Sashe 17
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga hanya muka raba tasha ta yi gidansu, nayi namu dan kar Ya Danish ya ganta, ina isa gida na yi sallah na je kitchen na ɗauko rabona na ci, sai da muka yi isha'i, sannan muka zauna dukanmu, Alhaji yana ja mini aya ina ƙarisawa, haka muka dinga yi har dai muka yi iya dai-dai izu arba'in ɗin da za muyi musabaƙan a kai, ko ina ya canko ina idawa dai-dai, kuma yana tambaya ina basa amsa dai-dai, gyara biyu kawai ya mini, sai da muka yi sosai sannan ya kulle ƙur'anin ya sa na mayar da shi, muka zauna muna kallo, ba jimawa na musu sai da safe, sai da nayi karatu sosai na yi nafila da shafa'i da wuturi, sannan nabi lafiyan gadona na kwanta bayan nayi addu'an bacci.
Mami da Alhaji ba laifi yau ba'a yi faÉ—a ba, amma ko da suka shiga É—aki Alhaji nafilfilu kawai ya dinga yi har Mami tayi bacci, shi kuma ya tattara ya koma É—aya É—akinss ya kwanta, bayan yayi waya da matarsa Hajiya Sa'adatu.
Washe-gari haka muka je tahfiz muka dawo, nan ma dai Malam Abbo bai zo ba, ya Danish dai ya gama haɗa irin muguntan da zai mini, sai dai cikin rashin sa'a kuwa ba mu haɗu ba har ya koma da yamma, haushi kaman ya kashe sa, amma ya gama cin alwashin wata satin zai gyara mini zama, Alhaji Mukhtar kuwa sai washe-gari Monday sannan ya sallami Mamina, ni kuma ya mini faɗa sosai akan na dage, idan nayi ƙoƙari shi ma zai mini kyauta duk abinda nake so, sannan ya ƙara ƙarfafa mini guiwa sosai, sai ya kama hanyan Yola, yana isa ya wuce airport jirginsa ta ɗaga sai garin kano kanawan dabo.
Ranan Monday munje tahfiz amma boko kam mun ƙyale sa sai result ta fito kuma next semester, a ranan aka gama komai da komai a tahfiz na shirin musabaƙa saboda daga ranan Laraba za'a fara kuma har sai asabar a gama saboda makarantu da yawa ne za su yi musabaƙan, an tashe mu akan ranan talata kada muje kowa ya huta kuma yayi karatu yayi addu'a, ni da Umaima kuwa washe-gari talata maimakon karatu sai muka shirya abinmu muka tafi gidan yaya babba duk da kusa-kusa ne amma yini muka kai masa tunda ya ce bama zuwa, kuma zai yi fushi, munje gwanin daɗi-daɗi Amaryan sa mai ɗan matashin juna biyunta ta amshe mu da fara'a, amma tunda yaya babba ya dawo taga yanda muke wasa da dariya da shi, musamman ni sai ta fara haɗe fiska tana hararata, kamun ka ce me ta tsawwalawa kanta wai kishi take da ni, amma daga ni har Umaima har yaya babba babu wanda ya hararo jirginta, abinda ya dame mu muke yi.
Sai da yamma tayi liss, sannan muka ma Amarya Hindatu sallama, amma sai wani cin magani take yi, ba mu damu ba yaya babba ya sako mu gaba muna tafiya muna hira har gida, kallona yayi yana murmushi ya ce, "su sistor an kusa zama graduate, ga kuma za'a ciyo mana kyauta a musabaƙa, sannan kuma za'a amarce."
Ina dariya na ce, "wa ya faÉ—a maka haka babban yaya? Amarci kuma?"
Ya kabeer (babban yaya), yana dariya ya ce, "Faruq ne ya faɗa mini ai, wai haka kika faɗa musu, kuna zama graduate sai aure, inyee! Waye wannan mai sa'an? Ni na ɗauka ma da Danish za'a yi, irin wannan stamar tsakanin naku ai ta love ce, gaskiya koma waye a basa haƙuri muyi tuwo na mai na."
Haɗe fiska naayi, girar sama da ƙasa duk na haɗe su, na tura baki tare da bankawa Umaima harara kaman ita tayi maganan na ce, "Ni na tafi gidanmu sai gobe."
Yaya babba yana ta ƙira na amma naƙi juyowa, dan sosai ya ɓata mini rai, ni ba aure ne a gabana ba, ba zan je a dinga wulaƙantani ba, kuma ko auren zan yi har abada babu abinda zan yi da Ya Danish, ni ban taɓa jin na tsani mutum a duniya yanda na tsani ya Danish ba, a haka rai a haɗe na shige gida, Mami ta kalle ni kawai ta girgiza kai, cikin sigan rarrà shi ta ce, "Wa ya taɓa fitilar Maminta? Shalelena, Sayyada Faɗimah, autar mata, shugabar mata, gudalliyan Maminta."
Tura baki nayi, kaman zan yi kuka na ce, "Mami ba kina ganin babban yaya ba, wai ai...wai... wai ai..uhmñ!"
Mami murmushi tayi ta ce, "kina ta cewa wai wai kin kasa faÉ—an abinda ya faÉ—an, wai me?"
Langwaɓar da kai nayi na tura baki na ce, "uhmñ! Ni dai ba ruwana kada ma yan Ameen su amsa magana ya wuce."
Mami taɓe baki tayi ta ce, "Idan tayi tsami zan ji, in kuma sun riga sun amsa, shikkenan ko mutuwa za kiyi yess ne, indai alkairi ne."
Tashuwa nayi kawai na wuce ɗakina, jin Mamina za ta ƙara nata akan na babban yaya.
Babban yaya kuwa dariya ya dinga yi, Umaima tana taya shi ta ce, "yaya ka kora mini Masoyiya kuma kasan ba wannan maganan tsakaninta da ya Danish, ranan ina laɓe ina ganin su har da ranƙwashinta yayi, ranan da ka zo da yamma."
Murmushi yaya babba yayi ya ce, "Nima na gani ai, na sani Umaima, da gangan na faɗa, amma na sani Danish da Banafsha ba wannan magana, mutane kaman masu ganin hanjin junansu,ya riga ma da ya ɓata rawansa da stalle babu ta yanda za'a yi ta ƙaunace sa."
Umaima dai murmushi tayi ta shige gida yaya babba kuma ya juya ya koma gidansa, yana shigowa ya kalli matarsa ta haɗe nata giran sama da na ƙasa, fiska kaman an haɗo mummunan hadari, cikin mamaki ya dubeta ya ce, "my love me ya faru? Ko baby ne ya naushe ki? Ya faɗa yana murmushi tare da zama a gefenta.
Stam! Hindatu ta miƙe ta koma gefe ta zauna, tare da juyar da kai, yaya babba bai kawo komai a ransa ba akan su Banafsha, kawai ya ɗau abun akan ko fushin masu ciki ne, haka ya dinga lallaɓata, da ƙyar ta haƙura sannan ta ce ya shiga tsakanin Banafsha da zuwa gidanta bata so, babban yaya kam mamaki ne ya kashe sa a zaune, wato daman abinda ya sanya ta sauya fiska tun ɗaxu kenan, girgiza kai kawai yayi ya lallaɓata komai ya wuce.
Banafsha duk da tasan gobe ba lallai a fara da su ba, amma ta dage da karatu da addu'a, duk da gefe guda na zuciyarta tunanin rashin zuwan Malam Abbo kwana biyu ne cike fam a ciki, haka kawai take kewansa sam bata jin daÉ—in rashin ganinsa.
Æangaren Umaima ma karatun da addu'an tayi sosai, Nana ce ta shigo ta ce, "yaya Umaima wai inji Umma ki zo."
Miƙewa tayi ta fice, ɗakin Umma ta shiga da sallama, bayan ta zauna a gefe ta ce, "Umma gani nan."
Rai a ɓace Umma ta dubi Umaima ta ce, "Umaima! Umaima! Umaima! Sau nawa na ƙira sunanki?"
Umaima ta ce, "sau uku Umma."
"Umaima kinsan dai ni ce uwarki ko? Ni na stugunna na haifeki ba wata banza ba ce ta haifa mini ke, kibar ganin ansaka miki sunanta tana nuna tana sonki, to duk soyayyan munafurci ce ba ta gaskiya ba, Umaima ki nistu ki shiga hankalinki da ni, kada ki bari rai na ya ɓaci kiga fushina, ko kuwa na miki baki akan wasu mutane daban, Umaima uban wa ya ce kije gidan kabeeru da wancan fitsaratun yarinyar?"
Umaima tura baki tayi ta ce, "Umma kiyi haƙuri, wallahi ni ba ruwana babban yaya ne ya ce muje da ita."
Umma hararan Umaima tayi ta ce, "Dan ubanki rufe mini baki, munafuka kawai, ƙarya za ki mini? Bansan halinki ba ne ko me? Sau nawa ina faɗin ki fita harkan yarinyar nan bana so, bana so amma kin mini kunnen uwar shegu kinƙi ji, to kada ki bari rai na ya ɓaci."
Tura baki Umaima tayi ta ce, "ki yi haƙuri Umma."
"Tashi ki bani waje kamun na karya ki yanzun nan, mara zuciya kawai wacce bata gaji uwatta ba." FaÉ—in Umma kaman za ta kifawa yarinyar tata mari.
A É—ari Umaima ta tashi ta fice, ta koma É—akinsu tana faÉ—in, "Allah huci zuciyanki Umma, Allah shirya mana ku iyayenmu."
Washegari Umaima da Banafsha suka shirya staff suka tafi tahfiz, Banafsha da Malam Abbo ta fara yin tozali, farinciki kaman ya kasheta, har Malam Abbo sai da ya kusa fahimtan hakan saboda ya ga wani irin murmushi da take sakar masa, abubuwan da ya kamata suka yi sannan aka ɗauki ɗalibai aka tafi wajan gabatar da musabaƙa, makarantu ne kusan nawa, haka aka fara gabatar da musabaƙa, ɗalibai kowa na iya ƙoƙarinsa, amma har aka tashi na yau ba'a taɓo ɗaliban makarantan su Banafsha ba, sai da suka dawo sannan Banafsha ta sa Malam Abbo a gaba da shwagaɓa wai me ya sa kwana biyu bai zo ba, Malam Abbo murmushi kawai ya mata ya ce su tafi gida ta ci-gaba da dagewa da karatu.
washe-gari ma haka aka yi musabaƙa lafiya-lafiya kuma dai ba'a iso su Banafsha ba, Laraba, Alhamis, juma'a duka ba'a iso su Banafsha ba, kuma abu na ta kan tafiya, ɗalibai masu ƙoƙari suna yi, wasu kuwa ana musu gyara, wasu kam ma dismiss nasu ake yi saboda they're not fit and compited, ɗalibai da dama wasu akwai ilimin, akwai kuma ƙoƙarin, amma ba su da confidence na tsayuwa a gaban dubban jama'a su gabatar da abu, wanda kuma wannan confidence ɗin shi ake buƙata a wajan ɗalibi, wani sa'in ma shi aka fi buƙata fiye da ƙoƙarinsa ko iliminsa, so dan haka yaranmu students ku dage, ku sa a ranku kuna da ƙwarin guiwan stayuwa a gaban duniya kuyi magana, just feel you can stand and talk for whole world, wannan courage shi ake buƙata, Allah ya taimaka wa yaranmu masu karatu da mu kanmu, Allah buɗa basira ya dafa mana a ko wanni hali da juyin rayuwa.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# ð˜¾ð™¤ð™¢ð™¢ð™šð™£ð™©
# ð™‡ð™žð™ 𙚠&
# ð™¨ð™ð™–ð™§ð™š
👄'YAR KARUWA👄💅
Officially
ð˜½ð™®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)