Sashe 35
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummu da ba ta gane ba ta ce, "Wajan waye kuma aka aike ki, kin dawo makaranta ba za ki taho gida ba, ina kika bi har Ummanki ta haÉ—u da ke a can."
Umaima kaman za ta yi kuka ta ce, "Ummu wallahi ba inda na je, gidan su Banafsha ne kawai, kuma ban shiga ba da naga Umma."
Ummu shiru tayi kawai ta rasa me za ta ce, dan tasan muddim Umma za ta daki yaranta, to bata isa ta ce ƙala ba, in ma ta saka baki to yanzu kuma faɗan zai dawo kanta.
Umaima ta yi rau-rau da ido ta ce, "Dan Allah ki bata haƙuri Ummu."
Ummu ta buÉ—e baki za ta yi magana sai suka jiyo muryan Umma tana faÉ—in, "Dan ubanki, kin staya a wajan uwarki ta biyu ko ba za ki zo ba ina jiranki."
Umaima baya-baya ta fara za ta juya, sai Ummu ta girgiza mata kai ta ce, "a'a kar ki gudu Umaima, kije ki bata haƙuri, babban budurwa da ke Ummanki ba za ta dake ki ba, faɗa za ta miki kuma ko me ta ce ki bata haƙuri, ki ce kin ji kin daina."
Umaima ɗaga kai tayi tana tafiya a hankali kaman wanda ƙwai ya fashewa a jiki, har ta shiga ɗakin Umma da sallamanta, Umma kuwa ko amsawa bata yi ba ta miƙe ta saka wa ƙofanta sakata, mugun kallo ta jefawa Umaima ta ce, "Me na ce miki ranan? Wato sai dai na stine miki ki lalace nine da asara ba uwar kowa ba ko? To kuwa ko ban stine miki ba zan daka ki sai na sauya miki kamanni, idan tare aka haifo ku da ita za ki faɗa mini yau."
Umaima ta buɗe baki za ta bawa Umma haƙuri, amma ina sai sauƙan bulala ta ji a jikinta ko ta ina, Umaima na ihu, Umma na dukanta kaman an aiko ta bata fasa ba.
Ummu na zaune a palour, tana jin ihun Umaima ta taho da sauri duk da bata shiga ɗakin Umma, amma ta tura ƙofan da niyan shiga, sai ta ji da gam a garƙame da sakata, magana take tana faɗin, "Dan Allah dan Annabi SAW ki ƙyaleta ki yi haƙuri Maman Kabeer, ki bar dukanta haka nan...." Magiya Ummu ta dinga yi amma Umma ko jin ta bata yi ba, balle ma ta saurareta kawai jibgan Umaima take yi.
Umaima tun tana kuka da ƙarfi har ta zube a waje guda muryanta ya dishe, ba abinda take faɗi sai, "ki yafe ni Umma, ki yi haƙuri ba zan ƙara ba, wallahi Abbaa ne ya ce muje, ki yi haƙuri Umma ki mini rai, zan mutu, wayyoooo! Ummuna!!!" Umaima na faɗan haka ta sume.
Umma duk da Umaima ta sume amma dukanta take zuciyanta kaman zai faso ƙirjinta ya fito, magana take kaman zararriya, "Ni za ki mayar ƴar iska bansan me nake yi ba, wato kin faɗawa ubanki sai ya saka ki gaba kuka je, ban isa da ke ba, to gwanda ma na kashe ki na huta da ki kasheni da naki takaicin, har da ke ubanki zai je zance, duk munafurcinku ne ya ja in ba haka ba, me za'a yi da karuwa a kishiya, ai sai ta addabi kowa ta ishi kowa ta nemi ɗaga mutum akan yaransa..." Umma tana magana tana dukan Umaima tana haƙi, har sai da ta ji kaman za ta sume ita ɗin ma, sannan ta jefar da bulalan ta jawo ruwa ta kwankwaɗa ta wastawa Umaima, wani wawan ajiyan zuciya Umaima ta sauƙe tare da sakin marayan kuka tana numfashi a hankali-hankali.
Ummu kuwa da ta gaji da magiyan, ficewa tayi ko ta duba samarin gidan amma ba kowa, Abbaa ma bai dawo ba, haka ta dawo cikin gidan lokacin Umma ta gama jibgan Umaima, Ummu kaman za ta yi kuka haka ta koma ƙofan ɗakin Umma, amma har lokacin bata buɗe ƙofan ba, ƙarshe Ummu ɗakinta ta koma.
Umaima na zube a wajan, Umma ko ta kanta bata bi ba, ta shige bayi ta wasta ruwa, ƙwafa tayi tare da kallon Umaima ta ce, "tashi ki fice mini a ɗaki, idan kin so gobe na hanaki yin abu ki yi, idan yayanki ya dawo kuma na faɗa masa ya ƙara miki, kinsan dukansa kuma sarai."
Umaima ko yastanta ta mosta raɗaɗi take ji, dan ta daku sosai ba ƙarya, Umma tsawa ta mata, dan dole Umaima ta ja jikinta tana kuka ta shige ɗakinsu, ga shi Ummu bata san ta fito a ɗakin Umma ba, haka ta zube a stakar ɗakinsu tana kuka har baccin wahala yayi gaba da ita.
Ummu kuwa tana ɗakinta, bata san Umaima ta fito ba, har Abbaa ya dawo a palourn sa na cikin gida ya gama komai ya tafi wajan Mami, har ya dawo duk bai san wainar da ake toyawa ba a cikin gidan, sai da ya shigo ciki ya ji gidan shiru kaman ba kowa, ɗakin Umma ya fara shiga sai ya sameta tana sallah, juyawa yayi ɗakin Ummu, samunta yayi ta haɗa hannayenta ta tallafe kuncinta, Abba ƙarisawa yayi wajanta ya zauna tare da cire mata tagumin da ta yi, Ummu ɗagowa tayi ta kalli Abba sai kawai ta faɗa jikinsa tana faɗin, "Dan Allah kabar maganan auren Mamin Banafsha, ka yi haƙuri, kuma ka ce Umaima ta bar shiga gidan, komai ya wuce, zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki."
Abbaa kallonta yayi ya ce, "Me ya faru? Me yasa kika ce haka? Bayan ke kika kawo shawaran kuma na amsa, meyasa?"
Ummu kaman za ta yi kuka ta ce, "nidai dan Allah ka bari, nasan ni na bada shawara amma kuskure nayi, dan Allah ka mance da batun ka ji Alhaji."
Abbaa miƙewa yayi ya ce, "Ba zan zamo mutumin banza ko kuwa mijin da ake juyasa ba, ke kika yi magana ba ni na ce ba, dan haka bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na samu Ramla na faɗa mata abinda ake ciki, yanzu haka amsanta nake jira, kuma ina da tabbacin amsan nata eh ne" yana gama faɗa ya nufi hanyan waje fiska ba sassauci, ta ya za ta ce abu kuma yanzu ta ce a'a idan ba ta renasa ba, to shi ya riga da ya sakawa zuciyansa son Mamin Faɗima, kuma idan har bai aureta ba Allah ne kawai bai nufa ba.
Ummu jiki a sanyaye ta ce, "ka yi haƙuri Abbaansu ba nufi na kishi nake yi ba, duk da nasan kishi dole na yi sa tunda ina ƙaunanka, amma ba hakan bane dalilin maganana, ka je ɗakin Maman Kabeer ka duba halin da Umaima ke ciki, na tabbata kai ma za ka fahimci janye maganan nan shi ne alkairi da zaman lafiya."
Abbaa bai kuma cewa da Ummu komai ba ya fice a É—akin, É—akin Umma ya koma lokacin ta idar da sallah, ba murmushi ba komai kaman an mata dole ta ce, "Sannu da dawowa."
Abbaa ko ta sannunta baya yi ya ce, "Ina Umaima?"
Umma taɓe baki tayi ta ce, "tana ɗakin su."
Abbaa bai ce komai ba ya juya, da sallama ya shiga ɗakin su Umaima, bai ma kula da ita a stakar ɗakin ba, sai da ya ga bata kan gadonsu sannan idanuwansa ya sauƙa a stakar ɗakin, da mugun sauri Abbaa ya nufe ta a rikice yana faɗin, "Ummu-khultum lafiya?"
Umaima ta jima da tashuwa daga baccin wahala, amma zuwa lokacin jikinta yayi stananin stami, ba abinda take sai aikin nishi, ko da taji Abbaa na ƙiran sunanta ba daman amsawa, sai kuka ta sanya wanda idan ba kana kallonta ba, ba za ka ji sautin kukan ba saboda yanda muryanta ya dishe.
Abba yana taɓa jikinta yaji yayi zafi sosai, ya juyo da ita kuwa ya ga fiskan a kumbure alaman ta sha kuka, kallonta yayi cikin damuwa ya ce, "Me ke damunki Umaiman Abbaa?"
A hankali take mosta laɓɓanta tana jan zuciya ta ce, "Umma ceeeee" ta ƙarishe maganan kaman za ta sume.
Abbaa ficewa yayi ya nufi ɗakin Umma, amma ya samu ta kulle ƙofa, bugawa yayi taƙi buɗewa, ɗakin Ummu ya koma ya ƙirata, tana shigowa ta kalli Umaima sai ta fara hawaye tana mata sannu, Umaima lumshe ido tayi cikin azaban da jikinta ke mata, Abbaa ya ce, "Khultum shiryata mu tafi asibiti" yana faɗa ya fice.
Ummu haka ta ƙoƙarta ta ɗaga Umaima ta ja ta banɗakinsu da ke cikin ɗaki, ruwan zafi ta koma ta ɗauko a ɗakinta ta zo ta haɗa ruwa, kamawa Umaima jikinta tayi, ta mata wanka ta shiryata sannan ta yiwa Abbaa magana akan ta gama.
Abbaa da kansa ya ɗauki Umaima suka fice a gidan, asibiti ya kai ta a cikin gari, sai dai an kama su a gado, dole Ummu ta kwana a asibiti, shi kuma Abbaa ya koma gida, bai bi ta kan Umma ba dan tabbas zai yi abinda ba dai-dai ba, mataki ne kuma ya ɗauka, in Allah ya yarda zai auri Mamin Faɗima ya ga ta ƙarshen rashin mutuncin ta.
Æangaren Mami da Banafsha haka suka kwana, ba wanda ya fito balle ya sa wani abu a cikinsa, Mami sai da dare tayi sosai sannan ta fito ta zo É—akin Banafsha, samu tayi tana bacci jikinta da zafi, kayan jikinta ta rage mata ta share mata jiki da towel mai sanyi, sannan ta tofa mata addu'a ta ja mata Æ™ofa ta koma nata É—akin, alwala Mami ta É—aura ta dinga sallah, har sai da ta ji Æ™iran assalatu, bayan tayi sallahn asuba tayi ayyukanta ta gyara gidan staff, É—akin Banafsha ta shiga ta sameta ta fito wanka kenan, Mami murmushi ta sakar wa Banafsha ta ce, "shalelen Mami har an tashi, fatan jikin da sauÆ™i?"
Banafsha wani abu ne ya soki zuciyanta, sai take jin sam-sam bata kyauta ba duk da gaskiya ce, amma Mami bata chanchanci haka daga gare ta ba, hugging na Mami ta yi ta amsa da sauƙi, ta gaisheta ta amsa, Banafsha ta ce, "ki yi haƙuri Mamina."
Murmushi Mami tayi ta ce, "ya wuce Allah miki albarka, Allah shirya mini ke."