Sashe 26
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin raha da ɗan faɗa-faɗa Alhaji yayi waya da General har suka yi sallama kaman kada su kashe, General ma ya sanar da Alhaji za su shigo duka da yaran Insha Allah ba jimawa, Alhaji ya ce Allah ya kawo su lafiya, bayan sun yi sallama sai Alhaji ya miƙe dan tafiya ga masoyiyarsa, yana buɗe ƙofa zai fita ita kuma ta sako kai za ta shigo har kusan karo suka yi, kallonta yayi yana murmushi ya ce, "Na ɓata lokaci ko Hajiyata?"
Mami jinjina kai kawai tayi ta juya, ɗakin Mami suka shiga, Alhaji ya samu waje ya zauna, ta zauna gefensa, dukkansu shiru suka yi, sai Alhaji ne ya gaji da shirun ya ce, "Allah ya baki haƙuri, Allah ya huci zuciyanki Ramlatu."
Ajiyan zuciya Mami ta sauƙe ta ce, "Kai ma Allah ya huci zuciyanka Alhaji, in Allah ya yarda ba jimawa zan sanar da kai komai a kai na, ka yi haƙuri."
Murmushi yayi ya ce, "Bakomai Ramla, yauwa inason faɗa miki daman, bayan kyautan da zan wa Banafsha idan Allah ya sa result nata yayi kyau, to yanzu ina son kiyi haƙuri ki barta ta riƙe waya."
Mami ba tare da ta É—aura idonta akan Alhaji ba ta ce, "a'a Alhaji ba yanzu ba tukunna."
"Meyasa ba yanzu ba Ramla?" FaÉ—in Alhaji yana kallon Mami.
Mami ta ce, "Alhaji har yanzu Banafsha yarinya ce, bana son waya ya zama sanadiyyar lalacewan tarbiyan ta, nafi son idan ta samu miji to Masha Allah! Idan ya aureta sai ya saya mata, nan ba mastala matarsa ce, amma ni yanzu storon yarinya ta riƙe waya nake yi."
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Eh to wani gefen da gaskiyanki, wani ɓangaren kuma ba gaskiya a magananki, domin komai da kike gani a rayuwa yana da ɓangare mai kyau da kuma ɓangare mara kyau, tabbas a wannan zamani da muke ciki, ƙaramin abu ne yarinyarka a ɓata mata tarbiya ta waya, musamman ƙawayen banza da fasiƙancin neman jinsi yayi yawa, ko kuwa ɓata garin samari, amma fa ina son ki sani, wani a wayan nan zai iya shuka abin alkairin da zai kai sa aljanna, sannan wani a babu wayan ma yana iya lalacewa, addu'a ita ce ke stare komai ta kare kowa, Banafsha yanzu ba yarinya ba ce, ko saboda abinda ya shafi makaranta yana da kyau ki barta ta riƙe waya, yanzu suna final year nasu ne, to wani abun tana buƙatan waya."
Mami shiru tayi bata ce komai ba, ganin haka kuma Alhaji yasan me take nufi na bata yarda ba, sai kawai ya ƙyale maganan, nan suka kama hiransu kaman ba abinda ya haɗa su ɗazu har Mami ta fara gyangyaɗi, Alhaji ya ce su kwanta, ba jimawa Mami tayi bacci shi kuma Alhaji a sulale ya tashi ya fice a ɗakin.
Washe-gari da wuri Banafsha ta tashi sakamakon ranan asabar ne akwai zuwa tahfiz dan ba su da lecture ba za su shiga makaranta da wuri ba.
Banafsha na fitowa gida sai ga Umaima na ƙoƙarin shigowa nasu gidan, murmushi suka sakarwa juna, Umaima ta ce, "Masoyiya muyi sauri lokaci ya ƙure kada muyi latti."
"Aikam muka yi latti akwai mastala, yau ba shiga aji kenan sai dai mu dawo mu wuce College dan ba mai taɓa mini lafiyar jikina" na faɗa tare da riƙe hannun Umaima muna tafiya, muna hiranmu a haka har muka isa, Allah ya taimake mu ba'a fara tare lattin ba.
Mun yi karatun ranan mun gama har aka tashemu, mun fito muna tafiya ta hanyar da muke bi ta cikin anguwa, sai gani muka yi mutun ya tsaya stegege a gabanmu, ganin wanene dukkanmu sai muka haÉ—a fiska, Umaima ce ta buÉ—e baki tana hararansa ta ce, "Malam me damuwanka da mu? Yau kuma da me ka zo?"
Garba kallon sama da ƙasa ya yiwa Umaima ya ce, "ke mastalana da ke shishshigi ya miki yawa, ina ruwanki? Ko na miki magana? Na taɓa ƙiran sunanki? Dan Allah ki ƙyaleni nayi da wacce take gabana."
A zuciye Umaima ta buɗe baki za tayi magana amma sai na dakatar da ita, kallon uku saura kwata na wásta masa sannan na riƙe hannun Umaima muka wuce, amma still Garba ya ƙara stayawa a gabanmu, a hasale na ce, "ka ɓace mana a hanya."
Murmushi Garba yayi yana shafa suɗaɗɗen kansa da yaji askin tanƙwal ya ce, "stakani da Allah na kasa nistuwa, wallahi soyayyanki ta mini mugun kamu, ni ba ruwana da sana'ar babarki, dan Allah ki so ni, kiyi haƙuri da abinda na miki ranan."
Hararansa nayi kawai naja Umaima muka wuce abinmu, duk magiyan Garba ko ta kansa ba mu bi ba.
Muna komawa kuma muka shirya shirin tafiya makaranta, Alhaji ne ya kai mu bayan ya gama jinjina mana na ƙoƙarin da muka yi, ya ce da Umaima ma ta dage nan gaba kada ta yi bracket, mudai cewa muka yi mun gode, yana sauƙe mu muka shige school, class da muke da shi sai wajan ƙarfe sha biyu, mun yi kuma, mu ne bamu bar makarantan ba sai wajan ƙarfe uku na yamma, muna dawowa Umaima ta shige gidansu na shige namu.
Mami da Alhaji na samu suna zaune suna hiransu da fara'a, gaishesu nayi sannan na shige ɗakina, wanka nayi tare da yin sallah, duk da yau ina jin wani yanayi hakan nan, marana ya fara ciwo-ciwo ga ƙafana ya fara kama mini, haka dai a daddafe nayi ayyukan da zan yi ma gida na shirya zuwa tahfiz na yamma, da Umaima muka tafi, yau bayan antashi Malam Abbo ya faɗa mini anjuma zai zo wajena akwai maganan da yake so muyi, nidai nasan ban aikata wani laifin ba, amma na amsa masa sai ya zo, muna komawa gida na samu Alhaji da Mamina za su fita, nima ta ce na shirya muje wanke kai, na ce a'a ni sai gobe, a dawo lafiya na musu, kallo na kunna kawai na kwanta amma inajin ciwon maran nawa na ƙaruwa.
Abbaa tunda Ya Danish ya zo jiya ba su zauna ba, sai yau ya faɗa masa da dare yana son magana da su shi da Ya Farooq, duk amsawa suka yi, dare nayi bayan sun yi sallahn isha'i suka amsa kiran Abbaa, a palournsa da ke cikin compound ɗin gidan suka zauna, ga Umma ga Ummu gasunan su ma, Abba gyaran murya yayi tare da mayar da kallonsa kan Umma ya ce, "Sabeera da ke zan fara, saboda kece babba kuma mahaifiya, duk turban da kika nunawa na ƙasa da ke, musamman yaranki to shi za su bi, duk da bansan me yarinyar nan Banafsha da mahaifiyarta suka tsare miki ba, amma na sha faɗa miki ki gyara halayyanki akan su, inason ki faɗa mini me mastalarki da su, dan duk abinda kuka yi ranan da matar kabeeru ya dawo kunnena."
Umma Sabeera ɓata fiska tayi ta ce, "Ni ba abinda suka stare mini, halayyan mahaifiyarta ne kawai bana so, kuma ta dena shiga stabgan yarinyata kada ta lalata mini tarbiyaanta, gida kuma ka ce naka ne, dan haka ta shigo banda mastala."
Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, "Hakan yayi kyau tunda kinsan gida nawa ne, kuma sai wanda na bawa ikon shigowa zai shigo, dan haka kuma ina son ki sani ita Umaima ma yarinyata ce dan haka ni mastayina na mahaifinta na bata daman kula Banafsha da shiga gidansu, in kuma kin ce a'a sai ki nema mata wani uban bayan ni, lalacewa kuma idan Allah ya rubuto mata a ƙaddaranta to ko a ɗakin ki take akan gadonki to sai ta lalace, sannan akan abinda kuka yi ranan zan ɗau mataki ba shiru nayi da na ƙyale ba" Abbaa ya faɗa ransa a ɓace.
Umma dai fiskan nan a haɗe, Ummu kuwa kanta na ƙasa ma, Abbaa kallonsa ya kuma mayar wa kan yaransa ya ce, "Ku ma na dawo kanku, musamman kai Danish, kasan abinda ka aikata ba sai na faɗa ba, inason ka sani kai baka isa ka sani jin kunya ba, ni kuma ban haifi mara mutunci a cikina ba da yardan Allah, idan ka ƙara kuskuren aikata irin wannan abun ba iya ga Banafsha ba, wallahi ko a can wajan aikinka naji labari to ka tabbata zan cireka a cikin yarana, ka ji wallahi na ranste maka, bana son hauka da rashin hankali, ina ruwanku da rayuwar su? Haka Allah ya iyo su kuma haka Allah ya so ganinsu, kowa da ƙaddaransa da kuma jarabawansa, su wannan ne jarabawansu, ku zo a banza kuna uzzurawa kanku akan rayuwan mutanen da ba ruwansu da ku, kuma wataƙila a wajan Allah sun fi ku mastayi da komai, ni ba wanda ya bani mamaki sai kai Danish, da iliminka da tunaninka da tarbiyyanka da hankalinka, a bari ita mahaifiyarka da matar wanka su mata ne, kuma mata daman tunaninsu sai a hankali, amma kai za ka haɗa lissafinka da nasu kana na miji wanda ya isa ajiye iyali, to idan ka kuma gigin aikata irin wannan kuskuren ranka zai yi mugun ɓaci, yarinya da tarbiyyanta da komai ta fi wani wanda ya ke ɗan babban Malami nustuwa da komai amma kana neman aikata mata ba dai-dai ba, to wallahi kana ji na ka kiyaye, kuma daga kai har ɗan uwanka ina mai umurtanku da ku fito da matan aurenku akan lokaci dan ba zan ɗau wannan shirmen ba, tun kamun ku fara lalata yaran mutane gwanda na muku aure ku ɗin ma tunda duk kun kai riƙe iyali har kun kai zama iyaye ma, abinda ya sa nayi ƙiranku kenan, kuma duk wanda ya ɓata lokaci zai ga matakin da zan ɗauka, fatan kuna ji na Danish da Farooq?"
Dukkansu ɗaga kai suka yi alaman sun amsa, sannan Abbaa ya ƙara musu faɗa sosai ya ce ya sallamesu, su tashi su basa waje, miƙewa suka yi suka fice, Danish fiskansa a haɗe, Farooq dai murmushi yake yi.