Sashe 51
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nusaiba ma abu ya fara kai mata karo, tuni suka fara ƙoƙarin raba kan su da kayan jikinsu, cikin ƙarfin hali Abeed ya haƙura ya ƙyaleta, wanka yayi ya shirya, ita ma ta yi, suka wuni soyayyan su, dare na yi ya ce kuma bai san zancen ba, alwala ya sa ta tayi, suka gabatar da duk wani abu na al'ada, kayan cin su da Bunayd ya turo musu da shi, suka yi haniƙan, sannan fa aka fara zuba soyayya.
Abeed sarrafa Nusaiba ya ke yi kaman abinda aka turo sa yi a duniya kenan, tun da Abeed ya fara haukata mata boob's nata, yana gyara musu lissafi, tuni ta fice a nata lissafin, hidima sosai Abeed suke yi, ko ciwon ƙafan ba ya tunawa, sai da ya tabbatar ya gama da ita, sannan a niste ya fara neman hanyarsa bayan addu'an da yayi, wanda Sunna ya tanada domin ma'aurata, ita wannan addu'a kuwa tana stare masu gabatar da Sunna daga sheɗan, sannan idan a wannan lokacin ma an samu ƙaruwa, to Insha Allah wannan yaro zai zama nistastte ba sheɗani ba, mata w ƙoƙarta ko miji baya yi ke ki dage ki dinga yi, duk iya fitanki hayyacinki, idan ma ba'a iya ba ko bismillah ayi ta wadatar, addu'ar na da matuƙar amfani da muhimmanci, addu'an ita ce BISMILLAHI ALLAHUMMAH JANNIBNASH SHAITAN, WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAƘ'NA.
Nusaiba ta ji azaba dai-dai gwargwado amma dai ta daure, Abeed gaba-ɗaya ma ya mance duniyar da yake, hidima yayi ba ta kaɗan ba, sai da ya samu nistuwa sannan ya janye jikinsa tare da rungumeta yana lallashinta, bayan sun starkake jiki, ta gasa kan ta, sun gyara wajan kwanciya, sun kwanta, nan ƙafan Abeed ya fara damunsa, wasa gaske zuwa safiya kaman ya yanke ƙafan ya huta dan azaba.
Jikin Mami yayo sauƙi sosai, satinsu guda da kwana biyu a asibiti, aka sallamesu, zuwa lokacin kuma DR ARSHAN sun yi sabo da Umaima da Banafsha, Malam Abbo ya zo har asibtin ya duba Mami.
Gefen Umma kuwa tana prison a ajieye, tukunna ba'a bi ta kan case nata ba ma, gaba ɗaya a sati guda kawai ta lalace ta fice a hayyacinta, da yake ƙaramar ƴar tasha ce har ta yi nadaman abin da ta aikata, dan ta galabaita.
Ya Danish tun da Abbaa ya faɗa masa ba su yi magana da Mami ba tukunna, sai ya fasa zuwa weekend ɗin, yaya babba kuma gani yake kaman Danish da gangan ne bai zo ba, sai bai tuntuɓe sa ba, kuma ko ya ƙira ba ya ɗauka, shi kuma ya Mus'ab daman ba gwanin zuwa gida ba ne, yana can abin sa.
Abbaa ganin halin da Mami ke ciki, sai ya ɗaga ƙafa ba yanzu zai sameta da maganan ba, har Mami ta kuma yin sati da dawowa asibiti bai mata maganan ba, zuwa lokacin ta ji sauƙi sosai, su Banafsha sun ci gaba da zuwa makarantansu boko da tahfiz, in da yanzu suke shirin tafiya musabaƙan su, wanda za su gabatar a cikin jimeta tare da sauran makarantun local ɗin Adamawan.
MASU SHARHI UWAR BATOORL NA MUGUN ƘAMNARKU, INA MIƘO GODIYA MUTANEN AMANA.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# ð˜¾ð™¤ð™¢ð™¢ð™šð™£ð™©
# ð™‡ð™žð™ 𙚠&
# ð™¨ð™ð™–ð™§ð™š
👄'YAR KARUWA👄💅
Officially
ð˜½ð™®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.
PAGE NAKI NE
Heartbeat, ina mai addu'a Alfarman wannan wata ta Ramadan mai ɗimbin albarka, Allah baki lafiya ya sauƙeki ƙalau ukhtynh.
اللهم صلى Ùˆ سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤ðŸ¤
ðŸ…¿ï¸ 86 _ 90
Bayan wani lokaci Mami ta warke rass da ita, amma bata yi maganan Umma ba, lissafi kawai take yi da tunani akan rayuwa, musamman maganan Malam Abbo da Banafsha, dan Banafsha ta dage ba za ta yi aure ba sai dai Mami ta yarda ta yi ita ma, ko kuwa ta koma wajan danginta, wannan zaɓi biyu na Banafsha sun damu Mami, domin burin Mami bai wuce aurar da Banafsha ba, akan hakan kuma za ta iya yin komai, sai dai tuno abubuwa da dama na mata kastalanda akan amincewa da abin da yarinyarta take buƙata kamun a ce tayi aure.
Yau Abbaa ya shirya abinsa ya je wajan Mami, ba tare da ta nuna wani abu akan akasin da aka samu ba, haka ta tarbesa da fara'a, kuma ko Abbaa ya ji daɗin hakan, sai ya ji ta ƙara kwanta masa a rai sosai, ya ƙara son ta.
Cikin nistuwa Mami ta gaishe sa tare da tambayansa Ummu, amsawa yayi yana washe baki.
Abbaa cewa yayi, "Da farko dai ina mai baki haƙuri Hajiya Ramla, ina kuma baki haƙuri, dan Allah ki yi haƙuri da abin da ya faru, daman jiran warkewanki ake yi sai a fara shari'a ma, Insha Allah za'a ƙwatar miki ƴancin ki."
Murmushi Mami tayi wanda ke ƙara mata kwarjini, sannan makari ga duk wani damuwanta, cewa tayi, "Lah! Ai ba komai Abbaansu, na haƙura wallahi na yafe mata، saboda duk wata mace mai kishin mijinta za ta iya aikata fiye da haka, kuma ƙauna da soyayyar miji ke kawo kishi, duk da dai kishi ba hauka bane, amma da gaskiyanta ni banji haushinta ba ko kaɗan, da ina hayyacina ma ba zan bari abin ya kai ga hukuma ba, ko nine a mastayinta idan ba wai na danne zuciyata ba, to zan aikata abinda ya fi wanda ta aikata, dan sai na haɗa da mijin duka na ƙone su, kawai dai haƙuri ake tun da Allah ya halatta muku, sai dai mu ce Allah bamu ikon fin ƙarfin zuƙatanmu, Allah kuma ya bamu haƙuri da dangana, tun da ko matan Annabi SAW ma sun yi wannan kishin, har sai da ta kai Allah ya sauƙe aya guda a kan su a cikin Suratul Tahrim, dan haka dai ita kishi halitta ce, Sunna ce, ba yan da za'a yi ka guje mata sai ikon Allah, faɗin Manzon Allah SAW ne ma cewan kaicon ma'auratan da basa kishin junansu, tun da dai sai da kishi sannan ake samu a kiyaye wasu dokokin Allah a zaman auren, to kada ka ga laifinta, Allah ya kyauta kawai."
Abbaa shi dariya ma Mami ta basa, jin wai idan ita ce sai ta haɗa da mijin, jinjina kai yayi ya ce, "To yanzu dai idan na fahimta, Hajiya Ramla cikin ruwan sanyi take kafa mini sharaɗi, wato na kulle ƙofa daga kan ki, babu ta huɗu kuma ko na ce ta biyu dai."
Wani kallon rashin fahimta Mami ta masa ta ce, "Abbaansu ba dai nufinka ka sallami Maman Kabeer ba?'
Abbaa jinjina kai kawai yayi ya ce, "Eh! Saboda bana son tashin hankali da rashin haƙuri, Ita Ummu-khultum ai tana da zuciya da nata kishin, amma ta haƙura duk da haka, tun da ƙarin aure Sunna ce, ga kuma yanayin zamani ya zo ƙarshe."
Murmushin taƙaici Mami tayi tare da jinjina kai ta ce, "Ai daga wannan kuma ka riga ka faɗi zaɓe Abbaansu, ai yanzu na faɗa maka nima idan ba wai Allah ya taimaka ba zan yi fiye da haka, duk da ba sharaɗi bane amma ai hannunka mai sanda ce, gaskiya Abbaansu ka yi haƙuri kawai ka dawo da matarka, ku cigaba da zamanku lafiya, ni xan fi son hakan, domin yanzu gani zan yi kaman nima aje-aje gaba za ka iya mini haka akan wata, ka yi haƙuri amma zai fi ka dawo da matarka uwar yaranka, da stohon zuma ake magani, kuma da kake maganan Ummu ai kai ma cewa ka yi nata kishin daban, to da haka za ka fahimci kowacce mace da irin nata kishin, ba duka aka zama ɗaya ba, kar garin gudun gara ka faɗa wa zago kuma, a zo ni nafi Maman Kabeer kishi da rashin haƙuri, ka ga ai akwai mastala babba ma sosai."
Abbaa murmusawa yayi ya ce, "Ba zan iya dawo da Sabeera ba, saboda idan akan kishi ne kaɗai ta yi hakan, to da sauƙi dan nima nasan kowa da irin halittan kishin da Allah ya masa, amma har da dalilin dan Danish ya ce yana son Faɗima a nema masa izinin nemanta."
Da mamaki Mami ke kallon Abbaa, wato dai ranan gaskiya kunnenta suka jiyo mata, daman was-wasi take ko dan storita ne ya sa ta ji kaman Maman Kabeer ta ce, yaronta na son Banafsha, su mayu ne sun lashe mishi zuciya, murmushin yaƙe Mami ta yi ta ce, "Allah ya bawa Maman Kabeer haƙuri, Allah ya huci zuciyanta, in Allah ya yarda tun da bata so, to Banafsha ba za ta auri Danish ba, in ba dai Allah ya rubuta hakan a ƙaddaransu ba, to babu yanda muka iya kuma, sai dai addu'a da fatan alkairi, dan haka wannan ma ba dalili bane da zai sa ka rabu da iyalinka, ka yi haƙuri Abbaan yara, mu mata sai a hankali, haƙuri ake da mu, kaga Allah bai haɗa jininmu da ita ba shiyasa bata son ma ɗan ta ya auri Banafsha, to nan ma ina bayanta, saboda maganin bari kada a soma."
Abbaa wani gauron numfashi ya sauƙe cikin ƙara jin haushin Umma akan abin da ta aikata, kallon Mami yayi a yanayi na tausayi ya ce, "Hajiya Ramla a taimaka mana ni da Yarona, gaba-ɗaya tun da aka yi abin nan hankalina ya ƙi kwanciya, sannan yaron nan kwata-kwata ma ya ƙi zuwa ma, balle kuma ya san halin da ake ciki, ya ce sai ya ji labari an yarda ya nemi Fatima sannan zai zo, dan Allah a taimaka mana."