, amma zan yi abinda ya kamata, sai dai dan Allah ko ne na yi kada ki ga laifina soyayyanki ne ya ja."

Shiru nayi ban ce komai ba, saboda kokawa nake da zuciyata na samu da rashi da nake gani a filin Allah.

Malam Abbo ba tare da damuwan komai ba ya ce, "kwana biyu Umaima ma bata ke makarantan ba, fatan dai lafiya?"

Cikin damuwa na ɗago kai na, amma muna haɗa ido sai naji wani iri, tuni nayi ƙasa da kai na na ce, "Amma bansan me ya sameta ba, bansan ko wani abun ya faru ba, dan nima yau ne naji daɗin jikin nawa, sai dai in Allah ya yarda gobe da safe zan shiga na dubata kamun mu wuce makaranta."

Jinjina kai Malam Abbo yayi ya ce, "Hakan ma yayi Sayyadata, Allah ya yarda ya kuma nuna mana da rai da lafiya, sannan kuma Allah nuna mana bikinmu, ranar da Malama FaÉ—ima za ta zama mallakin Aliyu bawan Allah."

Shiru na yi ban kuma cewa komai ba, Malam Abbo dai sai hiransa yake mini na soyayya, duk da ina jin daɗi da kuma sanyi a rai na amma na kasa nuna hakan dan bana son na yaudari malam Abbo ko kaɗan, sai da lokaci ya ja idan yayi magana sai dai na ce Uhmn! Ko uhun!, Ganin dare na ƙoƙarin yi suka ya dube ni yana sakar mini murmushi wanda yake daga zuciyansa ya ce, "Nikam zan tafi Sayyadata sai na ƙara zuwa kuma."

Ba tare da na kallesa ba na miƙe na ce, "Bari na ƙira Mamina ko gaisawa ba ku yi ba."

Murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "Umma ta zama surkuwata kunyarta nake ji, ki bari zan zo daga baya na gaisheta daban, yanzu kunya nake ji dan yau wajanki na zo."

Abinda Malam Abbo ya faɗa dariya ya bani, dan haka murmusawa nayi, kawai muka yi sallama na rakasa har ƙofan gida, kallona yayi ya ce, "Ina matukar ƙaunarki Sayyadata."

Kallon juna muka yi na ƴan second's, inajin kaman na faɗa abinda ke rai na, amma ba dama, ganin kuka na neman zuwa mini sai na juya da sauri na kulle ƙofa na koma ciki.

Malam Abbo murmushi yayi dan shi ya riga ya sanya a ransa indai FaÉ—ima rabonsa ce to zai sameta, yasan mai zai yi, in Allah ya yarda zai mallaketa.

Ni kuma ina share hawayena na shige ciki, kusan karo muka yi da Mamina, girgiza kai tayi.

Mamina ta ce, "lafiya kuwa? Me ya faru? Me ya sameki? Yanzu nake cewa bari na bi bayanki kin zauna a waje me ya faru?"

Share hawayena nayi na seta kai na, cikin dakewa na ce, "Ba komai Mami."

Ganin dare yayi duk yin Mami, sai ta ƙyale kawai ta wuce ɗakinta na wuce nawa, ina addu'an Allah ya sa lafiya an ce Umaima ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba, da tunanin haka na kwana a rai na.

Masu Sharhi ina matuƙar Godiya 👏 Uwar batoorl taku.

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
Chapter 40 · 0% Book details