Sashe 38
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Mukhtar business yake sosai, kuma ya mallaki companies da dama, a Nigeria da ma ƙetaren Nigeria, shi ma General yana da nasa business ɗin kuma shi babba ne a sojoji.
Bunayd ma ba iya aikin Soja yake yi ba, domin daga General har Alhaji Mukhtar ba wanda bai ba sa jari ba, sannu a hankali ya fara business da kuɗaɗen, kuma shi da kansa yake kula da harkokinsa, sai dai kawai wakilai da yake da su, ya na da gidaje uku a cikin Lagos, sannan yana da gida a Kano, sai kuma ƙasashen waje da ya yawaita zuwa, duk inda business nasa ya yawaita a can yana da gida, ƙasashe shida duk ba inda bai da haɗaɗɗen gida a can, kuɗi CAS Bunayd yake da shi na fitan hankali wanda har ya ƙere iyayensa da suka basa jari, kuma shi ma duk ƙannensa maza ya basu jari duk da ƙananun shekarunsu, dan Suhaila shekarunsa 17 ne, amma shi ma yana da nasa Companyn a Turkish inda yake karatu, sannan yana zama a gidan Bunayd da ke can.
Nabeel mai shekaru 14 yana cikin na 15, shi ma Bunayd ya mallaka masa nasa rabon, yanzu haka dai rikice yake da General, shi Nabeel ya ce baya son aikin Soja, General kuma ya ce sai yayi.
Majeeder ta taso sai a hankali, amma da yake ita mace ce da sauƙi, Hajiya Sa'adatu na kula da ita ba kaman lokacin da ta haifi Bunayd ba, Alhaji ganin irin halin Hajiya sai shi da kansa ya ke duba duk abinda ya shafi Majeeder, tarbiyanta da komai nata, bai bari rashin kulawan mahaifiya ya sa yarinyarsa ta lalace ba, tana karatu boko da Arabic, bai jima ba da suka yi musabaƙa a cikin Kano kuma ta zo ta ɗaya, a boko kuwa tana matakin degree tana shekaranta na kusa da final year, inda take karantar Agriculture, a University na Kano.
Ramla tana karatu a babban Private University na Lagos, Anchor university, inda take karantar Education and computer science, sai kuma Suhaila da take nursing school a Lagos ɗin tana karantar midwifery, ita Nabeela kuma yanzu ne za ta tafi matakin gaba da secondary, ta dage University na Abuja za ta je, Bunayd kuma ya ce ba za ta yi zaman hostel ba, dole ita ma a Anchor university za'a nema mata admission ta karanci accounting, Suhail dai yana Turkish yana karantan abinda ya shafi business, shi ka Nabeel ya ce business administration zai karanta ko a Lagos ko kuma wata ƙasan, amma sam General ya ƙi.
Bunayd na da tarbiya dai-dai gwargwado dan sosai yake kula da abinda ya shafi addininsa, kuma yana da girmama manya, sai dai yana da abin dariya wani lokacin, kuma idan hali ya mosta to yana da miskilanci, bayan Abeed yana da wasu abokanan amma a wajan aiki, kawai ba wai ana together irin sosai ɗin nan ba ne kaman yanda yake da Abeed, kuma a wajan abokanansa ya koyi zuwa su club da sauransu, ba inda za'a je bai je ba amma kuma tunda ya ke bai taɓa kai abinda ya shafi giya ko kusa da bakinsa ba, kuma duk iya yanda sojoji ke harka da mata to shi babu shi a ciki, domin shi gani yake ko ashawo ba su gana waye wa ba, shi ya fi son ya samu wayayyiyar mace wacce bata da kunya ya aura, sam-sam baya son Ustaziyan mace, dan gani yake duk ustazan matan nan ba abinda suka sani sai ƙauyanci da kunya ba su iya soyayya ba, kwata-kwata bai taɓa yin ko budurwa ba a rayuwansa, duk da kuwa harin da mata ke kawo masa ta ko ina, ba ya wulaƙanta mace amma kuma yana koya mata tarbiya, dan idan mace ta dame sa da maganan banza sai ya koya mata hankali wai a kan me za ta taɓa sa bata biya sadaki ba, maganan iyayi kuwa akwai a bakin Bunayd sinƙi-sinƙi.
Bunayd ɗan shashu ne sosai, indai zai je club to ko mazari ne a wajan ba zai kai sa rawa ba, kuma tun tashuwansa ya ke ƙiran General Sufyan da General, Alhaji Mukhtar kuma ya ce masa Sir, har sai da aka haifi ƙannensa suka fara ƙiran Alhaji da Papi sannan wani lokacin yakan ce wa Alhaji Papi, General kam duk da ana ce masa Affa, to sai ranan da ya ga dama zai faɗi hakan.
Wannan shi ne asalin wannan tarihin wannan ahali a taƙaice, kowa kun ji halinsa saura kun ji a baya, sauran kuma za ku ji a gaba.
CI-GABA LABARI
Upstairs na farko a gidan Papi shi ne sashinsa da matarsa Mom Hajiya Sa'adatu, É—aya upstairs É—in kuma shi ne na Affa General da Momsee Hajiya Huraira, sai haÉ—aÉ—dun flat É—in kuma É—aya na CAS Bunayd, É—aya na Suhail da Nabeel.
Duk da Bunayd yana da part nasa a gidan, amma sai bai ko je ba ya tsaya a sashin Affa General, anan da masu aiki suka kawo abinci, Momsee ta saka su Ramla suka yi saving nasu, cikin nistuwa suka ci, sannan kowa ya shige ciki dan ya wasta ruwa, Bunayd na miƙewa Majeeder ta miƙe ta rufa masa baya, juyowa yayi ya kalleta ya ɗaga mata gira ɗaya ya ce, "Autan dole ya aka yi?"
Tura baki Majeeder tayi ta ce, "Ni dai ƙafanka ƙafa na, sai ka ƙara guduwa irin na lokacin kuma ka jima ba ka zo ba."
Murmushi Bunayd yayi dan ya tuna wayon da ya yiwa Majeeder ya samu ya koma Lagos, last time da ya zo, bai ce komai ba ya riƙo hannunta ya ce, "To Autan dole muje sai ki bani labari ma, amma dai wanka zan yi, kuma nan gaba matata ta ga kina maƙale mini haka haushinki za ta dinga ji, ba ruwanta da ke ƙanwata ce."
Majeeder maimakon ta ɓata rai sai ta yi dariya ta ce, "Yauwá sweet bro yaushe za ka yi aure? Ai na faɗawa Papi ya faɗa maka zan zauna a gidanka idan ka yi aure, sai shi kuma ya ce na faɗa maka ka yi aure."
Bunayd darawa yayi É—an dai-dai sannan ya ce, "Autan dole ba wayo, kar ki damu zan yi aure soon, yanzu dai ki taya ni nemo matan kin ga ban da budurwa."
Majeeder har da stallenta an ce ta taya sa nemo mata, "Sweet bro ka yi wanka ka zo na shafa maka wani labari."
Bunayd dariya yayi ya shige ɗakinsa da ke sashin Affa General, Majeeder kuwa ta zauna tana jiransa, tana ta danne danne a wayansa, photo's take ta kallo, wani idan ta gani sai dai ta dara, har Bunayd ya gama wanka ya shirya, sannan ya mata magana ta shiga ɗakin ita ma, zama tayi a kan gadonsa ta ce, "Sweet bro ban ga photon kowa a wayanka ba balle na taya ka zaɓan matan."
CAS ya ce, "Autan dole ai ke za ki nemo mini, amma fa bana son masu saka hijabin nan, wacce dai ta waye hakan nan, ta fi ki wayewa fa, dan ke nistasttiya ce."
Majeeder dariya tayi ta ce, "sweet bro wasa kake mini ko."
CAS Bunayd ya ce, "To bani labarin da kika ce za ki bani, tunda ba za'a barni na huta ba za'a cika ni da hira."
Murmushi Majeeder tayi ta ce, "Da ɗumi-ɗuminta ai ta fi yaya, kar ta huce makwabta su ji baka ji ba, kuma kai ne baka zuwa shiyasa ba zan iya haƙura ba."
"To nidai bani labarin dan bacci nake so nayi" CAS ya faÉ—a yana kwanciya a gadonsa."
Majeeder ta ce, "albirshir yaya."
"Goro fari tass kaman Suhaila ba kaman ke ba."
Cunna baki Majeeder tayi, sai an ce bata da haske sosai ita, cewa tayi, "To Papi ne ya ce mini zai kawo mini Aunty kuma Mami zan dinga ce mata, kuma har da ƙawa za ta taho mini da ita, yanzu ai ba dan ƙawata ƙanwarka ba ce, da sai ka aureta, ni nasan mai kyau ce ita daga sunanta, Faɗima Banafshaaa, kuma fa ita ma wai a musabaƙansu ita ta zo ta ɗaya."
Bunayd ɓata fiska yayi ya ce, "tashi ki tafi zan yi bacci."
Majeeder sturut! Ta miƙe ta ce, "Na tafi da wayan sweet bro sai ka tashi."
CAS idanuwansa a lumshe ya ce, "je ki da shi."
Majeeder juyawa tayi ta fita da wayan, ita bata lura da yanayin Bunayd ma ya sauya ba akan magananta, shi kuma guntun tsaki ya ja ya ce, "To ban taɓa tsanan mutum ba, amma har kin saka naji haushin yarinya na staneta, ni ma haɗina da Ustaziya wacce har musabaƙa take yi" yana cikin magana sai ga kira ga shigo a ɗaya wayansa, yana mita ya ɗauka bai ma duba waye ba ne.
Maganan da aka yi a ɗaya ɓangaren ne ya sa shi dan taɓe baki, cikin yaren Yoruba yayi magana, ya ce, "aikinka ya jima da kammaluwa, mun yi magana da baturen, sun amshi contract ɗin."
Mr Sonny Yoruba, a ɗaya ɓangaren cewa yayi cikin Yorubanci, "Ok nagode CAS, yaushe za ka shigo? Ko kuma ni yaushe kake free na shigo."
Taɓe baki CAS yayi ya ce, "ina Kano kuma zan yi kwanaki, duk abinda ake ciki ka ƙira ni ko kuma ka mini magana ta WhatsApp kawai...", Haka suka gama tattaunawa suka yi sallama.
Bunayd ya gyara zai yi bacci sai ga ƙiran Abeed, guntun tsaki ya ja ya ɗauka tare da karawa a kunne ya ce, "Jarababben Ango ya aka yi? Ka bi ka dameni da kira ina hutawa, idan kai maye ne fa ka kama kurwan mutum to sai ka kashe mutum zai samu sukuni."
Abeeb taɓe baki yayi a nasa ɓangaren ya ce, "Da alaman dai wani ya taɓo ka, ba sallama sai surutu haka, duk da daman kai kanari ne, to faɗa mini me ya faru."
CAS ajiyan zuciya ya yi sannan ya ce, "Yanzu Majeeder ke shirin ɓata mini rai wai ai Papi zai ƙara aure kuma za a taho mata da ƙawa."
Dariya Abeed yayi ya ce, "Soyayyan Mom ta mosta kenan, shi ne kake taya ta kishi, dan za'a mata kishiya."