← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 58

Sashe 16

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangarena ma baccin ne yayi gaba da ni, sai wajan azahar na tashi, fitowa nayi naji gidan shiru alaman duk basu tashi baccin ba, sai na shige kitchen na kunna gass na hau haɗa mana abincin rana, fried rice da yaji ice fish da haɗin coslow na mana, sai da na gama sannan na koma ɗakina lokacin ana ƙoƙarin shiga sallah, wanka nayi na ɗaura alwala na gabatar da sallah na sannan na fito dan tashin Mamina, amma sai na same ta zaune a palourn ta sha kyau, ina isa wajanta da murmushi sai kuma ga Alhaji ya shigo, alama daga masallaci yake, ƙasa nayi da kai na, Mamina ta ce, "je ki kawo mana abincin mu ci, mu yi la'asar za mu fita duka da Alhaji."

Miƙewa nayi na haɗo mana abincin, na Alhaji na ajiye masa, na ajiyewa Mamina nata, sannan na juya, nawa na ɗebo na shige ɗaki, ina ci ina game a wayan Mamina da na ɗauko, binciken da na saba yi ko zan ci karo da layin wani ɗan uwan Mamina a wayanta na yi, amma ba ko alaman abinda ya shafi layin wani nata, ganin haka sai na dinga game kawai ina cin abinci, har aka ƙira la'asar, sannan nayi sallah na kuma wanka na sanya riga da skirt na swiss-less, ba ƙaramin kyau kayan ya mini ba, kuma ya zauna a jikina ɗamas, mayafina na yafa na fito, lokacin Alhaji da Mamina ma sun shirya, Mami kallo ɗaya ta mini ta ce na koma na sako hijabi, cunna baki nayi ina shagwaɓe fiska na ce tayi haƙuri, amma ta dage sai na sako hijabi, Alhaji ne ya bata haƙuri tunda a mota ne ta kyale ni da mayafin tunda ba ƙarami bane, Mamina da ƙyar ta ƙyale ni tana wasta mini mugun kallo, wanda nasan nufinsa bai wuce ta ce nasan halittan da Allah ya mini ko ina a cike amma bana son hijabi, ni abun har ɗaure mini kai yake yi, Mamina kaman wacce ta fito a jikin bishiya ba iyayene suka haifeta ba, ko kaɗan bata damu da kanta ba, burinta a rayuwanta komai nine, bata damu da mutuncinta ba tana kule-kulen maza, amma ni ko saurayi har yau bani da kuma ta hanani waya ma, ajiyan zuciya kawai na sauƙe tunda ta bar ni naje hakan ba komai, Allah dai shi ne mai starewa.

Tare muka fito duka, Alhaji ya shiga mazaunin driver, Mami ta zauna a gefensa kujeran mai zaman banza, ni kuma na buɗe gate, sai da motan ta fita sannan na kulle gidan gaba-ɗaya na nufi motan, a ƙofan gidan su Umaima na hango ya Danish da yake shigewa gidan bai ma kalleni ba shi, murmushi na sake na abinda na rashin mutuncin da na shirya masa, gidan baya na shige Alhaji ya ja mota muka shige gari, Japsal Shopping-mall muka fara zuwa, waje ne na sayayya kuma kayaki ne masu kyau da kuɗi a can, sayayya Alhaji ya mana ba kaɗan ba, kama daga dangin kayan sawa, kayan kwalliya, kayan abinci, kayan abun sha da su snacks, muna gamawa da sayayya kuma ya wuce da mu ADU, nan ma sai da ya mana ordern abinda za mu ci, kowa aka kawo masa abinda yake so, muka cika ciki, muka yi takeaway, ƙara zaga gari yayi da mu, yawo muka yi sosai kaman ba gobe, idan ka ganmu za ka ɗauka Mami da Alhaji, mata da miji ne da kuma ni ƴar su.

Sai da yamma tayi liss muka dawo da kaya niƙi-niƙi, Alhaji ya kashe kuɗi ba kaɗan ba, kuma ya ce kada Mami ta yi girkin dare, wannan takeaway ya ishe mu, idan da wani abin ma zai fita ya nemo, ni kuwa daman na jidowa Umaimata nata tunda nasan mayyar ice cream ce ita da naman kaza, muna iso wa, na sauƙa na buɗe ƙofa Alhaji ya shige da motansa, kayan da na jidowa Umaima na ɗauka na ce, "Mamina bari na bawa Umaima nata", kamun Mami tayi magana tuni na fice a gidan da sauri saboda kada ta dakatar da ni, ai kuwa hakan aka yi, ƙwala mini ƙira ta dinga yi amma na gudu, Alhaji murmushi yayi tare da riƙo hannun Mami ya ce, "Amarya ta mu shiga ciki ko."

Wani kallo Mami ta masa tare da ƙwace hannunta ta shige fuuuu! Ga haushin Alhaji ga haushin Banafsha ta fita ba hijabi.

Ni kuwa ina shiga gidan su Umaima na dinga leƙe-leƙen Ya Danish, amma ban gansa ba, kuma dai motansa na gida, nasan ba zai wuce yana part nasu ba, shigewa cikin gidan nayi ba kowa a palourn, sallama nayi na nufi ɗakin su Umaima, samunta nayi tana guga, murmushi na sakar mata, ta ce, "Masoyiya irin wannan kyau haka, komai Masha Allah! Daga ina?"

Ledan hannuna na miƙa mata na ce, "Ga tsaraba tawan."

Umaima kaman za ta fire ta ce, "Wayyo! Allah bar mini ke Banafsha, Mamina Allah ƙara buɗi, wayyo naman kaza da ice cream, kutt har da shawarma, oyoyo chocolate" faɗin Umaima tana dariya.

Zama nayi a gefen gadonta na ce, "Mun godewa Allah da ba'a ƙauye kike ba, ko gidan talakawa da abin ya fi haka, Abbaa yana da kuɗinsa, yayyunki ma haka, kuma Umma na business, Ummu ma ba'a bar ta a baya ba, kuma babu wanda ba ya saya miki, amma idan kika ga kaza da ice cream kaman me, gaskiya idan Allah ya kai mu Abuja za ki ba da mu, muna zuwa saudi kuwa nasan sai na dinga riƙe ki, saboda kada a samu masu jan ki da dajaja(kaza da larabci), kinsan larabawan Makkah wasu yan albarka ne, wasunsu iskanci suke da mutane."

Hararana Umaima tayi ta ce, "To zabiya, kanki ake ji, ki bari idan munje makkan sai mu tabbatar, ba kyau shedan zurrr."

Nima rama hararan nayi ma miƙe na ce, "sai anjuma bari na shirya ki same ni a ƙofa mu wuce tahfiz."

Amsawa Umaima tayi, na fice na shige ɗakin Ummu na gaisheta, sannan na fito ina ta kan leƙe-leƙe ban hango sa ba, yaya babba ne ya shigo gidan, da murmushi na ɗan rusuna na ce, "Sai babban yaya! Allah taimaki babban yaya."

Dariya yaya babba yayi, ya ce, "sistor ba'a raba ki da abin dariya, kun gama exam's lafiya?"

"Alhamdulillahi babban yaya, ya Auntynmu."

"Tana lafiya, tunda kun ƙi zuwa gidan mu, ga baki ga hanci amma bakwa son shiga, daga ke har Umaima, bealkysou ce kawai ke shiga."

Murmushi nayi na É—an sosa kai, dariya yayi ya ce, "Allah shiryaki sistor, wannan kyau haka daga ina zuwa ina?"

Na buɗe baki zan basa amsa cikin kunya, sai muka jiyo muryan Umma tana masifa wai ta ƙirasa ya tsaya magana da fistararriyar yarinyar nan ƴar karuwa, yaya babba haƙuri ya bani da ido kawai ya wuce, ni kuwa fakan idon sa nayi ganin ya juya na aikawa Umma da murguɗa baki, juyawa nayi ina tafiya na, kaman daga sama kawai naji an zuba mini ranƙwashi aka ce, "Dan uwarki, fistararriya uwar tawa kike wa gastine da baki?"

Ina ɗagowa, idanuwana suka sauƙa akan Ya Danish, cikin zafin ranƙwashin na ɗaga hannu zan maresa, amma sai ya riƙe hannun nawa ƙam na kasa mosta sa balle ƙwace sa, wani kallo ya wasta mini ya ce, "mara tarbiyya kawai, dube ki haka kike yawo, uban wa za ki ja hankalinsa da wannan ƙazamin jikin naki, mai rijiyan kasuwa kowa zura gugansa yake, mara aji kawai."

Taƙaici ne ya rufe ni na maganganun sa, na ma rasa da me zan rama ga shi har yanzu ya ƙi sake mini hannuna, idanuwana ne ke ƙoƙarin kawo ƙwalla, amma ƙoƙari nake wajan maida su, cikin dakewar zuciya na ce, "sake mini hannuna ni ba sa'ar yinka ba ce, wanda bai san darajar uwar wani ba balle a kai ga tasa" ina faɗa na ƙwace da ƙarfi, sai da na staya na ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan naja staki na ce, "Ni ko iskancin nake yi ai kasan na wuce wa irinka, na wuce yinka, na fi ƙarfinka, ba ka da abinda za ka isar da ni, ka yi kaɗan abinka yayi kaɗan, ka je a sake maka kaciya tukunna, riƙe hannuna ba zai sa naji komai a kanka ba, saboda kallon jariri nake maka, abinka kuɓewa ma ta fi sa a waje na, mtsww!" Ina gama faɗan haka na juya da sauri-sauri na bar sa a wajan tsaye da buhun mamaki, ni ko ina ficewa na juya na harari gidan, sannan na murmusa dan nasan ko banza na faɗa masa magana, ina dariya kaman ba ƙalau ba na shige gidanmu.

Ya Danish mutuwan tsaye yayi, jin abinda yarinya ƙarama ke faɗa masa, haushinta da stananta suka ƙara cika sa, ƙwafa yayi ya ce, "ko na fi karfin zura gugana a rijiyar mutane da yawa, to tabbas sai na gwada miki karatuna ya fi ƙarfin na 'yan iskan abokan iskancinki" yana gama faɗa shi kaɗansa ya shige sashinsu ya fasa shiga cikin gidan ma, saboda taƙaicin Banafsha.

Ni kuwa ina shiga tun ba'a faÉ—a mini ba na buÉ—e motan Alhaji na dinga jidan kayan ina kai wa ciki, sai da na gama sannan na kalli Mamina a sace na wuce É—akina, shiryawa nayi na fito na ce, "Mami sai na dawo."

"A dawo lafiya" Mamina ta faɗa a taƙaice, na fice a gidan, a ƙofa muka haɗu da Umaima muka wuce tahfiz, sai da aka tashe mu sannan muka kamo hanya muna hira, na faɗa wa Umaima yau Malam Abbo bai zo ba Allah ya sa lafiya, amsawa tayi da Ameen tana kallona tana murmushi, saboda Umaima ta gama fahimtan akwai abu a zuciyan Malam Abbo game da Banafsha.
Chapter 16 · 0% Book details