← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 58

Sashe 57

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, "Banafsha na sadaukar miki da abubuwa da dama a rayuwata, tun kina ciki har zuwan ki duniya, ban taɓa gajiya ba kuma bana fatan gajiya watarana indai zan sa ki farin ciki, kaza bata taka ɗan ta saboda bata son sa, a'a saboda tarbiyya take haka, nasani kina da tarbiyyan da na baki dai-dai gwargwado, kina jin maganata kuma kina kiyaye ɓacin rai ba, Banafsha ina da dalilin ƙin aure, amma kuma dalilin nawa bai kai naki ba na yan da kike so nayi aure, Allah ya ce ko iyayene idan suna ba dai-dai ba ka faɗa musu gaskiya, dan haka zan yi abin da kike so, nasan ke ma ba ƙin abinda nake so kike yi ba, zan yi aure da yardan Allah, zan kuma baki labarin dangina kaman yan da na faɗa, zuwa gaba kuma zan kai ki gare su, aure dai yanzu zan yi, labari kuma zan baki shi ne a matsayin kyautan bikinki, dan haka idan kin amince kin turo miji to kin shirya jin labarin Maminki."

Ajiyan zuciya na sauƙe cikin sanyin jiki na ce, "Mami Allah nima ina son ki kuma zan iya sadaukar da komai saboda ke da farincikinki, ki yi haƙuri ki yafe ni idan na ɓata miki."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Ya isa haka Banafsha, yanzu dai ke ce ƙawar Maminki, ke ce mahaifiyar Maminki, kuma mahaifin Maminki, ƙanwata, yayata, yarinyata kuma komai na, dan haka sai ki bawa Mami shawara wa ya kamata ta aura tsakanin Abbaanku da Alhaji", Mami ta ƙarishe maganan tana murmushi.

Wani farinciki ne ya lulluɓeni, tun ba'a je ko ina ba, na fara ganin sakamakon haƙuri da kuma jarrabawan rayuwa da na shiga, Mamina ke mini wannan magana, lallai uwa-uwace, bai ma kamata mutum ya haɗa soyayyan mahaifiya da na kowa ba a duniya, cikin ƙaunan Mamina na ce, "Mami tsakani da Allah da farko Abbaa nake so ki aura, amma yanzu na fi son ki aure Alhaji."

"Saboda me kika so na auri Abbaa kuma kika fasa, Sannan saboda me kika ƙi Alhaji yanzu kuma shi kike so Maminki ta aura."

Murmushi nayi na ce, "Mami da farko na ga ƙoƙarin Abbaa ne na stawon shekaru yasan irin rayuwan da kike yi amma yake dakon soyayyanki har zuwa yanzu da ya faɗa miki shiyasa na so ki aure sa dan gani ga Umaima ta, amma kuma da wannan abu faru sai hankalina bai kwanta da hakan ba, Abbaa ya saki Umma kuma saboda ke yana son aurenki, to bana son kema ya miki haka nan gaba, sannan kar Umma ta kashe mini Mamina."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Sayyada FaÉ—ima, ina jinki shi kuma Alhaji fa."

"Uhmñ! Mami haushinsa nake ji saboda yan da yake zuwa gidannan yayi kwanaki, kuma da aurensa da yaransa, yana ta ɗawainiya da mu wataƙila baya yi wa matansa da yaransa, shi ne bana so dan kada ya aureki ya miki haka, amma yanzu na fahimci ba haka bane, da gaske Alhaji yake son ki, dan Allah Mamina ki amince ki aure sa, wallahi ko ba za ki kai ni wajan dangin babana ba to na yarda ya bayar da aurena."

Mami jinjina kai ta yi ta ce, "Madalla da yarinya ta mai halin manya, tunanin nesa da kuma nazartan rayuwa, Allah miki albarka Banafsha, naji shawaranki kuma na ɗauka indai hakan zai saka ki farin ciki, amma kuma zan cigaba da neman zaɓin Allah, kema ina son ki dage da addu'a da istihara duka, tsakanin Aliyu da Danish Allah zaɓa miki mafi alkairi, idan dukan su ma ba alkairi bane, to Allah baki nagari wan da ya fi su, saboda duk halin da kuke ciki da Danish na sani, ina kallonki ne kawai da ido, to ki dena ki bari bana so, ba kyau wulaƙanta mutum dan ya ce yana son ka, aya ce guda a ƙur'ani mai girma cikin Suratul baƙara da ya ce, "ASA AN TUKRAHU SHAI'AN WA HUWA KHAIRUN LAKUM, WA ASA AN TUHIBBU SHAI'AM WA HUWA SHARRUN LAKUM" dan haka ina son ki cire stanan kowa a ranki ki yi addu'an alkairi kawai, Allah miki albarka ya tabbatar mana da alkairi."

Da, "Ameen" na amsa cikin gamsuwa da maganan Mamina.

Haka rayuwa ta din ga tafiya Umma har yanzu tana kulle kuma tukunna ba'a fara shari'anta ba, amma dai an kai Court ɗin, kuma ana ƙoƙarin farawa.

Ɓangare na kaman yanda Mami ta mini faɗa to naji, addu'a nake na neman zaɓin Allah, idan Ya Danish ya zo ba hantara ba komai zan kulasa amma dai ba dan ina jin son sa a rai na ba, Malam Abbo ma duka ina kula shi.

Ɓangaren Mamina ma ta cigaba da addu'a, kuma zuwa yanzu Alhajin ne take jin ya kwanta mata a rai, dan haka ba ɓata lokaci ta fara shiri tana gyaran jikinta, ni ma tana bani wasu abubuwan.

Bayan sati biyu komai sai hamdala, Case É—in Umma, su ya Mus'ab sun dage yanzu dai nan da sati guda za'a fara sauraran Shari'an.

Ni da Umaima kuma mun shirya staf dan washe-gari ne za mu tafi Yola ɗin, Abbaa kuma tun da ya je Mami ta basa haƙuri shikkenan ya haƙura ba dan ya so ba, sai dan ganin Mami da gaske take ba za ta auresa ba.

Washe-gari ranan tafiyanmu, a ranan matar yaya babba ta haihu, Umaima an kai ta wajan Umma, ta sha kuka ba kaɗan ba sai da Umma ta rarrasheta ta bi ta da addu'an alkairi a musabaƙan.

Mun shirya tare da sauran ɗalibai da malamai, mota ce babban ta jide mu muka nufi Yola, sai da muka kwashe awanni uku zuwa huɗu sannan muka isa cikin ikon Allah lafiya-lafiya, a wani babban makaranta aka mana masauƙi, akwai masu kula da mu da komai, ɓangaren mata daban na maza daban, haka ma na malamai, sannan har da jami'an staro akwai ana kula da shige da fice na kowa.

Satinmu guda curr a a Yola aka gama musabaƙa, muka juyo cikin farin ciki sai addu'an sauraran sakamako, daga dawowanmu kuma aka fara shirye-shiryen yaye mu, dan ba zai wuce wata biyu ba nan gaba, wan da ake saka ran kamun a yaye mu idan Allah ya sa mun yi nasara a wannan musabaƙa da muka yi, to sai mu je kuma na ƙasa da ƙasa a garin Abuja.

Mamina ta ƙira Alhaji ta sanar da shi ta amince da batun aure, Alhaji saboda farin ciki ya rasa ma me zai ce, ko me zai yi, abu na farko dai da yayi ya bata goron kyautan kujeran Makka na albishir ɗin da ta masa ta amince, sauran abubuwan kuma ya ce sai ya zo, sannan ya tura mata kuɗaɗe masu yawan gaske akan ta fara shirya masa kan ta tun yanzu, irin maganganun da Alhaji ya fara faɗawa Mami yana sakin layi tuni ta ji a karo na farko ta fara jin kunyarsa, dan kaman wan da aka ce masa an basa budurwa kyauta.

Mami shiri ta fara ba kama hannun yaro, mu kuma lokacin muka fara test a college, idan ka kalli Mamina za ka É—auka wata balarabiya ce, sosai take gyara kan ta.

⭐⭐

ACM Bunayd gidan Papi ya wuce, yana danna horn aka buɗe masa ƙofa ya shige, da sallama ɗauke a bakinsa ya shige cikin gidan, samun Hajiya Sa'adatu yayi a hakimce a kan kujera tana kallo.

Amsawa tayi tare da sakin murmushi ta ce, "Bunayd iso ka zauna."

ACM Bunayd murmushin da yake iya leɓensa yayi, a fili ya ce, "Ai gidan babana ne Mom, ba sai kin ce na zauna ba", ya faɗa tare da zama, ya gaisheta.

Hajiya Sa'adatu amsawa tayi dan abinda ya faɗa bai dameta ba, tambayansa tayi jikin abokin nasa, ya amsa mata da sauƙi a taƙaice, wayansa ya fidda yana dannawa, sai can ya ce, "Wai ina yaran nan ne na ji gidan shiru?"

Hajiya Sa'adatu hankalinta na kwana TV ta ce, "suna sama ne ina ji, kasan Majeeder ba ji take yi ba, ni duka sun fitineni ma, kai ba da haihuwa da yawa ba, kai bakinka yayi stayi, yaushe za su koma gidansu ne?"

Murmushi Bunayd yayi ya ce, "Insha Allah gobe za mu koma gidanmu Maa!"

Hajiya Sa'adatu juyowa tayi ta kallesa ta ce, "kaga wannan sunan naka na rena mutane ba son sa nake ba, ni ce maa ɗin? To ranka zai ɓaci, ai ita Huraira baka faɗa mata haka Momsee kake ce mata tun da ita ta haifeka ba ni ba, kuma kai ai nan gidanku ne ba can bane gidanku."

Bunayd shafa kiston kansa yayi ya ce, "To ai mastala da aka samu kika ki riƙe ni, ita ta riƙe ni shiyasa amma dai ki yi haƙuri Mom, da ni da su Ramla duk abu guda ne, idan can gidansu ne to nima can ne gidanmu, idan kuma nan ba gidansu bane to nima ba gidanmu bane, dan ni nafi son su a kan Majeeder ma."

Hajiya Sa'adatu ƙwafa tayi ta ce, "Zan kuwa shiga ƙafan wando guda da kai."

ÆŠan murmusawa yayi ya ce, "wannan kam sai da Papi, ni ina wando guda xa ta ishemu da ke Mom."

Hajiya Sa'adatu murmusawa tayi jin amsan da ya bata, ta ce, "Allah ya shiryaka."

"Ameen", ya faɗa tare da miƙewa ya haura sama, samun su Majeeder yayi suna ta hira suna dariyan shirme akan wai wani ya ce yana son Ramla a wajan bikin Ya Abeed, ganin Bunayd sai duk suka yi shiru, suka yi zuru-zuru da idanuwa, waje ya samu ya zauna ya ce, "Idan duniya da gaskiya ku yi hiran na ji nima na samu na yi dariya?"

Duk dariya suka kwashe da shi, sai kuma Bunayd ya gimste fiska, ganin haka duk sai suka sha jinin jikinsu, a daƙile ya ce, "maza ku tashi ku shirya na kai ku yawon da kuka ce, sannan muna dawowa ku shirya gobe za mu wuce", yana gama magana ya fice.
Chapter 57 · 0% Book details