← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 58

Sashe 22

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umaima da ke yashe a gefe can ta buge hannunta a jikin kujera har hannunta ya É—an kumbura, kuka ta sanya kawai, cikin gaggawa yaya babba yayi wajanta yana duba hannun nata, tausayinta ne ya rufesa ganin har taji ciwo, dan sosai suke son Umaima yayyun nata.

Ni kuwa rai na a ɓace na fito bana ko kallon hanya haka nake tafiya kaman zan tashi sama, ba zato ba tsammani naji anyi sama da ni, saboda ɓacin rai da nake ciki ko ƙoƙarin buɗe baki banyi ba balle ihu, sai dai zillewa da nake ƙoƙarin yi dan bansan wa ya ɗaga ni ba, ganin da nayi an shiga sashin mazan da ni, nan na tabbatar da mai wannan aikin, muna shiga ciki aka dire ni a ƙasa har sai da na ƙafata ta lanƙwashe ta mini zafi.

Miƙawa nayi naja staki kawai na nufi ƙofan fita, dan ba sai na kalli waye bane, saboda nasan wa zai iya mini wannan aikin marassa hankalin, hijabina ya rike tare da jawo ni baya ya hankaɗa ni kan kujeran zaman mutun uku da ke cikin palourn, faɗawa nayi kai na buge bayana kuma, runste ido nayi tare da sakin ɗan marayan ƙara, sai lokacin na ɗago idanuwana na sauƙe su a kan sa, wani malalacin ɗan iskan kallo na aika masa da shi sannan na ce, "Wallahi ka fita a harkata idan ba haka ba zan iya kashe ka Danish, na tsaneka kaman yanda ka tsaneni, banason kallonka, ka dena taɓa ni idan ba haka ba zan iya illataka."

Danish murmushin mugunta ya saki ya ce, "bayan kisa kiyi abinda za ki iya yi, ba dai ni kike faɗa wa maganan banza ba, to zan gwada miki iskanci irin nawa ganin idonki dan ki sani, ko a cikin kwartayenki babu sa'a na balle ke ƙaramar karuwa, har ni za ki cewa ba'a ɗan iska ɗaya sai biyu, to kuwa yau zan nuna miki irin nawa iskancin, gobe ko da kuɗi ba za ki yiwa wani ba balle ni Danish."

Miƙewa nayi tare da sakin murmushi mai nuni da bai san abinda yake faɗa ba, kallonsa nayi sama da ƙasa duk da belt na wandonsa da yake ƙoƙarin cirewa amma hakan bai dame ni ba, sai ma dogon stakin da naja na ce, "Na faɗa, na kuma faɗa, kuma zan ƙara faɗa, jikin Banafsha ya fi ƙarfinka Danish, na wuce sa'ar yinka, kai mata-maza nake maka kallo, ka je a kuma maka kaciya sannan ka tunkare ni, " ina gama magana na yi hanyan fita.

Wannan karon cikin zafin rai ya jawo ni ya haɗa ni da bango har sai da na buge kai na, a cikin mugun ɓacin rai ya ce, "Zan kuma gwada miki cewan nafi ƙarfinki yanzu, sai na miki kaca-kaca, sai na illataki, sai na miki abinda babu wanda ya taɓa miki irinsa duk yawon iskancinki, za ki ga mata-maza ganin idonki yau" yana gama magana cikin zafi ya ja hijabin jikina ya yage sa, saboda kada nayi ihu ya haɗe bakinmu waje guda sannan ya fara kiciniyar cire mini kayan makarantan da ke jikina, ni kuwa tunda ya haɗe bakinmu waje guda tuni wani irin storo ya ziyarce ni, banason zina, na tsani zina, bana son mai aikatasa, ko mahaifiyata babu yanda na iya da ita ne shiyasa, ita ɗin ƙaddarata ce.

Abbaa da Ummu dawowansu kenan daga asibitin da suka je, da yake a waje Abbaa ya bar mota, to tun shigowansu suke jin kaman ana kokuwa a sashin su Sadeeq, har za su wuce sai Ummu ta ce su duba dai su gani ko lafiya, Abbaa ba musu suka juya suka nufi ƙofan palourn samarin, suna isa kuwa suka jiyo kaman shessheƙan kukan mace, da sauri Abbaa ya tura ƙofan.

Kiciniyar ƙwacewa na fara yi, ina son nayi ihun naiman taimako ganin ya Danish da gaske yake, amma yaƙi bani daman hakan, ba shan bakina yake ba amma ya rufe mini baki da nasa, nan muka fara kokawa da Ya Danish, da yake ya fi ƙarfina sai samun galaba yake a kai na, har ya kai ni ƙasa ya danneni, kaman yanda zuciyana ke buganawa nakan iya jiyo nasa sautin bugun zuciyan tunda ƙirjinmu ya haɗe waje guda, yana ƙoƙarin zare wandon jikina kawai aka banko ƙofa aka shigo, waye za mu gani? Abbaa ne da Ummu, cikin hanzari Abbaa ya zo ya janye ya Danish tare da kwashe shi da maruka, Ummu kuma ta ɗaga ni tana kuka ta ja hannuna, bata koma cikin gidan da ni ba ta yafa mini ɗankwalinta hannunta cikin hannuna tayi gidanmu da ni, nima a nawa ɓangaren hawaye kawai nake yi dan nayi mugun storata, stanar Ya Danish ya ƙara rufe ni, nayi nadaman sanin wannan gidan nasu a rayuwata, tuna har ya haɗa bakinsa da nawa sai kawai na fashe da kuka na faɗa jikin Ummu dai-dai mun shiga haraban gidanmu.

Abbaa kuwa ba abinda yake yi sai aikin marin ya Danish yana faɗin, "Ni za ka tozarta Danish? Ni za ka wulaƙanta a garinnan? Yarinyar mutane za ka yiwa fyaɗe dan baka da kirki? To wallahi gwanda na kashe ka na huta da ina gani na bari ka ƙetawa yarinyar mutane mutunci, abun kunya za ka jawo mini ina zaune lafiya."

Ya Danish ko ajikinsa maganan Abbaa bai damesa ba, shi haushi ɗaya yake ciki kawai da bai koyawa Banafsha hankali ba, ƙwace kansa yayi ya fice tare da barin gidan gaba-ɗaya, a lokacin ya shige motansa yabar mubi ya nufi Camaroon tun weekend ɗin bata ƙare ba.

Abbaa cikin haushi yayi cikin gidan, nan kuma ya tarar da Umaima na aikin kuka, kallonta yayi har yanzu ransa a ɓace ya ce, "Me ya same ki?"

Umaima cikin kuka ta nunawa Abbaa hannunta, ta kuma faɗa masa duk abinda ya faru, ƙara tunzura Abbaa yayi, ransa ya kuma ɓaci, lallaɓa Umaima yayi ya shige ɗakin Ummu dan idan yaje wajan Umma yanzu ya tabbata zai yi abinda ba zai yi kyawun gani ko ji ba, amma dai dole ya ɗau mummunan mataki akan Umma da Danish, dole ya take musu birki zuwa yanzu, abu shekaru da shekaru amma kullum cikin stanan yarinya da tsangwamarta, to zai nuna musu iyakar su, yasan abinda zai yi.

Ummu stayar da nata hawayen tayi ta ce, "kiyi haƙuri Umaima, in Allah ya yarda haka ba zai ƙara faruwa ba, Abbaanku zai ɗau mataki kin ji?"

Ɗagawa Ummu kai kawai nayi ina stagaita kukana, sai da Ummu ta rarrasheni sosai sannan ta ce, "Da banso ɓoye lwa Maminki wannan abinda ya faru ba, amma kiyi haƙuri kada ki faɗa mata kinji, ki bari muji daga bakin Abbaanku, amma dai ba wai ina nufin hanaki zuwa wajan ƙawarki ba kinji, kiyi haƙuri ki rage shiga gidan can, in Allah ya yarda komai zai dai-daita, kada ki faɗawa Maminki dan hankalinta zai tashi sosai, kuma ba za taji daɗi ba, kede ki kiyaye, kada ki ƙara ko haɗa hanya ne da shi."

Jinjina kai kawai nayi, tare da share hawayena, Ummu ta fice ta koma gida ni kuma na shige cikin palournmu, cikin rashin sa'a na samu Mamina zaune a palour, kai na a ƙasa na seta muryana na ce, "Sannu da gida Mami" ina gama faɗa nayi ɗakina da sauri.

Mami da kallo ta bini, ganin ina ɗingisa ƙafana, ga shi kuma wani ɗankwali na rufe kai na da shi a maimakon taga hijabin makaranta, tun ɗaxu tasan muke dawowa amma taganni shiru, sai abin ya dame ta, tashuwa tayi tabi bayana, amma tana shiga ta samu har na shige banɗaki, daga waje ta ce, "lafiyanki kuwa Banafsha?"

Daga cikin banÉ—akin na ce, "Lafiya lau Mami, wanka nake yi."

Mamina ba dan ta yarda ba ta fice kawai, ni kuwa a banɗaki sai da na gama shan kukana, sannan na dirje jikina kaman ba gobe, sai da jikina ya fara zafi sannan na fito, da haushin Ya Danish ya haɗa jikinsa da nawa, sallah nayi na miƙa kukana wajan Allah sannan na yi addu'an musabaƙan gobe Allah bamu sa'a, sai da nayi isha'i sannan na fita, abincin dare na ɗiba na ci ɗan dai-dai, Mami ta sani gaba da tambayan me ya hanani dawowa da wuri? Me ya samu hijabin makarantana? Duk tambayoyin Mamina amsa guda take samu, ba komai ba kuma abinda ya faru, da ta gaji sai ta ƙyale ni ta tambayi batun musabaƙa nan ma na faɗa mata sai gobe za muyi namu in Allah ya yarda, addu'an sa'a ta mini, can ba jimawa na mata sai da safe na shige ɗakina, yau gaba-ɗaya na kasa karatu saboda taƙaici, karshe kawai kwanciya nayi dan nayi bacci ko zan samu nustuwa.

Ummu haka ta koma gida ta rarrashi Abbaa da ya bari ya bi abun a sannu, dan Abbaa ya faÉ—a mata duk abinda Umaima ta faÉ—a masa, kuma Ummu bata yi musu ba dan tasan staff Umma Sabeera za ta aikata abinda ya fi haka ma, saboda irin stanar da ta yiwa Banafsha mara dalili, Ummu dai wani abu take tunani a ranta amma ta bari ba yanzu za ta bawa Abbaa shawaran ba, yanzu dai ya kwantar da hankalinsa tukunna, sai da ta samarwa mijinta nustuwa, sannan taje wajan Umaima ta rarrasheta ta bata abinci a baki ta bata magani ta shafa mata na shafawa, dan babban yaya sai da ya kai ta chemist kamun ya tafi, ita ma Umaima bata iya karatu cikin wannan daren ba, kwanciya kawai tayi baccin wahala yayi gaba da ita.

Yaya babba kuwa ransa yanda yayi mugun ɓaci, ko takan matarsa Hindatu bai bi ba, haka zalika wai ita ma fushi take da shi, an mareta bai yi komai ba sai ma haƙurin da ya bawa Banafsha, ga shi kuma a gabanta ya riƙo hannun Banafsha, kuma ita ko sannu bai ce mata ba, sai ta hau dokin zuciya.

Washe-gari Lahadi da wuri su Banafsha suka tafi makaranta, daganan aka wuce wajan musabaƙa, yau da makarantan su Banafsha aka fara, cikin ikon Allah suka yi lafiya suka gama, aka cigaba da sauran makarantun da suka rage, har sai yamma yau ma aka tashi, amma yau kam an kammala sai jiran sakamako.
Chapter 22 · 0% Book details