← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 58

Sashe 46

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙiran Umma da Ummu Abbaa yayi, gyaran murya yayi ya ce, "Sai ku fara shirin da ya kamata, na tarban abokiyar zamanku, da kuma matan yaranku, zan faɗa muku ne na fita haƙƙinku ba wai dan dole ne sai na faɗa muku ba, Farooq ya samo mata a nan anguwan Kaban, sai kuma Danish a nan gida ya samu tasa matar, Faɗima yake so, kun ga abu ya zo gidan sauƙi, tuwo na mai na, ni ina son uwa, yarona kuma yana son yarinyar, dan haka ina gargaɗan ku da yin tashin hankali, Sabeera wancan karon ki daka mini yarinya akan kishinki na hauka, kina ga na zuba miki ido ban ɗau mataki ba, kin ɗauka banza kika daka ba, to zan ɗau mataki, kuma kika yi wannan karon to matakin da zan ɗauka zai baki mamakin da ba ki taɓa zato ba, aure ba gudu ba ja da baya daga ni har Danish Insha Allahu, indai Allah ya nufa to sai mun aure su."

Ummu da mamaki take kallon Abbaa, ta ce, "Danish dai ke son Banafsha? Anya ka ji da kyau?"

Abbaa jinjina kai kawai yayi bai ce uffan ba.

Umma kuwa saboda haushi ma ta kasa cewa komai, miƙewa tayi ta fice, Abbaa kuma taɓe baki yayi bai ko stayar da ita ba, dan yanzu halin Umma ya fara gimsarshi, Ummu kallon Abbaa tayi ta ce, "kana ganin hakan ya dace? Ba za'a ja wa yarinyar nan mastala sosai a rayuwanta ba, a yanzu ma kusan kullum cikin kuka take da damuwa da mahaifiyarta, idan aka mata irin wannan auren kana ga yayi? Ni bana tunanin ma daga ita har mahaifiyarta za su amince da wannan batun, duk da babu wanda yasan abinda ya faru ranan."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "ke dai ki ce Allah tabbatar da abinda ya ke alkairi."

Ajiyan zuciya Ummu ta sauƙe, ta ce, "Ameen summa Ameen."

Umma tana shiga gida ta shige ɗakinta, gabas da yamma kudu da arewa ta rasa me za ta yi ta huce, ta rasa wani mataki za ta ɗauka, wai yau Danish da ke goyon bayanta ne ya kwaye mata zani a kasuwa, ya rasa wa zai so sai fistararriyar yarinyar nan, tana fama da Umaima ta raba su, sai kuma shi ya kawo magana mai gaba-ɗaya, maganan aure, to ba zai saɓu ba, dole ta ɗau mummunan mataki, wayanta ta ɗauka ta dannawa layin Danish flashing, saboda cherge's na international call to sai dai ta yi flashing ba daman ƙira.

Ya Danish a nasa ɓangaren daman ya jima yana stumayen ƙiran Umma, dan haka yana ganin flashing nata ya biyo ƙiran, Umma na ɗauka bata saurari ko sallaman da yake yi ba ta ce, "Danish ni za ka tozarta? Ni za ka nunawa kai ɗan yau ne? To wallahi idan kaga ka auri yarinyar nan to ko bayan rai na ban amince ba, sai dai ka mutu babu aure."

Danish ajiyan zuciya ya sauƙe ya buɗe baki zai yi magana, sai Umma ta dakatar da shi ta ce, "Idan ka kuskura ka ce mini wani abu, to wa billahil Azeem ranka zai ɓaci, kai ka san halina fiye da kowa, to kada ka yarda rai na ya ɓaci..", Umma na gama masifanta ta kashe wayanta tana huci.

Haka Umma ta wuni da bala'i da masifa, abin na cin ta kwata-kwata ta kasa haƙuri ta kasa nistuwa, har yamma ta yi ta kasa haƙuri, wani abu ke ingiza ƙeyanta zuwa gidan Mami.

Yau har ƙarfe shida ta same mu a makaranta, sai da ta ɗora da mintuna sannan aka tashe mu, muka kamo hanya muka dawo gida, Umaima ta wuce nasu nima na wuce namu gidan.

Muna zaune da Mamina bayan sallahn isha'i sai kawai ganin mutum muka yi a kan mu ba ko sallama, daga ni har Mamina da mamaki muke kallon Umma Sabeera, dan nidai a iya sanina ban taɓa ganin ta shigo gidan mu ba.

Kamun Mami ta yi wani yunƙurin buɗe baki tayi magana sai gani muka yi Umma Sabeera ta fito da wuƙa, ta yi kan Mamina gadan-gadan, ihu na stala na yi kan Umma ina faɗin, "Me muka miki? Kashe mu za ki yi Umma? Dan Allah ki yi haƙuri."

Umma tureni gefe tayi tana faɗin, "Wallahi idan ke mayya ce yau sai na kashe ki kowa ya huta, idan ya so nima a kashe ni, haba dan Allah kin dameni kin addabeni kin staya mini a maƙoshi, abun ya wuce na aure mini miji da za ki yi, ya koma har yarona kuka lashewa zuciya yana son yarinyarki, to indai ina raye ko aure ɗaya ba zai ƙullu ba, wallahi ba za mu haɗa jini da karuwa kuma mayya ba."

Mami ƙoƙarin kare kanta take yi, amma Umma ta zuciya sosai, ƙoƙarin caka mata wuƙan take a ƙirji, suna kokowa har dai Allah ya bawa Umma nasaran caka wa Mami wuƙa a ciki, ihun da Mami ta yi shi ya tattaro mini sauran ƙarfin jikina, da kumburarren goshi na mike, na rarumi tire a gefe ba ƙwalawa Umma a kai, faɗuwa ta yi, ga Mami a kwance cikin jini ga kuma Umma a kwance a sume, ihu na kuma saki na fice a gidan da mugun gudu, cikin anguwa na yi ba hijabi ganin ba mutane sai na juya gidan su Umaima, a bakin ƙofa na ci karo da Abbaa da ya fito saboda ihuna da yake jiyowa.

Kasa magana nayi sai kawai nuna masa gidanmu nake ina faɗin Mamina, ina kuka, Abbaa bai tsaya tambaya na ba yayi gidanmu, muna shiga ya ga halin da Umma da Mami ke ciki, bai tsaya tambayan ba'a si ba ya fice, tare da ya Sadeeq suka shigo, Mami kawai suka saka a mota, nima Ya Sadeeq ya ja hannuna na shiga muka nufi asibiti, Abbaa ran sa a ɓace ko kallon Umma bai yi ba, General hospital Mubi muka nufa.

⭐⭐
CAS Bunayd suna tafiya yana jan staki ganin irin lokacin da suke ci, tafiya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, har sai bayan isha'i suka shigo mubi, hamdala yayi, sannan aka wuce da shi direct General hospital na mubi.

Ayi haƙuri rashin update jiya, jikinne sai a hankali kawai ku ta tayani da addu'a.

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

My ƙawas Oum inaya.
Nana ƙanwar Soja.
Aunty Salma (maman humaira da bashir)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

Noted: afuwan fan's, mastayin Bunayd na Air Force ba CAS bane, wato Chief of the air staff, mastiyinsa ACM ne, Air Chief Marshal, a yi haƙuri da mistake ɗin, shi CAS a land army ne, ACM ne Air Force, kuma Bunayd Sojan sama ne Air Force kenan, abin ne da rikitarwa sorry for the mistake.👏

🅿️ 76 _ 80

Driver na parking, Bunayd ya fito a rikice, amma idan ka kallesa ka ranste ma rigima yake ba'a cikin damuwa yake ba, amma kuma shi ya san damuwan da yake ciki na abinda ya samu Abeed, cikin hanzari suka shige ciki, sojan da ke tare da Abeed ne ya musu jagora har É—akin da Abeed ke ciki, ya so shiga amma kuma aka tsayar da shi, sakamakon taimakon gaggawa da ake kan bai wa Abeed É—in.

ACM Bunayd stayuwa yayi a bakin ƙofan ya na safa da Marwa, da ya kasa haƙuri sai ya juya kawai, dai-dai lokacin kuma ya samu kuma ana rikici tsakanin Nurses da wata kyakkyawar matashiyar budurwa, da ke rikice kaman wata mara ishashshen hankali, taɓe baki yayi zai fice sai idanuwansa suka sauƙa akan mara lafiyan da ke kwance a gadon ɗaukan marassa lafiya, ɓata rai yayi ya nufe su gadan-gadan.

Banafsha tun barowansu gida kuka take yi, Abbaa saboda ɓacin rai ko magana ya kasa yi, sai ya Sadeeq ne ke ƙoƙarin bata baki akan tayi haƙuri, amma ta ƙi shiru har suka isa General hospital ɗin.

Abbaa kuma layin babban yaya ya ƙira, yana ɗauka Abbaa bai tsaya amsa sallaman da yake masa ba ya ce, "kabeeru ka je gidan Mamin Banafsha ka ɗau uwarku, kuma kar ka kuskura ka shigar mini da ita gidana, idan ƙafanta ya taka gidana ko gawanta ne, to ban yafe maka ba, kuma kuna farfaɗo da ita ta kwana cikin shiri dan ƴan sanda suna hanya."

Babban yaya cikin tashin hankali ya miƙe, daman yana wajan aikinsa ne, gareji yake yi, cewa yayi, "Abbaa me ya faru? Me ya kai Umma gidan Mami?"

Guntun tsaki Abbaa ya ja, ya ce, "kana tambayana ne, ni na san irin haukan da ke damun uwarku, to dai ka ji abinda na ce, mu yanzu haka ma muna general hospital", Abbaa bai jira me babban yaya zai ƙara faɗa ba, kawai ya kashe wayansa yana yin ƙwafa kawai.

kusan tare motan su Abbaa suka iso da su Bunayd, Bunayd suna shigewa, su Abbaa kuma cikin gaggawa aka É—auko gadon É—aukan mara lafiya aka É—aura Mami a kai, suna shiga ciki Nurse É—in ta dube su ta ce, "kunsan ba'a attending irin waÉ—annan patient's É—in sai da police ko?"

Abbaa ya ce, "Ku yi haƙuri ku fara ceton rayuwanta baiwar Allah, police kam dama dole ne ku gan su, dole su shigo cikin lamarin nan."

Ya Sadeeq dialing layin Ya Farooq yayi amma ba ya shiga, dan ya Farooq ma a general hospital ɗin yake aiki, Banafsha cikin shessheƙa ta ce, "Dan Allah dan Annabi ku taimaka ku fara bata agajin gaggawa tukunna, ai an ce muku police ɗin za su zo."
Chapter 46 · 0% Book details