← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 58

Sashe 31

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji barin abinda yake yi yayi ya shafa kanta tare da kamo hannunta ta zauna a kusa da shi, yana murmushi ya ce, "Mai jiddan babanta kina so idan kika tafi na zauna ni ɗaya ne nima? Kina son damuwa ya yiwa babanki yawa? Ke nake gani a gidan nan naji sanyi a rai na, ki yi haƙuri ko, in Allah ya yarda komai zai wuce, na kusa kawo miki Aunty da kuma ƙawa abokiyar hira, ba dai kina son ƙawa ba?"

GyaÉ—a kai Majeeder tayo ta ce, "Eh Papi ina so."

Murmushi yayi ya ce, "yauwá na kusa kawo miki ƙawa, kuma auntynki har da ƙanne za ta haifa muku, Mami za ki dinga ƙiranta ma, ƙawarki kuma sunanta Faɗima amma ana ce mata Banafsha, ita ma ta sanki, kuma tana son ƙawance da ke, su ma da suka yi musabaƙa a makarantar su ita ce ta zo ta ɗaya kaman yanda kika zo ta ɗaya."

Majeeder da murna da farin ciki ta ce, "Wayyo Papi ina sonta sosai, dan Allah a kawo su da wuri, nima a mini ƙanne, ka ga sister Ramla ma da ƙannenta, Suhaila da Nabeela."

Alhaji dariya yayi ya ce, "kinsan me Maman babanta?"

***
Masu Sharhi ina godiya, waɗanda basa yi ma na gode amma dan Allah a ƙara himma, kunga jiki da jini sai a hankali sharhinku ke bani ƙwarin guiwan yin typing balle yanzu da bana jin daɗin jikina sai a hankali, Uwar batoorl taku ❤️ masu daraja habibties.

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE
Ɓingel kabi
Heartbeat
Hafsat Umar
Habiba muhammad Yusuf

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

Ba editing ayi haƙuri da typing errors.

🅿️ 51 _ 55

Majeeder girgiza kai tayi ta ce, "A'a Papi."

Alhaji ya ce, "Sunan Maminki ke da ƙawarki ne Ramla, dan haka ki daina ƙiran sunan kinji."

Jinjina kai Majeeder tayi, tana murmushi ta ce ta daina, Alhaji ya ce, "good girl, kuma su General É—in ma suna zuwa in Allah ya yarda nan da next week, inyaso idan kuna hutu a school ba lectures sai ki je can ki yi hutunki, saboda nima zan yi tafiya kuma zan iya kai 2 month's kamun na dawo."

Majeeder washe baki tayi ta ce, "Allah ya kai mu lafiya, Allah kai ka lafiya ya
dawo da kai lafiya, Allah kawo su yaya lafiya, finally zan ga yaya Bunayd bayan stawon lokaci, gaskiya ni Papi ka faɗawa yaya idan yayi aure ni gidansa zan koma da zama" ta ƙarishe maganan kaman za ta yi kuka.

Alhaji murmushi yayi ya ce, "Idan kika koma gidansa ke kuma wa zai zauna miki a naki gidan? Maman babanta."

Majeeder tura baki tayi ta ce, "Ni dai Papi sai na koma gidan yaya da zama."

Alhaji ya ce, "Shikkenan Allah basa mace tagari, sai kuma ki masa magana ki ce yayi aure, ni kuma sai ma faÉ—a masa za ki koma gidansa da zama ko?"

Majeeder na murmushi ta gyaÉ—a kai, hira Alhaji ya dinga janta da shi har bacci ya É—auketa a wajan, tashuwa yayi ya gyara mata kwanciyanta, sannan ya ci-gaba da aikinsa hankali kwance, cike da kewar Ramlatunsa.

⭐
CAS Bunayd mancewa yayi da maganan zuwa Kano, ya shirya ya bar Nigeria, daman shi kaman network haka yake ba tabbatas, yau yana Nigeria gobe kuma yana wata ƙasar, musamman ma da yake Sojan sama, kuma yawancin ƙasashen da yake zuwa yana da gida a can, kuɗin gaske Bunayd yake da shi, ko iyayensa ba su kai sa kuɗi ba.

Yau kuma a ƙasar Spain ya sauƙe zangonsa, jirginsa na sauƙa drivernsa ya zo ya ɗauke sa, a gaban wani tankamemen gida motan nasu ya staya, da wani button ake buɗe gate na gidan, ana buɗe musu suka shiga, mota na parking Bunayd ya buɗe da kansa ya fito, cikin takunsa na isa ya ƙarisa bakin ƙofan shiga gidan, ƙofa ne mai amfani da numbobi (password) wajan buɗewa, sai da ya saka sannan wani murya kaman na yara ya ce, "welcome" ƙofan ya buɗe ya shige.

Subhanallahi! Gida ne na gani na faɗa, stayawa faɗan staruwan gidan da haɗuwansa ma ɓata baki ne, direct ɗakinsa ya wuce ya wasta ruwa ya sauya wasu haɗaɗdun kayan sannan ya fito, a babban palourn ya samu wata dattijuwar baturiya ɗauke da tray, cikin turanci ta gaidasa, Bunayd ya amsa mata ba yabo ba fallasa, faɗa masa tayi ga abinci, lumshe ido yayi kawai bai ce komai ba, saboda ya sha faɗa mata tabar wahalar da kanta masa girki ko ya zo, indai yana buƙatan abu zai mata magana, amma dattijuwar muddin ya zo ƙasan to sai ta masa abinci, faɗa mata yayi ya ƙoshi sai ya dawo zai ci, yana gama faɗa yayi gaba, a wata haɗaɗɗiyar mota baturen drivern nasa ya ja sa suka tafi inda ya faɗa masa.

Wani irin haɗaɗɗen wajan shaƙatawa ne, ba abin da babu a wajan, gefen eatery, club, bar, hotel, swimming pool etc.
Bunayd wajan pool ɗin ya nufa, irin kujera mai kama da resting chair haka nan ya samu ya zauna, matan turawa sai zirga-zirga suke, daga masu swimming-wear sai masu pant da bra kawai, Bunayd kallon ma na rigima da isa yake yi, idan ya kalli wannan ya taɓe baki, idan ya kalli wannan ya runste ido, idan ya kalli wannan ya yi murmushi kawai, wayansa ya ciro tare da dialing layin general, a ɓangaren General daman ya gama gwada layin Bunayd na Nigeria bai shiga ba, rasa layin wacce ƙasa zai fara ƙira yayi, sai kuma ga ƙiran Bunayd ɗin ya shigo, amsawa yayi yana murmushi ya ce, "ɗan halak ya ƙi ambato."

Murmushi ƙayatacce Bunayd yayi ya ce, "Affa Barka da gida."

General ma murmushin yayi ya ce, "Yau kuma kai ne da ƙiran Affa? To ban amsa ba ka faɗa General ya fi daɗi, Affa haka kaman wani stoho, General ya fi ana ji ansan matashi ne ni ba stoho ba."

Bunayd murmushi yayi sosai har sai da fararan haƙoransa suka bayyana, dimples nasa suka losta, cewa yayi, "Affa ai daman kai ba stoho bane, Sir ne dai stoho."

General ya ce, "Yaya dai ya ce ka daina ce masa Sir, yauwa daman yanzu nake ƙiran layinka naji shiru na ce ka tafi kuma."

"Eh amma 2 day's kawai zan yi na dawo, akwai abinda na zo yi ne mai muhimmanci."

General ya ce, "ai ko yawonka ma mai muhimmanci ne kai kam my Man, yanzu dai ka tabbatar ka dawo nan da kwana biyun saboda tare nake so muje Kano dukanmu."

Dafe kai Bunayd yayi ya ce, "Ni na manta ma ai General, amma dai gobe zan dawo in Allah ya yarda, daman auren Abeed ma ya kusa may be na zauna har a yi bikinsa."

"Ok! Allah dawo da kai lafiya Man, daman nasan yawo ka je ba aiki ba, kai ai ko stunstu ya ganka haka ya ƙyaleka, Allah ya sa ka haɗu da taka matar a wajan auren Abeed ɗin."

Murmushi kawai Bunayd yayi bai ce komai ba, ci-gaba da wayansu suka yi kaman abokanaye ba uba da ɗa ba, sai da suka gama suka yi sallama ya kashe wayansa, wata baturiya ne ta zo wajan tare da miƙa masa sabbin kaya a ledansu, amsa yayi ya je ya sauya ya zo ya shige ruwan shi ma, tunda ya shiga ƴammatayen ciki suka fara yiwa wa kansa, Bunayd murmushin mugunta kawai ya yi dan shi kaɗai yasan abinda zai yi, wayansa da ke wajan kujera ne ya ɗau suwwa, drivernsa da ke staye a gefe shi ya miƙo masa, kara wayan yayi a kunnensa ya ce, "ina pool Abeed, idan na gama zan ƙiraka."

Dariya Abeed yayi ya ce, "CAS ka ce kaje bawa idonka abinci, musulmin É—an jagaliya ba, kai daga can sai can, kuma duk ka gama yawo ka dawo ka ce matan ba su gama sanin duniya ba, to nidai maganan serious ne kawai mu yi ta yanzu ba wani sai ka gama, inba dai Chaji kake yi ba."

Ɓata rai Bunayd yayi ya ce, "Amma dai ka gama da ni wallahi, yanzu har akwai macen da za ta iya mini Chaji a Spain? Ƴan banzan da duk Palace nasu yake a salafce ba ɗumi, zan je ina Chaji ina gane akwai mutane a duniya ne, ai full definition of Chaji shi ne wanda kana yi baka sanin kowa yana existing, duka matan Spain ƙauyawa ne, yanzu ma so nake na ɗura wa wata ruwa."

Dariya Abeed yayi sosai ya ce, "To ko ba Palace kake Chaji ba nasan ko kana taɓa biyu kyauta milkies."

Guntun tsaki Bunayd ya ja ya ce, "Duka matan Spain ƙwailaye ne, ba wacce milkieynta yayi girman da zai ishi CAS Bunayd, wasunsu ƙirjin ma kaman an shafe sa, abu kaman ƙwallon cashew, da dai akwai mai kaman Mango ko Orange ai na iya lallaɓawa, amma duk abu ba kyawun gani, kuma fa yanda suke yawo hakan nan gani suke sun ƙure adaka suna da kaya load-load back an front, kai Allah mun gode maka, kuma mun tuba, Alhamdulillahi da ba mu fito a cikin turawa ba, haba dan Allah sai kaga mace kaman boss a dire kawai ba shape, baya ba tudu ƙirji ba tudu, daga kyawun fiska har na sura ana cire matan larabawa da na indiyawa to sai matan Africa, ni kwata-kwata turawannan ba burgeni suke ba, ƙauyanci ya musu yawa basu waye yanda ya kamata ba, bari na ɗurawa wata ruwa zan ƙiraka" Bunayd ya faɗa lokacin da ya ji wata na shafasa.

Abeed dariya yayi ishashshe ya ce, "Baka da kirki, nasan ba zai wuce an ɗan rungumeka ka ji ɗumi ba, ka ci-gaba da dannawa beb's na mutane ruwa a pool, wataran sai ka kashe wata saurayinta ya ɗaureka, bar ganin kai Soja ne, law's na ƙasashen turawan nan sam bai da daɗi, ba tausayi ba sassauci mugaye ne."
Chapter 31 · 0% Book details