← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 58

Sashe 34

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai na yi a zahiri, a zuciyata kuwa mamakin Mamina nake, mamakin gaske ma kuwa, wato Mami ba za ta ma faɗa mini ba, ana cewa yaran fari abokanan shawara ne kuma ƙawaye amma banda Mamina, musamman a irin wannan magana, uhmn to Alhamdulillahi!, Duk da nasan maganan da ta yi ɗazu da ɗan gaskiyanta na Umma bata ƙyaleta ba kuma ba ta ƙyale ni ba, amma wannan ba hujja ba ne, ko ni da ya Danish yayi ƙoƙarin ƙeta mini mutunci na so mata auren Abbaa balle ita da bata san da wannan ba ma, kuma Mami in za ta duba da kyau ni a ganina auren Abbaa ya fi mata auran Alhaji, tana son Alhaji kam amma wani lokacin abinda muke so ba shi ne alkairi a gare mu ba, sannan tana maganan aurar da ni, a muna zaune haka ba namiji shi ne take tunanin wasu za su zo neman aurena wajanta tana mace? Ai babu mai aurar mara uba, ana dai auran wacce/wanda ba su da uwa amma banda marassa uba, saboda da uba ake ado ba rigar aro ba, ni sai yanzu ma Malam Abbo ya faɗo mini a rai, Mamina bata nadama a irin wannan rayuwan ina na isa na yi maganan aure, shiyasa ma ni ban saka wa rai na zan yi aure ba, tunda haka Mamina ta zaɓa sai mu zauna duka haka, niyan nayi shiru nayi mu je a haka a bansan abinda ke tafiya ba, amma zuciyata ta ƙi ƙyaleni nayi shiru, numfasa nayi a hankali kaman munafuka na ce, "Mamina me yasa kike yi yin haka?" Na faɗa kaman zan yi kuka.

Mami kallona tayi ta ce, "Me nayi Banafshan Mami?"

Gyara kwanciya nayi a cinyan Mamina na ce, "Dan Allah ki yi haƙuri Mami idan abinda zan faɗa zai ɓata miki rai, gaskiya ce komin ɗacinta faɗansa yana da kyau, Mami me ya sa za ki ce ba aure a gabanki? Mami me yasa kike nunawa mahaliccinki ba za ki cika sunnan ma'aikinsa Annabi SAW ba, Mami duk mace ko namiji da suka kai aure suka mutu ba aure fa Allah ma tausayinsu yake, Mamina nasan kin sani aure ni'ima ne kuma rahama ne, Mami Allah ya azurtaki da farinjini wanda wasu ma sai sun nema da kuɗi sun saɓa ma Allah sannan suke samu, Mami har yanzu taurarinki suna haskawa ba su disashe ba, me yasa ba za ki yi aure ba tun yana binki, kamun ya zo yana guje miki kina bin sa, Mami a haka akwai mai aure na ban da uba ina ƴar mace? Mami...." Maganan baki nane ya maƙale sakamakon wani irin stawan da Mamina ta daka mini, wanda ya sa na miƙe zaune babu shiri a rikice.

"Banafshaaaa!!!!" Haka Mamina ta ƙira sunana a stawa ce.

Tura baki nayi tare da runste ido na inma duka na Mami za tayi sai dai ta kashe ni, amma sai na faɗa mata gaskiya, ci-gaba nayi da magana ba ruwana da hucin da Mamina take yi, cewa nayi, "Mami ranan Alhaji ya ce miki Amaryansa kika ɓata rai, ya ce za ki haifa mini ƙanne kika yi fushi, Mami yau ina ji Abbaanmu ya ce zai aure ki nan ma kika ce ke ba aure bane a gabanki, Mami menene damuwanki dan Allah? Mami ya kike so a miki, duk da Alhaji mutum ne da yake rayuwan da bai dace da ke ba amma ya nuna yana ƙaunanki a haka, kuma zai aure ki, akwai soyayyan da ta fi wannan? Abbaa ya san ki shekara da shekaru, ya san duk abinda kike da wanda kike aikatawa na ba dai-dai ba amma hakan bai dame sa ba, bai hana sa ƙaunanki ba, yana sonki ya danne zuciyarsa, yanzu ya kasa haƙuri kuma ya furta miki kin ce ba haka ba ya kike so Mami? Wani irin masoyi kike son samu sai ki kawo maganan aure a starinki? Mami kina tuna mutuwa kuwa? Kina tuna za mu mutu ba tare da mun san yanzu ne ko anjuma ko kuma yaushe ba? Mami ita fa mutuwa ba ta alert a ko wane yanayi za ta ɗauke ka idan lokacinka yayi, Mamina kowa burinsa da fatansa ƙarshensa ya fi farkonsa kyau ya kuma gama da duniya lafiya yana mai imani mumini amintacce, Mami ke me yasa bakya fatan hakan? Mami dan Allah ki yi aure, wallahi idan ba za ki yi aure ba to kibar cewa aurar da ni ne damuwanki kuma burinki, sabida babu mai aure na a wajan mace, kuma ko akwai ma to ba auran zan yi ba, ba zan jure a goranta mini ina gidan mahaifiyata a ƙira ni da ƴar karuwa, sannan a ce nayi aure a goranta mini a ƙira ni da ƴar mace ba, Mami kina da dangi, kuma nasan ina da uba tunda mutum ba ya haifan yaro shi ɗaya, amma duk kin rabamu da su kin guje su kin wastar da su saboda me Mami? Ni Ko da mahaifina na raye ko ba ya raye ai ya kamata ki haɗa ni da danginsa saboda su ne gata na, kuma su za su shiga tsakanina da masu yi mini gori, Mami wallahi ko shegiya kika haife ni to haɗa ni da mahaifina ya fi wannan hukuncin naki kamata, kuma ni na yafe muku ina ƙaunarki a haka ke da mahaifi na, in ma ba ta hanyan da ya dace kuka same ni ba, na ɗauki ƙaddarata ta zamowa ƴar shege.........."

Tasss!!Tasss!Tasss!!!!, Shi kawai kake ji Mami ta kwashe Banafsha da wasu mahaukatan maruka, idanuwan Mami jajazir kaman garwashin wuta ta ce, "Banafsha ni kike wastawa wannan kalaman? Banafsha har ni za ki saka a gaba kina mini magana kaman ƴar cikinki? To wallahi kin ji na rantse ranki zai yi mugun ɓacuwa akan rashin kunyan da kike mini, har kina ƙiran kanki shegiya kina faɗa mini kenan me nayi na haifeki? Banafsha...." Maganan bakin Mami ne ya sarƙe sai ga hawaye a idanuwanta, saurin juyawa tayi dan kar Banafsha ta gani, abinda bata sani ba kuwa duk da yanayin da nake ciki naga zubowan hawayenta.

Mami juyawa tayi tana ƙoƙarin danne hawayenta amma ina sun ƙi stayawa, ɗakinta ta shige kawai ta kulle, kan gado Mami ta faɗa tare da sakin sabon kuka tana jin duk abinda ya faru shekaru ishirin baya yana dawo mata sabo dall kaman yau abin ya faru, cikin kuka ta ce, "Duk wanda ya aikata wannan mummunan tabo gareni in har da son ransa ban yafe masa ba duniya da lahira, in kuma shi ma bai yi da niya ba na yafe masa, amma duk mai hannu a faruwan wannan mummunan ƙaddara gare ni Allah zai saka mini, ban yafe ba, ban yafe ba, ban yafe ma ko waye ne ba, astagfirullah Ya Rabbi!..." Haka Mami ta dinga sumbatu tana kuka, saboda duk maganan da Banafsha take faɗa mata baya damunta sosai, amma maganganun yau ya soketa sosai, ya tuna mata da abinda bata son tunawa a rayuwanta, ya tuna mata da lissafin da ta jima da cire shi a rayuwanta, ta stani baya bata son tuna baya domin bata ji daɗin baya ba, haka Mami ta dinga kuka har sai da kanta ya fara mata mugun ciwo.

Banafsha kuwa Mami na barin wajan ita ma ta ɓarke da nata kukan mai cin rai, ga ciwo a zuciyanta ga ciwon mara, ita ji take ma ta Mami ta bugeta har ta kasheta da ya fi mata daɗi, ko kaɗan bata ji zafi ko raɗaɗin marukan da Mami ta mata ba, kuka take kaman ranta zai fita, gaskiya ce ta faɗa wa mahaifiyarta, amma kuma ba wai dan ta sanya ta a damuwa ta saka ta zubar da hawayenta ba, lallaɓawa Banafsha tayi a dudduƙe ta ja jikinta ta ƙarisa ƙofan ɗakin Mami, tana turawa ta ji a kulle, a hankali da muryan kuka ta ce, "ki yi haƙuri Mamina, Allah ya huci zuciyanki, ba niya na saka ki a damuwa ba, niyana tunatar da ke da kuma baki shawara a mastayina na ƴar ki, Mami auren Abbaa Insha Allah alkairi ne gare ki Mamina, ki yi haƙuri ki auri Abbaa, shi cikakken me ƙaunaki ne Mami, wallahi ni nasan Abbaa zai fi Alhaji riƙe ki da amana, ki yi haƙuri Mami."

Mami bata yi niyan yin magana ba, amma jin abinda Banafsha ke faɗa sai wani abun ya ƙara tokareta, stawa ta daka mata ta ce, "Banafshaaa! Ki ɓace mini a ƙofa kamun na fito na saɓa miki, shashashan yarinya wacce bata gudun ɓacin ran mahaifiyarta, duk haƙurin da nake akan rashin kunyan da kike mini, ke burinki kawai ki sa na miki baki ko? To ki cigaba kada ki dena zan miki bakin da kike so na miki, ɓace ki bani waje."

Na buɗe baki zan bai wa Mami haƙuri, ta kuma sake mini wani gigitaccen stawan da ya saka ni barin ƙofan ɗakinta ban shirya ba, marana mugun murɗa mini yake ga kukan da nayi, tuni zazzaɓi yake son mini mugun kamu.

Umaima bayan ta je tahfiz an tashi, Malam Abbo ya ƙara ba da saƙon gaisuwa zuwa ga masoyiyarsa Banafsha, Umaima ko da ta dawo bata shiga gidansu ba sai ta yi hanyan gidan su Banafsha, kuma dai-dai lokacin Umma ta fito a gida kenan, wani irin mugun kallo Umma ta bi Umaima da shi, tuni Umaima ta sha jinin jikinta tare da fara yarfe hannu dan tasan yau sai dai ɗan buzunta, Umma fasa fita tayi ta juya cikin gida, Umaima haka ta bi bayan Umma tana faɗin, "Ƙulya ƙulle bakin Ummana".

Ummu tana zaune a palour, tunda ta ga yanda Umma ta shigo sai ta girgiza kai kawai dan bata san me kuma ya faru ba, Umma dakinta ta shige tana ƙwafa dan yau ba mai hanata daka Umaima sai ikon Allah.

Umaima haka ta shigo tana raɓe-raɓe kaman wacce ta yiwa sarki sata, Ummu tana ganin Umaima tasan to da wani abun, kamun Ummu ta buɗe baki Umaima ta ce, "Ummu ki bawa Umma haƙuri kada ta dake ni, wallahi saƙo na je kai mata malaminmu ne ya aike ni wajanta."
Chapter 34 · 0% Book details