Sashe 28
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Malam Abbo cikin fara'an yanda na sake ya ce, "Masha Allah! Ai dole na taɓa Sayyadata" ya faɗa tare da kurɓan ruwa, sannan ya dube ni, cikin jarumta ya fara mini magana kaman haka, "Sayyada Faɗimah fatan dai ban takura ki ba da zuwan da nayi na dare?"
Jinjina kai nayi kawai alaman ba komai, murmushi Malam Abbo yayi ya ce, "To! Godiya nake Sayyadata, Allah ƙara lafiya."
Murmushi nayi kawai, sai da muka gaisa ya tambayi karatu da boko duk na amsa masa, sannan ya ɗago yana bi na da wani irin kallo mai narkar da zuciyan abinda kakeso, ƙasa nayi da kai na, Malam Abbo ya numfasa ya ce, "Sayyadata ina mai fatan babu wanda ya rigani ko ya mini shigan sauri ya mini ƙafa?"
Ba tare da na fahimci abinda yake nufi ba kawai na ɗaga kai, murmushi ya kuma yi ya ce, "Masha Allah! Alhamdulillahi ala kulli halin! Ni ɗin mai sa'a ne Insha Allah, Sayyadata abin da nake faɗa da gaske nake faɗansa tun daga ƙasan zuciyata, soyayyanki da ƙaunanki sun jima da yi mini mugun kamu, kuma ƙauna ce wacce aure za ta zama ribarta Insha Allah, ina fatan za'a amsheni hannu bibbiyu tunda an ce babu wanda ya rigani."
Wani irin kunya ne ya rufe ni lokaci guda, kawai rufe fiskana nayi da hijabi ina ta murmushi, ba wannan bane karo na farko da namiji ke faɗa mini yana ƙaunata, amma wannan sai na ji sa daban, Malam Abbo ya kai maƙura duk inda ake buƙatar mijin aure ya kai, alhamdulillahi indai wannan ya zamo uba ga yarana to ina da tabbacin sun yi dacen uba, amma sai dai kashh! Ba wannan bane a gabana, ban da asali ban da kowa sai Mamina kawai, aure ba zai yiwu ba a gare ni, ba zan iya yaudaran bawan Allah ba na sa masa rai ba, ni na riga da na sani a ƙaddaran rayuwata babu aure, kowa na zagina da hantara ta akan ƙaddaran mahaifiyata, a yanzu zan iya jurewa amma ba zan iya jure hakan a gidan aure na ba, ko ga dangin miji ko kuma aje-aje har shi mijin da kansa, dole na haƙura da batun soyayya balle a kai ga aure, cikin sanyin jiki na ɗago shanyayyun idanuwana da ke neman zubar da ƙwalla na kalli Malam Abbo cikin ido, da duk sauran juriyata da jarumtata na ce, "ka yi haƙuri Malam, amma ni ba zan yi aure yanzu ba kada na bata maka lokaci."
Daga yanayin Banafsha Malam Abbo ya fahimci ya samu karɓuwa, ko abinda take furtawa ma kokawa take da zuciyanta wajan faɗan hakan, cikin damuwa ya ce, "Sayyadata ko nan da shekara nawa ne na miki alƙawarin zan jira ki, nasan ba zai wuce kina son kammala karatunki ba, wallahi banda mastala da bokonki ni da kai na idan ina da hali sai iya inda rai ya stayar da ni akan iliminki, ina ƙaunanki Sayyadata, na jima ina dakon soyayyanki amma na kasa furta miki, wannan karo da na samu ƙwarin guiwan faɗa miki dan Allah kada ki juya mini ƙoƙon barana ba tare da kin cika mini shi ba."
Zuwa yanzu hawayena ƙiris suke jira su kwalalo, a hankali na ce, "ka yi haƙuri Malam Abbo ba zan iya aurenka ba."
Cikin damuwa yake kallona yanda nake kallonsa ya ce, "Saboda menene Malama Faɗima? Halinane bai miki ba? Ko nasaba na? Ko kuma menene ba dai-dai ba ki faɗa mini, na miki alƙawarin gyarawa yanda kike so in Allah ya yarda."
Wannan karon muryana na rawa har hawaye sun fara bin kuncina na ce, "Malam nasan kasan gaskiya akan komai a rayuwata, nasan kasan duk abinda jama'a ke faÉ—a a kai na da mahaifiyata, Malam ba ta inda ka kasa, don babu macen da za ka nuna kana sonta ta ce baka mata ba, Malam ni kwata-kwata auren ne ba zan yi ba a rayuwata."
Malam Abbo kallon Banafsha yake ba kifta ido ya ce, "Zan aureki a haka Faɗima, zan aureki a duk yanda kike, ni ke nake so ba komai da ya shafe ki ba, ko wanni bawa da irin ƙaddaransa da kuma jarabawansa, ina ƙaunanki a duk halin da kike ciki Sayyadata."
Fashewa kawai nayi da kuka na ce, "Malam ko kana so na danginka ba za su aminta da ni ba na sani, dan Allah ka yi haƙuri Malam, Allah ya baka mace tagari wacce ta dace da kai", ina gama faɗan haka na miƙe ina kukana na nufi tafiya ɗakina.
Malam Abbo ma miƙewa yayi ya fara magana wanda shi ya stayar da ni, "Malama Faɗima kaman yanda na faɗa miki ina sonki a duk yanda kike, to ina son ki sani ke ce dai-dai ni, kuma ni zan zauna da ke ba kowa nawa ba, ina sonki ina ƙaunanki ki saka wannan a ranki, in Allah ya yarda in har da rabo kuma da alkairi to Allah da kansa zai yi Allahnsa ki zama mallakina, amma ina roƙon ba za ki ɗau fushi da ni ba akan wannan magana."
Ina gama sauraran Malam Abbo na wuce ɗakina da sauri ina kukana, ga samu ga kuma ráshi lokaci guda, Malam Abbo mijine da ko wacce mace tagari za ta yi addu'an samu, amma ni ga daman hakan ya sameni har gida sai dai babu hali, ƙaddaran mahaifiyata ya riga ya rusa mini komai nawa, ƙaddaran mahaifiyata ya sa na tashi banda kowa sai ita dan ina da tabbacin ƙaddaran rayuwanta ne ya rabata da kowa nata, ƙaddaran amsa sunan ƴar Karuwa da zamtowa ƴar Karuwa shi ne babban ƙalubale na a rayuwa, ɗaga hannayena sama nayi na ce, "Allah ga ni gare ka, Allah ka iya mini a lamurana, a yanda nake ina matuƙar son na ga nima na raya sunnan ma'aiki, amma mahaifiyata ta zama katanga a gareni tsakanina da aure, wa zai auri ƴar mace mara asali kuma ƴar karuwa? Banda Uba banda ƴan uwa banda kowa sai mahaifiya, ai ko a jikin bishiya na fito albarka, nasan babu ubanda zai amince ɗan sa ya auri ƴar mace mai zaman kanta, macen da maza daban-daban ke sintiri a wajanta" rushewa nayi da kuka mai ƙarfi saboda ciwon marana da ya ƙaru ya dawo mini sabo fill dan damuwan da nake ciki.
Malam Abbo kuwa Banafsha na shigewa kaman zai yi kuka ya koma ya zauna, sai da ya ƙara kurɓan ruwa ya dinga jera ajiyan zuciya sannan ya miƙe, ya juya zai fice sai ga Alhaji ya fito a ɗakinsa, Malam Abbo daurewa yayi ya shanye damuwarsa da murmushin yaƙe suka ƙara musabaha da Alhaji ya masa sai da safe, sai da ya rakasa har ƙofa sannan suka yi sallama ya tafi, Alhaji kuma ya rufe ƙofa ya dawo cikin gidan cike da tausayin wannan matashin, dan kusan maganansu na ƙarshe da Banafsha ya ɗan stinci saura, wannan jarabawa ce ga uwa da kuma ƴar ta, kuma Alhaji sam-sam bai ga laifin Banafsha ba saboda gaskiyanta ne, wasu iyayen sai a hankali ba lallai su amince ɗan su ya auri mara asali ba kuma ƴar mace, amma kuma yana tausayin saurayin dan ji yayi kaman yaronsa ne ya je neman aure aka masa haka, addu'an alkairi kawai yayi ya tura ƙofan Mami ya shiga, ganin tana bacci sai ya fice ya koma nasa ɗakin ya kwanta.
Malam Abbo yana fitowa ya samu har lokacin su Ya Danish na zaune a ƙofan gida, duk da duhun dare amma Ya Danish yana ƙoƙarin hango wani abu daga yanayin Malam Abbo, kaman zai ji daɗi kuma sai ya taɓe baki irin me damuwansa da kashin su, shi kuwa Malam Abbo haka ya koma gida cikin damuwa da niyan zai bawa Banafsha lokaci ko da sati guda ne ya ji ko ta sauya shawara, idan kuma abun ya ƙi to gaskiya zai samu Ummanta da maganan, shi ba zai iya jure rashin Banafsha ba, Allah ya gani soyayyanta ya jima da masa mugun kamu.
Ya Danish har suka gama hiransu suka shige gida zuciyansa cike da son ganin giftawan mara kunyar, ya samu ya mata wani rashin kirkin ko zai ji daɗi, haka washegari da sassafe ya fito tun su Umaima ba su tafi makaranta ba ya zauna a ƙofan gida yana son kallon giftawanta dan ya yaɓa mata magana.
A ɓangaren Banafsha kuma da wani irin mugun zazzaɓi ta kwana da ciwon mara, kamun gari ya waye tuni ta fice a hayyacinta, daman ita idan ciwon maranta ya tashi ba ya mata ta sauƙi, duk wata na Allah sai ta ji a jikinta, balle kuma ga shi jiya abin ya haɗu mata biyu, ga damuwa ga ciwo, kwata-kwata ko sallahn asuba ta kasa tashi ta yi, ta galabaita sosai-sosai kuma har lokacin ba wai jinin ya zo ba ne.