← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 58

Sashe 37

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wasu shekaru biyar Hauwa'u ta kuma haifan yaranta ƴan biyu mata, aka sakawa ɗaya sunan kakansu da ta rasu, Salma ɗayan kuma Salima, bayan haihuwansu ba jimawa Rahama ta samu mijinta dan ita kam auren ya ɗan mata jinkiri ma, shekaranta biyu da aure ta haihu ƴar ta mace ranan suna ta ci sunanta Huraira, kuma a lokacin Hauwa'u ta ƙara haihuwan ɗa namiji mai suna muhammad, amma ita rahama tun da ta haihu ciwon ciki ke damunta, a ranan da suka yi kwana ishirin da haihuwa a ranan ta cika.

Rasuwan Rahama sosai ya taɓa ahalinta, musamman da ta bar jaririyan da ko wata bata yi ba a duniya, mijin Rahama ya bar Huraira a hannun kawunta Sule saboda kara, Hauwa'u ta nemi ta haɗa su ta shayar tare da muhammad amma Ilyasu ya hana, dan haka madara ake bata, tun su Huraira ba su shekara ba muhammad yaron Hauwa'u ya koma, a wannan lokaci kuwa Mukhtar da ƙaninsa Sufyan sun zama Samari dan Mukhtar yana da shekaru kusan goma sha bakwai, shi kuma Sufyan shekaru sha biyu garesa, twin's kuma shekarunsu bakwai kuma duk suna nan lafiya-lafiya, Mukhtar ma yana karatu kuma yana kula da harkoki irin na mahaifinsa Sule kwalli, yayinda Sufyan ya dage shi Soja zai yi, kuma da yake ba rayuwan yau ba ne sai ya samu cikin ikon Allah.

Lokacin da Huraira ta yi shekaru biyar a duniya, lokacin Ilyasu ya buƙaci da su kai ziyara a Binji wa sauran ƴan uwa, Mukhtar da Sufyan duk suna makaranta ba sa gida, dan haka sai duk suka shirya da Sule da matarsa Hauwa'u da Ilyasu babansa da yaransa ƴan biyu, Salma da Salima da kuma Huraira, sun shirya sun kama hanya, lafiya-lafiya haka suka isa, suka zaga dangi suka musu alheri, kwanansu biyu suka tattaro dan su dawo gida, a hanya kuma suka haɗu da ƴan fashi, duk da sun samu abinda suke nema amma ba su bar kowa da rai ba haka suka kashe su suka yi gaba, labari na iske Mukhtar da Sufyan kaman za su yi hauka haka suka zo, sai dai wajan yi wa gawa sutura aka samu Huraira da ranta, storita da lamarin da ya faru ne ta yi dogon suma ba wai kasheta aka yi ba ita.

Wannan rashi kaman zai haukata Mukhtar da Sufyan, sannan Sufyan ya ɗau alwashin kama masu laifin sai ya ɗau fansan iyayensa da ƙannensa, Mukhtar kuwa sai dai ido kawai, Huraira haka ta zama shiru-shiru ita ma kaman mara ishashshen lafiyan ƙwaƙwalwa.

Malam Zahraddin mahaifin Huraira shi ya riƙe su Mukhtar tunda da girmansu ba buƙatan sai ya riƙe musu dukiya, kawai ya riƙe su ya zama kaman mahaifinsu ne dan saka halaccin iyayensu a garesa na riƙe masa ta shi yarinyar da kuma basa mata.

Shekaru sun ja, Mukhtar ya zama Alhaji kuma cikin ikon Allah tunda al'amuransa suka yawaita a Kano sai ya tattara su suka koma can, a Kano kuma ya samu matan aure Sa'adatu ƴar gidan wani kansila, tun da Alhaji Mukhtar yayi aure aka tura Sufyan aiki a Abuja, ita kuwa Sa'adatu wulaƙanci ne da ita ba kaɗan ba, haka ta ke yi wa Huraira da mahaifinta, Alhaji ya stawatar sosai, amma sai mahaifin Huraira ya ce za su je Sokoto ganin gida, duk saboda kada yana babba ya haddasa rashin zaman lafiya stakaninsa yaransa, haka ya tattara Huraira suka koma Sokoto a can kuma ta cigaba da karatu cikin kewan yayunta dan sosai Huraira ta saba da su Mukhtar.

Sufyan daga Abuja aka kuma shillasa Lagos, kuma tunda ya je Lagos ta masa daɗi ya zauna daram abinsa, ba batun aure a lissafinsa, sai dai ya kawo wa yayansa ziyara kwana ɗaya biyu ya koma, ya je Sokoto shi ma kwana ɗaya biyu ya koma Lagos, yana aikin Soja kuma yana da business wanda ya ɗaura masu kula masa da business ɗin, kuma a ɓangaren aikinsa ko da yaushe cikin ƙarin girma yake, inda yanzu yake mastayin General, kuma cikin ikon Allah da taimakon bincike, ya samu ya kama waɗanda suka kashe masa iyaye, hukuma ta yanke musu hukunci, saboda sun ishi al'umma daman.

Hajiya Sa'adatu ta haihu ɗan ta namiji mai shegen kyau mai kama da Sufyan kaman shi yayi kakinsa, idan ka ga yaron za ka ɗauka ɗan larabawa ne, yaro ya ci sunansa muhammad Bunayd, Sa'adatu ta ce ta daina haihuwa ita ba za ta iya ba ta stofe da wuri, ita ba son haihuwa take ba, kuma ko shayar da Bunayd bata yi sai Alhaji ya stawatar mata, amma duk da haka sam-sam Alhaji bai rageta da komai ba, domin da mahaifinta ya rasu aka raba gado aka bata nata, sai ya ƙara mata jari a kai ta fara business, wanda cikin ƙankanin lokaci kasuwancinta ya bunƙasa ta zama Hajiya ita ma, sai dai wulaƙanci ya ƙaru, kwata-kwata Hajiya Sa'adatu bata son kowa ya raɓe ta ko mijinta, hatta Sufyan da yake ƙanin Alhaji Mukhtar to ba ta ƙaunarsa, komai ita ɗaya haka take so, ko Alhaji zai yi yaya da ita yanzu bata yarda ta je Sokoto, sai dai ta kawo masa uzurin ƙarya.

Sufyan ya fi Alhaji Mukhtar ziyara sosai ba kaɗan ba, dan sai Sufyan ya je Sokoto sau biyar Alhaji Mukhtar bai wuce ya je sau biyu ko ɗaya ba, tunda Hajiya Sa'adatu ta haihu shikkenan kuma sintiri ya samu Sufyan Kano to Lagos, Allah ya ɗaurawa Sufyan stanstar ƙaunar Bunayd, dan ko da Bunayd yayi shekara biyu sai Sufyan ya ɗauke sa suka tafi Lagos, duk da ba shi da aure amma ya samu wata musulmar Yoruba tana kula masa da shi, kuma shi ma da kansa yana kula da Bunayd kaman shi ne mahaifiyarsa, kashinsa fistarinsa komai akan Bunayd ba abinda General Sufyan bai iya ba, kuma karatunsa Arabic da boko yana kula da shi, musamman abinda ya shafi Addini da kansa yake zama ya koya masa, baya taɓa yarda aiki ya sha kansa bai duba karatun Bunayd ba, gata kam iya gata Bunayd na samu a wajan General Sufyan, gatan da ko ɗan cikinsa ba lallai ya samu ba.

Alhaji Mukhtar kuwa ba abinda ya ce dan General Sufyan ya É—au Bunayd, saboda shi hakan ma hankalinsa ya fi kwanciya, akan hali irin na matarsa, ita Hajiya Sa'adatu kuwa gaba-É—aya hankalinta na kan business nata ko a jikinta, sai hamdala ma da tayi an rage mata aiki, dan ita ko haihuwan bata so ba balle yaro ya takura mata, kwata-kwata Bunayd bai san wani daÉ—in mahaifiyarsa ba, shiyasa shi ma a duniyansa komai nasa General ne, dan da shi yayi mugun sabo.

General Sufyan ko ina zai je ƙafansa ƙafan yaronsa Bunayd da ya zama kamar abokinsa, har Sokoto suke zuwa tare har wajan wani abokinsa Soja ɗan gidan wazirin Sarkin Sokoto, kuma Bunayd ya shaƙu da Huraira sosai, haka mahaifin Huraira ma sosai yake ƙaunar Bunayd, dan Bunayd yaro ne da duk wanda ya kallesa to sai ya shiga ransa, ba shi da ƙiriniya irin na sauran yara, kana ganinsa kaga zubin sadauki, yana da raha idan yayi niya musamman idan yana tare da General Sufyan ko Alhaji Mukhtar.

Bunayd na da shekaru sha uku mugun soyayya ya ƙullu stakanin General Sufyan da yarinyar Sultan na Sokoto, ta sanadin abokin General Sufyan, Major Ahmad wanda yake yaro a wajan wazirin Sarkin Sokoto, soyayyan General Sufyan sosai yayi nisa shi da Gimbiya Ramlat, ta san yana da yaya kuma tasan yana da yaro, wani stautsayi ne ya faru stakaninsu wanda yayi sanadin raba soyayyansu, damuwan da General Sufyan ya shiga shi ya sanya mahaifin Huraira ya basa auren Huraira tunda ba ta haramta a gare sa ba، duk kuma abinda ke faruwa Alhaji Mukhtar bai da labari dan yayi tafiya ƙasar waje.

Ba jimawa aka yi auren Huraira da General Sufyan, Bunayd sosai ya ji daɗin da Huraira ta dawo gidansu, kuma Huraira stakani da Allah take riƙe Bunayd da soyayya kaman ɗan cikinta, duk da ba wai ya cika zama bane, sakamakon makarantan sojojin sama da General ya saka shi, da farko Sojan ƙasa yayi niyan turasa amma sai Bunayd ya ce Air Force yake so, shi jirgi yake so.

Alhaji Mukhtar ya dawo ya samu labarin abinda ya faru nan ya bi su da addu'an Allah ya kyauta, a wannan lokacin ne kuma ciki ya bayyana jikin Hajiya Sa'adatu ba shiri ba sanarwa, duk ta gama sakankancewa ta daina haihuwa tunda ta yi planning, amma ikon Allah sai ga ciki, baƙin ciki kaman ta yi yaya, ta yi iya yinta amma ta kasa ɓarar da cikin, haka ta haƙura ba dan ta so ba sai dan ba yanda ta iya da nufin Allah, ciki na kai wata tara ta haifa yarinyarta santaleliya kyakkyawa mai sunan mahaifiyar su Alhaji Mukhtar, Hauwa'u amma suna ƙiranta Majeeder.

Huraira na cika shekara a gidan General Sufyan ta haifo yarinyarta mace kyakkyawa mai kama da Alhaji Mukhtar, yarinya ta ci suna Ramla, bayan shekara biyu ta kuma haihuwan ƴan biyu mace da namiji, Suhail da Suhaila, bayan wasu shekaru biyun ta kuma haihuwan ƴan biyu, Nabeel da Nabeela, bayan shekaru biyu ta haifi yaronta namiji amma ya koma, saboda wahalan da ta sha da cikin yaron sai General ya buƙaci da a stayar da haihuwan, Allah ya yiwa waɗanda suka haifa albarka.

Hajiya Sa'adatu tun da ta haifi Majeeder sai ta je asibiti a ɓoye aka cire mata mahaifa ba tare da sanin Alhaji Mukhtar ba, kuma har yau bai sani ba.

Yaran gidan General Sufyan sun taso cikin gata da soyayya na iyaye da kuma yayansu Bunayd, kaman yanda General ya kula da karatun Bunayd, haka shi ma yake kula da karatun ƙannensa, sosai yake ƙaunar ƙannensa, amma sam-sam ba ya shiri da Mom tasu Hajiya Sa'adatu.

Bunayd ya fara abota da Abeed ne tun san da ya shiga makarantar sojojin ƙasa da farko, sai ya zamana duk da ya koma air force school to ba su bar abota ba, shi ma Abeed ɗan Kano ne, mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, haka mahaifiyarsa ma tana nata business ɗin.

Malam Zahraddin mahaifin Huraira bai jima da rasuwa ba, sai bayan rasuwansa sannan suka ɗaga ƙafa da zuwa Sokoto.
Chapter 37 · 0% Book details