← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 58

Sashe 27

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitan su Danish Abbaa ya kalli Umma ya ce, "Sabeera na ƙara dawowa kan ki, ki sani kema abinda kika aikata zan ɗau mataki a kansa ba wai na yi shiru ba ne, matar dai da kika bi kika gallazawa kanki akan ta kuma bata san kina yi ba, to ina so ki sani ita zan auro, wataƙila idan na aureta to za ki dawo hanya ki koma hayyacinki, yarinyar ma nan za ta dawo da zama, kuma kika kuskura kika ce za ki aikata wani rashin hankalin to zan nuna miki abinda ke kai na ya fi naki, ai mutum ba shi yake yin kansa ba, dan mahaifiyarta na zaman kanta, ai ba yana nufin a staneta a stangwameta ba, ko akwai wanda yake zaɓawa kansa daga cikin iyayen da zai fito? Kowa da kike gani Allah ne ya riga ya gama stara komai a kansa tun fil'azal, dan haka ki dawo hayyacinki, bai kamata ke da za ki yiwa wasu faɗa, a ce ke da kanki kike aikata hakan ba, idan kuka tsamgwami yarinya kuka dinga kyamatarta, wani hali kuke tunanin za ta faɗa? Ai sai ta zaɓi ita ma ta shiga duniya tunda haka al'umma ke mata kallo, duk irin munin halin mutum, maganin zama da shi ake sha, sannan a ja shi a jiki a dinga nusar da shi gaskiya ana nuna masa abinda ya kamata, amma idan aka dinga ƙuntata masa to gaba-ɗaya ba za'a ribatu da mutum ba, yanzu idan yarinyar nan ta lalace kuma wani a yaranki ya bi ta shi ma ya lalace ya za ki ji? Kuma wa gari ta waya? Amma idan ta shiryu bata lalace ba ai ko ke hankalinki a kwance kinsan yaranki ba za su bita da ɓatanci ba idan ba maganan arziƙi ba, ba'a kyamar mutum ko ƙuntata masa ko da kafiri ne balle kuma musulmi wanda ya ke salla kai ma kake sallah, ya ambaci Allah da Manzonsa kai ma ka ambaci Allah da Manzonsa, akwai wani kissa na wani sahabin Manzon Allah SAW da ya kwanta mini, amma dai shi ma akwai wani abu da yake yi wanda ya zamana mutane na ƙyamatan shi, amma Annabi ya nusar da su hakan ba kyau ya ja bawan Allahn a jiki, daga ƙarshe sai da ya zama sahabi mayaƙin Annabi SAW wanda ake ji da shi, to ba'a rena ɗan Adam duk yanda ya je kuma ba'a ƙuntata masa, misalai dai da yawa akwai su kuma Annabi da kansa yayi magana akan hakan, dan Allah dan Annabi ki kiyaye Sabeera, wannan yarinya tamkar Umaima haka take a wajanki, Ummu-khultum ke ma abinda ya sa na ajiye ku, duk so nake ku gyara, mu gudu tare mu stira tare, duk da bantaɓa jin kin yi musu wani abun da ba dai-dai ba amma a kiyaye saboda zuciya watarana sai a hankali, kuma ku yi haƙuri amma zan ƙara aure, Insha Allahu dai ita Maman Banafsha zan aura, fatan za ku bani haɗin kai kuma ku ci gaba da tayani da addu'an alkairi."

Ummu tana murmushi ta ce, "Allah taimaka ya kuma tabbatar da alkairi, Allah shige mana gaba ya sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu, Allah kuma ya baka ikon yin adalci."

Murmushi Abbaa yayi ya amsa da Ameen, sannan ya dubi Umma ya ce, "Sabeera ke kuma ba ki da abin cewa ne?"

Umma cikin fushi ta miƙe fuuuu! zuciyanta na tafarfasa kaman za ta kifu akan Abbaa ta ce, "yanzu dan ka gama rena mana hankali ka rasa wa za ka auro sai gantalalliyar karuwa da ta gama yawon karuwancinta, wa ma ya sani ko tana ɗauke da ciwo, ka zo ka aurota ka raɓa mana, to wallahi ba da ni ba, kuma ban yarda ba ban amince ba, idan ma auren za ka yi jaraba na damunka ba ka godewa Allah da mata biyun ba, to sai dai ka auro wata amma banda wannan wastatstsiyar" tana gama faɗa ta fice.

Abbaa murmushi kawai yayi ya sallami Ummu, ya kwanta abinsa ba damuwan komai a zuciyansa, ransa wasai, sai addu'an fatan alkairi da yake yi, da kuma Allah haÉ—a yaransa da mata nagari.

Ya Farooq farinciki yake abinsa bai da damuwan komai, daman budurwansa ta faÉ—a masa an ce ya turo, yana niyan yiwa Abbaa magana kenan ya musu wannan magana, shi dai ya Danish cin rai kawai yake yi, shi yana da budurwan amma gaskiya ya rasa dalili tunda incident É—in nan ya faru stakaninsa da Banafsha, sai ya fara jin haushin budurwansa haka kawai, ga shi tunda ya zo weekend É—in nan, gobe Sunday zai koma amma ko kallonta bai yi ba balle ya mata wani mugunta, dan shi bai huce ba har yanzu, Ya Farooq na masa magana ma amma ko kula shi bai yi ba, kuma bai shiga cikin gida ba dan baya son surutun Umma.

Ina kwance na gaji da kwanciya na miƙe nayi ayyukan da ya kamata, wanka na shiga na gama na shirya, ina zaune shiru ni ɗaya a gida har nayi sallahn Magrib su Mamina ba su dawo ba storo ma ya bi ya cika ni, kaman nayi kuka haka nake ji, ga shi banda waya balle na ƙira Mamina, da ace ba weekend bane sai na shiga gidan su Umaima, amma weekend ne bana buƙatan haɗuwa da Ya Danish dan nasan yanzu haka ba zai wuce ma suna ƙofan gida ba, haka na daure na zauna cikin storo.

Malam Abbo sai da ya shirya zuwa wajan Banafsha abincin ruhinsa, sannan ya bi masallaci yayi sallahn Magrib, ana idarwa ya tashi ya kamo hanya cike da addu'an Allah bashi ikon furta mata soyayyansa, kuma Allah ya sa ta amsa, dan sosai take masa kwarjini, Malam Abbo ba ƙaramin kwalliya ya ci ba, ga wani ƙamshi da yake yi na musamman, Malam Abbo haɗaɗɗen matashin saurayi ne wanda ba macen da sa ta kallesa bata ji ya burgeta ba, cikin tafiyarsa na nistuwa yake taku har ya iso ƙofan gidan su Banafsha, kuma ya wuce su ya Danish a ƙofan gidansu, ya Danish kallo ɗaya ya masa ya ganesa, shi ne saurayin da yake ganinsu tare da Banafsha, tuni wani haushi ya rufesa da ya tuna abubuwan da ta ke masa, ga shi ranan bai samu ya koya mata hankali ba, ƙwafa yayi ya bi Malam Abbo da harara.

Dai-dai isowan Malam Abbo ƙofan gidan su Banafsha, dai-dai isowan motan Alhaji sun dawo daga anguwa da Mami, Alhaji da kansa ya sauƙa ya buɗe gate ya shige cikin gidan, Mami da yake ta kalli Malam Abbo, sai ta faɗawa Alhaji ai malamin su Banafsha ne ya masa iso, ta juya ta shige ciki shi kuma Alhaji ya fice waje, Malam Abbo yana ganinsa ya fara fara'a, cikin mutuntawa suka yi musabaha suka gaisa, sannan Alhaji ya masa iso suka shige cikin gidan.

Mami na shiga ta sameni zaune sturu-sturu da idanuwa kaman an tare kule a buta, duk a storace nake, murmushi tayi ta ce, "Sannu da gida Æ´ar Mami mai storo."

Ina murmushi na tashi na rungume Mamina na ce, "sannunku da dawowa Mamina."

"Yauwa FaÉ—iman Mami, ki shige ki sako hijabi dan naga malaminku ya zo" Mami ta faÉ—a tana nufan É—akinta.

Ajiyan zuciya na sauƙe dan storo ya tafi tunda Mami ta dawo, ɗakina na wuce ina murmushi dan sai yanzu da Mami tayi magana sai na tuna Malam Abbo ya ce zai zo gidanmu, amma mamaki nake da zuwan da yayi da dare da kuma ko me ya kawo sa Allahu a'a lamun, nidai ya ce akwai maganan da za mu yi, addu'a nake Allah ya sa alkairi ne, kuma Allah yasa ba wani laifin na aikata ba.

Alhaji tare da Malam Abbo suka shigo palournmu, waje Malam Abbo ya samu ya zauna, Alhaji ya shige ɗakin Mamina ya faɗa mata malaminnamu ya shigo, Mami ta amsa shi kuma ya wuce ɗakinsa, Mami cikin kamala ta fito da hijabinta, Malam Abbo kuwa cikin ladabi ya durƙusa ya gaidata yana ya sunne kai, Mami amsawa tayi da fara'a bata ce komai ba ta dai ce bari ta ƙira masa faɗima, ya amsa yana mai sunkuyar da kai cikin kunya.

Ni kuwa ina shiga ɗakina haka kawai na stinci kai na da ɗan gyara fiska na, na shafa humrana sannan na ɗau hijabina na saka, ba ƙaramin kyau nayi ba ga shi har da man baki da kwalli na saka, Mamina ce ta shigo ɗakin da sallama, kallona tayi ta girgiza kai ganin har da kwalli na saka, murmushi kawai tayi ta ce, "Idan kin gama kwalliyan to yana jiranki" tana gama faɗa ta fice tana murmushi dan yanzu ta fara harbo jirgin abinda ke shirin faruwa, Banafsha har da kwalliya, shi kuma malamin nata sai sunne kai yake kaman mara gaskiya.

Mamina na fita na tsaya na gama dariyana sannan na tattaro nistuwata na fice palourn ina mai jin wani iri haka kawai, ina isa da sallama ya amsa mini, waje na samu na zauna a ƙasa, amma yau Malam Abbo ya dage firr! Sai na zauna a sama, haka ba dan naso ba na zauna a sama ina cusa fiskana a cikin hijabina, da hijabin a bakina na gaishe sa muryana yayi wani iri, shi kuma ya amsa yana kwaikwayon muryan nawa yanda yayi, sai abin ya bani dariya kawai na ɗan murmusa nayi shiru tare da yin ƙasa da kai na, ina wasa da yastuna.

Malam Abbo can da shirun yayi yawa sai yayi gyaran murya ya ce, "Malama FaÉ—ima yau ba ruwan sha ne, abin rowa aka fara mini."

Kunya na ji na miƙe da sauri, ni gaba-ɗaya na sha'afa ma, wucewa nayi kitchen na haɗa masa abin taɓawa har da tuwon dare da nayi, na ɗauko cikin nistuwa na zo na ajiye masa agabansa, murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "ina godiya Malama Faɗima Allah ya yi albarka, sannu da ƙoƙari."

Ina sunne kai na amsa da ba komai, sannan na ce, "ka taɓa abincin dai malam, ka ji girkin ɗalibarka."
Chapter 27 · 0% Book details