Sashe 54
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami ta ce, "faÉ—ima ki stayar da mutum É—aya cikin masu nemanki, idan Aliyu ne ki faÉ—a masa ya turo, idan kuma Danish ne, za mu yi magana da Abbaanku, daman ina tunanin ko shi zai ba da aurenki."
Murmushin taƙaici wan da ya fi kuka ciwo na yi, na ce, "Mami ban da uba ne? Ko da gaske ba ta hanyar Sunna kika same ni ba, Mami wallahi idan ba auran mutum kika yi ba, ni ban yarda ya zama waliyina ba, kuma Allah sai ana auren na gudu, nima na shiga duniya kawai kowa ya huta, nima na ɗaura daga inda kika tsaya..."
Ban ida rufe baki ba na ji sauƙan mari a bakina, wan da take bakina ya fashe, Mami cikin surutu take cewa, "Banafsha wato dan ina miki shiru, shi ne kika dage ko? To kuwa zan nuna miki ni ce mahaifiyarki ba ke kika haife ni ba."
Idanuwana a bushe ba ko alaman hawaye na ɗago su, cikin dakiya na ce, "Mami ko kasheni za ki yi, ba zan auri kowa ba sai kin yi aure, Mami ke fa ranan kika faɗa mini Allah na son mai haƙuri, to me yasa ke ba za ki kasance cikin waɗanda Allah ke so ba? Me yasa ba za ki kasance cikin masu ɗaukan ƙaddaransu ba? Mami me yayi zafi shi ba wuta ba, Mami duk fa tsanani na tare da sauƙi, Ya mahaifiyata ki yi haƙuri, amma a yanzu ki samu Abbaa da maganar nan, kema kin san ba ki yi adalci ba Mami, kin ƙi sa kuma ki ce yayi wa yarinyar ki walittaka, ki duba lamarin da kyau."
Mami masifa ta fara mini, in da take shiga ba nan take fita ba, ni kuma yau na dage ba zan yi aure ba sai ta yi, saboda ɓacin ran da Mami ke ciki tuni ta fara jibgana yan da muka saba idan na mata irin magannan, duk dukan da Mami ke mini bakina bai mutu ba, kuma babu ko ɗigon hawaye, abu ɗaya kawai nake faɗi, "wallahi Mami ko kasheni za ki yi, ki kashe ni, na yafe miki kuma, amma ba zan yi aure ba sai kin yi..."
Ban fasa surutu ba, Mami bata fasa dukana ba, muna cikin haka sai ganin Alhaji Mukhtar muka yi, ba zato ba tsammani, Alhaji da sauri ya janye Mami ya riƙe hannayenta yana faɗin, "Ramla ba ki da hankali ne? Me ke damunki? Kashe ta za ki yi?"
Mami kawai fashewa tayi da kuka ta ce, "gwanda na kashe ta na huta, tun da baƙin ciki da damuwa ita ma take son cusa mini, in kai ta mahaifinta an faɗa mata tana da uba ne? Bayan sanadinta na rabu da kowa nawa, farin ciki na, mai so na, iyayena, dangina,mastayi na, da komai nawa, duk dan saboda ita na haƙura da su, na zaɓe ta akan kowa nawa, har sau nawa take so na dinga sadaukar mata da farin ciki na? Haka iya wan da na mata bai isheta ba?"
Jin furcin Mami tuni hawaye yayi shaɓe-shaɓe a fiskana, kuka na kama bilhaƙƙi kaman rai na zai fita, me Mami take nufi da bata san uba na ba? Mutum na fita a jikin bishiya ne? Ko mace na haihuwa ita kaɗai ba tare da namiji ba? Ɗagowa nayi ina kuka na ce, "Mami bayan jin wannan furucin naki, sai na kuma samun ƙwarin guiwan ƙin aure, Mami ba zan yi aure ba sai kin yi, kuma sai kin koma ga danginki.."
Kamun na rufe baki Mami ta iyo kai na, ta hau jibgana, da ƙyar kuma Alhaji ya riƙe ta bayan ya ce na tafi, haka na tashi ina haɗa hanya na nufi ɗakina, amma ina shigewa kamun na isa ga gadona, tuni wani mugun jiri ya ɗibeni, inajin jiri-jiri, baya na yi luuu na faɗi, lokaci guda numfashina ya ɗauke.
Æangaren Mami kuka ta dinga yi sai da Alhaji ya dage da lallashi, cikin soyayya yake lallashinta ya ce, "haba Ramla, da girmanki da tunaninki da komai naki, kike irin wannan furucin? Me yasa ne wai ke baki yarda da Æ™addara ba? Me yasa ba za ki mata abin da take so ba?"
Mami kuka ta dinga yi mai matuƙar ciwo da cin zuciya, ba abinda take nanata wa sai istigfari, bayan Alhaji ya gama lallashinta da mata nasiha, sai ya ga kawai ta miƙe stuttt! Kaman wacce aka stikare ta, share hawayenta ta ci-gaba da yi, tana faɗin, "faɗima zan yi abin da kike so in zai sa ki farin ciki ki kuma yar da ki yi aure.." tana magana ta wuce ɗakin Banafsha, sai dai tana shiga daga bakin ƙofa ta tarar da ita a yashe a ƙasa bata ko numfashi.
Mami ganin haka, ihu ta stala tare da faÉ—in, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un! FaÉ—imana kada ki mini haka."
Alhaji jin ihunta ya shigo da sauri, ganin halin da Banafsha ke ciki, da sauri ya ɗauke ta yayi waje da ita, Mami haka ta bi sa ba mayafi, sai shi ne ya koma ya ɗauko mata, sannan ya ja mota suka yi asibiti, Mami sai ƙoƙari take wajan danne ƙwallan da ke fito mata, kada ta yi hawaye wa yarinyarta.
General hospital Alhaji ya kai su, suna isa kuwa cikin sa'a suka samu Dr Arshan na duty, yana ganin Mami ya ganeta, nan yasa aka yi da Banafsha emergency, sai da ya dubata sannan ya sanar da su Mami kada su ɗaga hankali, suma ne tayi saboda wani abu da ta gani ko ta ji ya sa bugun zuciyanta ƙaruwa, ya firgita ta, amma zuwa ba jimawa za ta iya farfaɗo wa, ko zuwa gobe.
Alhaji da Mami ne suke zaune a kan Banafsha, Alhaji sai tausan Mami yake yana bata baki, har dare sannan ta farfaɗo tana sumbatu, Mami cikin hanzari ta rungumeta tana faɗin ta nistu ga ta nan kusa da ita, Alhaji kuma ya ƙira likita, sai da ya mata allura sannan a hankali kuma ta koma bacci yayi gaba da ita, tana sakin ajiyan zuciya.
Washegari da ta farka jikin ya zama normal, sai da ta ci abinci ta yi sallolinta, sannan Mami ta fara magana cikin lallashi, cewa tayi, "Faɗima ki kwantar da hankalinki kin ji, Inshà Allahu Maminki za ta yi duk abin da kike so da kuma abin da zai saki farinciki, zan yi aure kaman yan da kike so, sannan zan ba ki labarin dangina, zuwa gaba kuma Insha Allah zan haɗa ki da su."
Ina daga kwance amma a take na tashi na zauna, kallon Mamina nake cikin farin ciki da ƙaunarta, me nake nema a duniya ina da Mamina? Tuni ma na ji ciwon da ke damuna duk sun fece, karo na farko a rayuwa da naji tabbas mastalana sun ƙare, ko ba komai indai Mamina za ta yi aure to shikkenan, alhamdulillahi abin da nake so kenan, ko maganan danginta bai dameni irin maganan ta yi aure ba, ai rungume Mami nayi cikin farin ciki, ina sauƙe ajiyan zuciya, yayinda Mami kuma ke ƙoƙarin mayar da ƙwallan da ke son zubo mata.
Dr Arshan ya zo ya duba ni, da mamaki ya tambayi me ya faru haka, har komai da ke damuna ya setu, daga yanayin bugun zuciya na har jinina da ke neman hawa ya wuce misali, murmushi kawai na masa da yake mun É—an saba kwanaki da Mami ta kwanta.
Sai yamma sannan aka sallamemu, Alhaji ya jido mu muka dawo gida, bayan ya siya duk wani magani nawa da ake buƙata, kuma ya bi mun saya fruits da sauran su.
Muna dawowa gida da yake juma'a ne yamma ma ta riga da ta yi, sai ga Umaima ta shigo, É—akina muka wuce da ita bayan ta gaishe da su Mami, muna shiga ta tambayi me ya faru bata ganni ba tun jiya, kawai faÉ—a mata nayi ban da lafiya ne, mun je asibiti kuma Dr Arshan ma ya ce a gaisheta.
Amsawa tayi ta mini Allah ƙara sauƙi, sai da muka taɓa hira sannan na shiga na wasta ruwa, na zo na kwanta, ita kuma Umaima ta yi wa su Mami sallama ta fice.
Mami ta biyo ni har ɗaki ta bani magani da abinci, sannan ta mini sai da safe bayan ta ƙara kwantar mini da hankali, kwanciya nayi ba jimawa bacci yayi gaba da ni.
A ɓangarena da yake yanzu na samu nistuwa, ba jimawa bacci yayi gaba da ni hankali kwance.
Mami kuwa gaba-ɗaya kan ta chaji ya ɗauka, dan haka ba su wani yi dogon hira da Alhaji ba, ta tashi ta shige ɗakinta, wanka ta yi ta shirya staff sannan ta fito, sai da safe ta yiwa Alhaji, kallonta yayi yana murmushi ya ce, "Ramla sai da safe kuma, ba za ki ce nazo mu kwanta ba? Ko kin manta ke kika ce na dawo kina buƙatata?"
Mami murmushin yaƙe tayi ta ce, "Ai nasan ko na ce ba zuwa za ka yi ba, dan haka Allah tashe mu lafiya", ta faɗa tare da shigewa ɗakinta.
Alhaji murmushin shi ma yayi kawai tare da girgiza kai, ya ce, "Allah shirya mini ke cikin gaggawa ya nusar da ke gaskiya, ina matuƙar ƙaunarki da kuma buƙatanki Ramla, amma zan ci gaba da kiyaye wa har zuwa lokacin da zan mallake ki, sannan ke ma ina addu'an Allah baki ikon jure naki buƙatan, Allah stayar da duk wani mummunan ƙaddaran rayuwanki haka nan."