← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 58

Sashe 29

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da safiya tayi, Mami jin shirun tayi yawa, sai ta ɗauka ko yau Banafsha rigimanta ne ya mosta, da kanta tayi ayyukanta ta yi wanka chass abinta, Alhaji kam ya koma bacci daman baisan me ake ciki ba, Mami ganin dai har lokacin ba mostin Banafsha kuma lokacin makaranta ya wuce, sai ta nufi ɗakinta tana surutu, tana tura ƙofan ɗakin ta shiga ta samu Banafsha yashe a stakar ɗakin a sume, salati Mami ta rafka dan sai yanzu ta tuno lokacin al'adan Banafsha ya yi, month nata ya zagayo, cikin damuwa ta fice ta ɗauko ruwan zafi, shafa mata a fiska Mami tayi, sannan ta sa mata a baki, ruwan na kai wa maƙoshinta ta sauƙe wani wawan ajiyan zuciya, a hankali ta buɗe idonta da suka rine saboda azaban ciwo, ruwan zafin Mami ta bata ta sha sosai kaman ba mai zafi ba ko cire baki bata yi ba sai da ta shanye tass, sannan ba jimawa ta dinga kwarara amai, sai lokacin ta samu salama dama-dama ta koma ta kwanta, Mami sai aikin jera mata sannu kawai take yi, a haka ta tashi ta gyara wajan aman da ta yi, ta cire mata kayanta suka shige toilet ta gyara mata jikinta, sanin ba lallai in tayi sallahn asuba ba, sai ta mata alwala, suna fitowa ta shiryata staff ta saka mata hijabinta, a haka a zaune ta ce tayi sallahn kamun taje ta taso Alhaji su tafi asibiti, Banafsha amsawa tayi da kai, Mami ta fice.

Ya Danish na zaune a ƙofan gida har su Umaima suka fito, yana tunanin ko za su biyawa Banafsha amma sai suka wuce abinsu, Ya Danish bai san idan yana ƙofa Umaima bata biyawa Banafsha ba, haka suka yi tafiyansu da Nana, sun je makaranta ana ta karatu Umaima ta zuba ido ta inda Banafsha za ta ɓullo amma shiru, haka malamai suka shigo har Malam Abbo ma aka musu darrusa har aka tashi ba Banafsha ba alamanta, Umaima duk ta bi ta damu dan tasan idan ba wani abun bane ya faru to Banafsha ba za ta ƙi zuwa makaranta ba.

Ɓangaren Malam Abbo ma bai ji daɗi ba dan gani yake shi ya ja mata rashin zuwa makaranta, sai duk abin ya bi ya damesa, ko da aka tashi ya daure dai bai tambayi Umaima ba yana tunanin zuwa yamma Banafsha za ta zo, dan Maminta ba za ta barta ta zauna a gida ba.

Ya Danish har ya gaji da zama ya shige gida, har su Umaima suka dawo, shiru ba giftawanta, Umaima ma ko da suka dawo ba ta shiga gidan su Banafsha ba, ta bari sai zuwa yamma dan tana tunanin ko wani abun ne ya kuma faruwa tsakanin Banafsha da mutanen Mami ya sanyata fushi taƙi zuwa, bata son taje dubo Banafshan kuma ta kalleta cikin damuwa, sai tayi zamanta cike da kewan ƙawarta aminiyarta.

Mami É—akin Alhaji ta shiga da damuwa ta tashesa a baccin, faÉ—a masa abinda ke faruwa ta yi, Alhaji da yake shi ma yasan da ciwon Banafsha, cikin hanzari ya shige banÉ—aki ya wanke fiska, bai yi kowa wanka ba ya zura jallabiyansa ya fito, Mami ta shiga ta samu Banafsha ta idar da sallahn, kamota tayi suka shige motan Alhaji, shi kuma ya ja sai asibiti, duk da safiya ne amma Allah ya taimakesu da yake asibitin kuÉ—i ne kuma babban asibiti ne, likita yayi attending nasu an mata alluran da aka saba mata, aka basu magani sannan suka juyo gida, suna dawowa kuma ba jimawa jinin ya zo, nan ma É—in wani ciwon maran ne dan sai Mami ne ta gyara mata jikinta staff, haka suka wuni cass! Alhaji daman sai Monday zai koma dan haka yana gida, Mami sai kula take da yarinyarta tana mata addu'an Allah ya yaye mata wannan ciwon maran jaraban.

Yamma na yi bayan ya Danish ya shirya tafiya ya fito ya staya a waje, nan ma dai shiru har su Umaima suka kuma wucewa yana wajan, saboda ganinsa Umaima bata yi gigin zuwa gidan su Banafsha ba, ya Danish gajiya yayi ganin su Umaima suna dawowa an tashe su ma, sai ya ja guntun tsaki ganin babu ita ya shige motansa yayi tafiyansa ko sauraran abokinsa IB bai yi ba.

Umaima kuwa suna zuwa makaranta nan ma babu Banafsha har aka tashi, cikin damuwa dai Malam Abbo ya tambayeta ƙawarta ko lafiya bata zo ba, Umaima ta faɗa masa bata sani ba dan bata dubo ta ba, amma za ta duba ta, amsawa Malam Abbo yayi yana addu'an Allah ya sa lafiya, Umaima suna komawa suka samu sai lokacin ya Danish zai tafi, shigewa gida suka yi, ta ce sai ya tafi da anjima za ta je ta dubo masoyiyarta.

Sai da suka yi sallahn Magrib sannan Umaima ta samu Ummu ta ce, "Ummu zan je wajan masoyiya Banafsha, yau kwata-kwata safe da yamma du bata je makaranta ba bansan me ya faru ba."

Jinjina kai Ummu tayi cikin damuwa ta ce, "To Allah ya sa dai ba wani abun ba ne ya faru kuma, wannan yarinya Allah bata miji nagari inda za ta huta, Allah dai-daita mata lamuran mahaifiyarta."

"Ameen Ummu ba na je, sai na dawo."

"To ki dawo lafiya, ki ce ina gaisheta, idan ba komai ki dawo da wuri saboda Abbaa kada yayi faÉ—a kin fita da Magrib, idan kuma wani abun ne ki kwana can zan faÉ—a masa, Allah muki albarka dukanku ko" faÉ—in Ummu.

Umaima ta miƙe tare da cewa, "Ameen Ummuna" ta fice a ɗakin, tana ƙoƙarin fita a ƙofan palourn su ta jiyo muryan Umma na faɗin, "Ina za ki je da daren nan bayan anyi Magrib? Abbaanku bai hana ku fita da dare ba?"

Umaima tura baki tayi ta ce, "Na faÉ—awa Ummu fa, kuma wajan Banafsha zan je ni, yau bata je makaranta ba kwata-kwata bansan ko bata da lafiya ba."

Wani kallo Umma ta mata ta ce, "Ita wacce kika faɗawa ita ce uwarki ko ubanki? Umaima zan yi mugun saɓa miki fa, wallahi ki fita a idona na kulle, na ce sannu Uwar Banafsha, ke ce karuwa uwar Banafsha ƙarshenta kenan, to maza ki juya ki koma ɗakinki, idan kika fita a gidan nan yau ba wanda ya isa ya hanani karyaki, ba dai kinga Danish ya tafi ba ko? Shi ne za ki stiro da wani hali, kullum na miki magana bakyaji, to ni nan zan karyaki, wuce ki koma kamun na taso" Umma ta ƙarishe maganan da mugun stawan da sai da Umaima ta ɗan firgita, tura baki tayi ta wuce ɗakinta tana kuka an hanata dubo Banafsha, Umma kuwa ƙwafa tayi ta koma ta zauna ta ga ta inda Umaima za ta fita, duk abinda ya faru Ummu ta jiyo amma sai ta yi shiru, ko ba komai ba'a shiga tsakanin uwa da ƴa, da gaskiyanta ita ce mahaifiyarta ta fi ta iko da Umaima, jan baki Ummu tayi ta yi shiru akan zuwa gobe Insha Allahu ita da kanta za ta je ta dubo Banafsha ɗin.

Washegari Monday bayan Umaima ta shirya tafiya makaranta kasancewan Monday ne suna da class na safe, sai Umma ta fito, mugun kallo ta bita da shi sannan ta ce, "Umaima kina fita ki wuce makaranta, idan kika kuskura kika bi gidansu yarinyar nan wallahi ranki zai yi mugun ɓaci, bana son shashanci, idan mutuwa ta yi ma ina ruwanki? Ko akwai wanda aka ce ba zai mutu ba ne?"

Umaima yanzu ma tura baki tayi haka ta fice, tana kallon gidan su Banafsha tana son zuwa amma tana storon Umma, haka ta wuce ta tafi makaranta, kaman yanda ta yi tsammani kuwa ba ta ga Banafsha a boko ba har suka gama class nasu wajan ƙarfe huɗu ta dawo gida, nan ma dai ba daman zuwa tana storon Umma haka ta shige gida, tana shiga kuwa ta samu Umma a palour, wani kallo Umma ta mata ko amsa gaisuwan da take mata bata yi ba ta ce, "kinje gidan ƙanwar uwartaki ko?"

Umaima girgiza kai tayi ta wuce kawai, Umma ta yi ƙwafa ta ce, "Ya fi miki, ai da kinje wallahi sai na kusa karyaki, kuma ki gama abinda za kiyi maza ki fito ki shirya ki tafi tahfiz, kuma kika sake kika bi gidansu sai na miki baki."

Umaima haka ta ci abinci ta yi sallah ta wasta ruwa, sannan ta shirya ta wuce islamiyya, yau ma shiru ba Banafsha ba alamanta, Malam Abbo duk ya bi ya damu, ga shi yana son ya bata sato guda tukunna ya kuma komawa, bayan an tashi ya tambayi Umaima lafiya kuwa ko akwai wani abun da ya hana ƙawarta zuwa makaranta, Umaima kaman za ta yi kuka ta ce bata samu zuwa ba, amma Insha Allah anjuma za ta je.

Malam Abbo cikin damuwa ya ce, "Allah ya kai mu anjuman, ki faÉ—a mata ina gaidata, na yi kewanta" yana gama faÉ—a ya wuce.

Umaima da kallo ta bi Malam Abbo, duk mamaki take yanda ya bi ya damu haka shi ma, duk da dai tasan masoyiyarta tana da shiga ran duk wanda ya zauna da ita saboda halinta masu kyau, haka Umaima ta juyo gida ita kaɗai da aka tashi, nan ma Umma ta kuma faɗa mata kada ta kuskura ta ce za ta je gidan su Banafsha, Umaima ko Ummu bata yi wa magana ba taja bakinta tayi shiru, sai da Abbaa ya dawo wajan isha'i sannan ta miƙe saɗaf-saɗaf ta tafi sashinsa, da sallama ta shiga.

Abbaa yana murmushi ya amsa mata ya ce, "shigo ko Umaimatun Abbaa."

Umaima shiga tayi ta samu waje ta zauna, gaishe da Abbaa tayi ya amsa, ta amsa sannu da dawowa.

Abbaa ya ce, "Ya aka yi Ummul-khultum kaman akwai magana a bakinki? Wa ya taɓa mini ke?"

Umaima sarkin taɓara, tura baki tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Umma ce Abbaa."

Murmushi Abbaa yayi ya girgiza kai dan yasan za'a rina, yana kallonta ya ce, "ya aka yi? Me Ummanki kuma ta miki?"
Chapter 29 · 0% Book details