← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 58

Sashe 12

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Stohon nan jin zagin Mami sai ransa ya ɓaci ya ce, "naji ba da kuɗin ubana kika gina ba domin kuɗin ubana yafi ƙarfin ki, kuɗin ubana kuɗin halal ne ke kuma karuwa ce ita kuma ƴar taki da kike tunani tana da mutunci to bata da sauran mutunci, don kuwa ƴar karuwa ce ita, maras mutunci har ni za ki gani ki zaga? To wallahi ba yarinyarki ba aure, kuma ita ma Insha Allahu sai tayi abinda kike yi, sai ta lalace, sai ta yi abinda ma ba ki yi ba tunda kika ɗaura hannunki a jikina saboda ita" ya faɗa yana ficewa a palournmu da kayansa a hannunsa.

Cikin kuka nake bin su da ido, shi da Mamina duka har ya fice, Mami zuwa tayi wajena ta zauna, tana ƙoƙarin ɗaura hannunta a jikina na miƙe cikin gaggawa ina kuka na shiga ɗakina da gudu ina kuka mai cin rai, abubawan da ke faruwa ya fara isa ta, bana jin zan iya daurewa, abin da yawa wai shege da hauka, ga shi shege ga shi mahaukaci.

***
Ina kyautan page ne ga masu Sharhi yanda ya kamata, da kuma waÉ—anda ke bada gudumawa a tafiyar wannan littafi, sister ba kya Sharhi kuma kar ki ce ba'a baki page ba, littafi dai yanzu aka fara tukunna ba abinda muka yi, so a dage da Sharhi fan's.

Lurv you all

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

Ummu muhammad
Maman Mhm'd
Nana Khadijah
Feenah's touch (Allah Ubangiji ya baki lafiya dear)🤲

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 26 _ 30

A haka na cigaba da risgar kukana, har ɓarawon bacci yayi awun gaba da ni, kuma tun daga wannan ranar ko ƙofan gida ban ƙara fita ba, balle kuma ayi maganan makarantar boko, ko kuma Tahfiz dan wannan abu da ya faru da kalaman mutumin nan ya dame ni ba kaɗan ba, nan dai na dinga salloli kawai ina karatun Alƙur'ani dan samun nistuwa, tsakanina da Mamina sai gaisuwa duk yanda ta so nayi magana naƙi yi, sai dai Umaima idan ta shigo mu yi magana sama-sama ita ma, amma bana iya dogon magana dan kuwa inajin ciwo a rai na, duk abinda ya faru kuwa ko kuka na kasa yi tun ranan alhamis da abun ya faru har yau da yake Lahadi.

Yau ma kaman ko yaushe ina cikin ɗakina, ina zaune a kan darduma da Alƙur'ani a hannuna, shigowa Umaima tayi ɗakin da sallama ta same ni da Qur'anin na buɗe na zuba masa ido amma ba karatun nake yi ba, har ta gama sallamanta ban ji ba, sai da ta taɓa ni kamun na ɗago firgit na zuba mata idanuwana da kana ganinsu za ka ga raman da nayi, cikin damuwa ta ce, "Masoyiya mene haka wai? Duk kin bi kin sauya, duba fa har ramewa kike yi, kuma na tambayeki kin ce ba komai, me yasa kike yin haka ne Banafsha? Ko kina so damuwa ya faɗar da Mami ne? Ke kin ƙi zuwa boko kuma kin ƙi zuwa tahfiz, kin sa hankalin Mami ya tashi, yanzu ke hakan ya miki?"

Lumshe idanuwana nayi kawai ba tare da na bata amsa ba, tunda na amsa sallaman da ta yi ban ce komai ba, ganin nayi shiru kuma tasan halina idan na yi hakan ba maganan zan yi ba, ko ya za'a yi da ni, sai ta girgiza kai kawai ta ce, "Allah ya kyauta! Idan kin gama shirun naki sai ki fito, Malam Abbo yana palour yana jiranki, kuma ya jima da zuwa."

A ɗan razane na buɗe idanuwana na kalleta, na kuma maimaita sunan da ta faɗa "Malam Abbo!", wani nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe wanda bansan nayo sa ba, a zuciyana na ce, "To me ya kawo sa gidanmu?"

Muryan Umaima na tsinkayo tana faÉ—in, "Idan kin fito ai zai faÉ—a miki abinda ya kawo sa gidanku, ni dai dan Allah ki fito dan ya jima da zuwa", Umaima na gama faÉ—an haka ta fice a É—akin.

Ni kuma da kallo na bita har ta fice ina mamaki, ashe maganan nawa a fili nayi ba'a zuciya ba, sai kuma gefe guda da nake tunanin abinda ya kawo sa gidanmu a irin wannan lokaci, kuma dai na ga ban wani jima da daina zuwa makarantar ba, share tunanin nayi na miƙe tare da rufe Qur'anin, na ajiye sa a wajan zamansa, ba tare da na tsaya yin komai ba na nufi hanyan palourn tunda daman ƙaton hijabi ne a jiki na, Umaima ta faɗa mini ya jima da zuwa, banson na tsaya ɓata lokaci ya ga kaman na renasa ina ɗalibarsa, kuma nima a maste nake naji abinda ya kawo sa.

Da sallama na shigo palourn namu, inda na same sa zaune a ɗaya daga cikin kujerun palourn, cikin shigansa ta alfarma da kamala kaman ko yaushe, Malam Abbo kyakkyawan gaske ne, sanye yake da jamfa dark-green mai ɗinkin da ake kira half-jamfa, da hulansa sannan ƙafan sa har da safa, agogo mai kyau ne a maƙale a hannunsa wanda idan ka gani za ka ɗauka ya kai na dubbanni saboda haɗuwan agogon.

Malam Abbo kenan saurayi matashin Malami mai ji da kyau da kuma ilimi boko da Arabic, namiji ne shi har namiji, duk inda ake neman namiji cikakke to ya kai.

Asalin sunan sa ALIYU HAIDAR haifaffen cikin garin Mubi ne, inda suke zaune da iyayensa a anguwan kwaccam amma ba kusa da gidajenmu ba, mahaifinsa da mahaifiyarsa duka malamai ne, shi mahaifin nasa limamin masallacin juma'a ne na Æ´an shi'a a cikin Mubi.

Malam Abbo shi ne ɗan Auta a wajan iyayensa, yana da yayyu maza biyu da yayyu mata biyu, Malam Abbo ba zai wuce shekaru ishirin da shida zuwa da takwas ba, kuma kyakkyawa ne shi na bugawa a jarida, yana da ilimi sosai-sosai a boko ya karanci Islamic Education, yayi har degree biyu, a addini kuma yana da haddan Qur'an mai girma complete a kansa da tafseer nasa da komai, yana da littatafai a kansa ba adadi kuma har yanzun yana kan ƙara karatun ne, domin musabaƙan sa na ƙarshe anɗau nauyin karatunsa da komansa a Madina, kawai bai tafi bane, amma idan ya shirya ko yaushe komai nasa yana nan ready.

Cikin nistuwa na samu waje na zauna a ƙasa tare da sunkuyar da kai na, a hankali cike da ladabi na gaishe da Malam Abbo, shi kuma ya amsa mini yana murmushi.

Umaima da ke zaune can gefe da ni kaɗan, miƙewa tayi ta ce, "Banafsha na gudu gida Umma ta aike ni."

Na ɗago kai zan ma Umaima magana, cikin rashin sa'a na haɗa ido da malam Abbo da ya zuba mini idanuwansa, wani iri naji a jikina nayi saurin yin ƙasa da kai na tare da cewa, "To sai kin dawo, ki gaishe da Ummu."

Umaima ficewa tayi bayan ta yiwa Mamina da Malam Abbo sallama, sai da ta fice sannan Malam Abbo ya dubeni ya ce, "tashi a ƙasa Malama Faɗima."

Kai na a duƙe ina wasa da yastuna na ce, "Nan ma yayi Malam."

Malam Abbo yayi-yayi na koma saman kujera amma naƙi, ganin na dage sai ya ƙyaleni kawai yayi murmushi, tare da gyaran murya ya ce, "Malama faɗima kinga na biyoki har gida ko? Nasan kina mamakin me ya kawo ni ko?"

Murmushi kawai na yi kai na a ƙasa har yanzu, kuma ban ce komai ba, dan kuwa gani nayi Malam Abbo kaman ya karance zuciyata ne.

Shi kuma ganin murmushin nawa sai hakan ya wadatar da shi amsan da zan buɗe baki na basa, cikin nustuwa ya fara magana, "Malama Faɗima da farko dai zan tambaye ki abinda ya hanaki zuwa makaranta, duk da bai kamata na tambayeki har gida ba, kamata yayi kije makaranta ki faɗa mini dalili, idan ta kama ta hukunci kuma sai na miki, idan na yafiya ne kuma sai na miki afuwa, to yanzu bisa ga wani dalili ga ni har gida, kuma ina tambayarki me ya hanaki zuwa kwana biyu, bayan kinsan akwai maganan musabaƙa da ake staka da shi."

Wani nauyayyan ajiyan zuciya na sauƙe jin tambayan Malam Abbo, wanda nasan da shekara za'a yi yana tambayana irin haka, to za'a kwashe wani shekaran nima ban basa amsa ba, balle na faɗa masa gaskiyan abinda ya faru ko ya hanani zuwa makarantar, kuma ga shi dai a rayuwata ni ban iya ƙarya ba, dole shirun dai shi zan yi, saboda wannan sirrinane ni da mahaifiyata, ko Umaima ba zan sanar da ita abinda ya faru ba balle wani a gefe, ban taɓa jin zan iya ɓoye wa Umaima wani abu ba sai wannan lokacin، a hankali na haɗiye wani mugun yawun da ya tokare mini maƙoshi na tuno abinda ya faru ranan, ɗago kai na nayi tare da kallon Malam Abbo, jin hawaye na neman zubo mini sai nayi saurin yin ƙasa da kai na ina haɗiye kukana da hawayena, dan basu da amfani tunda ko yaya za'a yi da ni ba faɗan dalilin zubansu zan yi ba.
Chapter 12 · 0% Book details