← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 58

Sashe 41

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKI NE

Surayyatou nah

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

BUNAYD: is a name use for baby boy's, that mean's sᴛʀᴏɴɢ, sᴛᴏʀᴍʏ ᴀɴᴅ ᴘᴏᴡᴇʀғᴜʟ, and also is a name that identify a specific ethnic, like halimatu-sa'adiya, the real name is halima, sa'adiya is her ethnic name.
Bunayd or Bunaid, in other face mean is ethnic name which located in Pakistan, in Muslim's society, the name is usually use as nick name for those with name Muhammad.
The name origin is Pakistan.

🅿️ 66 _ 70

Washe-gari da safe na shirya tafiya College da wuri, bayan na gaishe da Mamina ta amsa, sai na ce, "Mami zan bi gidan su Umaima kamun na wuce, Malam Abbo ya ce mini ita ma kwana biyu ba ta je makaranta ba, bansan ko me ya sameta ba."

Mami ta ce, "To a dawo lafiya, ki gaishe su, sannan ki kula sosai ko."

Ɗaga kai na nayi alaman na ji, sannan na mata sai na dawo na fice, ina ƙoƙarin shiga gidan su Umaima sai ga ta ita ma ta fito da shirin zuwa College, murmushi muka sakarwa juna, na ce, "Umaimatyna."

Murmushi Umaima ta mini wanda hankalina bai kwanta da shi ba, ina tunanin ma na ƙarfin hali ne, bata ce mini komai ba kawai ta riƙe hannuna muka yi gaba, ni bin ta nake kaman mara lafiya dan jikina yayi sanyi, bansan me yasa tayi haka ba, amma dai na yi shiru, muka nemi mashine muka tafi College.

Mun wuni a makaranta muna ta lecture's, amma kwata-kwata na kasa ganewa Umaima, gaba É—aya bata son yin magana sosai, Æ´ar rigiman da muke yi da stokanan juna duk yau babu, sai dai murmushi kawai take mini idan na yi magana, kasa jurewa nayi da hakan, ana tashinmu muna tafiya kan mu samu mashine na ce, "Umaima me ya faru? Me na miki? Ko ba ki da lafiya ne?"

Mashine ta tare mana muka shiga, ƙara kallonta nayi na ce, "masoyiya me ke faruwa dan Allah?"

Umaima murmushi ta sakar mini ta ce, "Me ne kika damu kanki haka Banafshaty, lafiya fa ba komai."

Kallon Umaima kawai nake yi ba dan na yarda da abin da ta faÉ—a ba, numfasawa nayi na ce, "To me ya hanaki zuwa makarantan tahfiz kwana biyu?"

Nan ma shiru Umaima tayi bata ce komai ba har muka isa gida, mashine na ajiye mu ta kalleni da murmushin ƙarfin halin da take mini tun safe ta ce, "Banafshaty ki gaisar mini da Mami", ta faɗa tare da yin gaba ta shige gidansu.

Haka Umaima ta tafi ta barni a staye a gantale ta shige gidansu, sai da na gaji da tsayuwa sannan na numfasa na juya cikin damuwa na shige namu gidan.

Mamina na samu zaune a palourn tana waya, jakana na ajiye a kan kujera na shige jikin Mamina na lafe, ba tare da na ankare na bacci ya fara yin gaba da ni, sai da Mamina ta gama wayan da take yi sannan ta shafa kai na ta ce, "Fatu kulen Maminta, shugabar masu son jiki tashi kada ki karya ni."

Ni kuwa tuni na fara bacci ban ma ji me Mamina ke faÉ—a ba.

Mami sunkuyawa tayi ta kalli fiskana, ganin bacci na fara sai ta murmusa ta girgiza kai kawai, a hankali ta bubbuga bayana ta ce, "tashi kije ki cire kayan makarantan, idan kin wasta ruwa sai ki kwanta ki yi baccin, dan da alama yau kin ajiye wanda zai je miki tahfiz É—in."

Cunna baki nayi, cikin shwagaɓa na ce, "Mami jikinki ne daɗin kwanciya shiyasa na ji bacci."

Murmushi Mami tayi ta ɗaga ni, amma na koma na lafe na ce, "Mami yau bansan me ya samu Umaima ba, magana ma da ƙyar take mini."

"Ba sai ki tambayeta ko wani abun ya faru ba Banafsha" faÉ—in Mami tana É—aga ni.

Zama nayi sannan na ce, "Mami wallahi na tambayeta, da farko ta yi shiru, daga baya ta ce ba komai."

"To wataƙila ko bata jin daɗine, ko kuma wani abun daban, amma ki bata kwans biyi idan ma bata da lafiyane Inshà Allah za ta ji sauƙi, kuma za ta faɗa miki, kada ki damu kanki kinji ƙawar Umaima."

"Uhmñ!" Kawai na faɗa na miƙe na ɗau jakana na shige ɗakina, sai da na cire uniform na watsa ruwa, sannan na fito na ɗau abinci na cika cikina, sai na koma na kwanta, kamun lokacin tahfiz yayi.

Yamma na yi na tashi na shirya, nan ma a ƙofan gida muka haɗu da Umaima, yanzu ma yanayinta kaman ɗazu da safe, haka har muka isa tahfiz, mun yi karatu har aka tashemu, sannan muka kamo hanyan gida, muna tafiya sai ga Malam Abbo, ba daman na ɓata rai ko wani abu, murmushi ya sakar mini ya ce, "Sayyadata ina zuwa anjuma."

Tura baki nayi na ce, "ka yi haƙuri Malam zan yi aiki."

Ba tare da damuwan komai ba Malam Abbo ya amsa da shikkenan ba mastala, ya juya abinsa, mu ma muka yi gaba, Umaima murmushi tayi ta ce, "Sayyadar Malam Haidar."

Taɓe baki nayi na harare ta na ce, "Tun da kin ƙi faɗa mini abinda ke faruwa, ba ruwana da ke kada ki mini wani magana "

Murmushi ta kuma yi ta ce, "To Allah ya sanya alkairi Banafshaty, Allah kuma ya tabbatar da alkairi, ashe da tabbata gaskiya ne hasashen É—alibai."

Ban ce mata komai ba, muka cigaba da tafiya har muka isa gida, Umaima ta shige gidansu, nima na shige gidanmu.

Haka muka kwashe kwanaki har muka cinye wannan satin yanayin Umaima ya ƙi sauyawa, kuma ta ƙi faɗa mini abinda ke faruwa, sannan a gefe guda kuma Malam Abbo kullum sai ya takura akan zai zo, ni kuma sai na dinga kawo masa uzurina duk saboda bana son ya zo, ni bana buƙatar shaƙuwa sosai ya shiga tsakaninmu, dan kada ma gaba idan na nuna bansan zancen ba, shi kuma ya ce na yaudaresa.

Yau da yake Friday ne muna da class na ƙarfe bakwai, da wuri na shirya, muka haɗu da Umaima a ƙofa yanda muka saba haɗuwa kwanannan, mashine muka shiga ya kai mu makaranta, mun yi lecture's har lokacin sallahn juma'a yayi aka fita kamun a sauƙo juma'a kuma.

Ni da Umaima daman ba damuwa muka yi da zuwa masallacin school ba, dan haka alwalanmu muka yi, muka yi sallahnmu a ƙasan wani bishiya mai inuwa inda muke zama, sai da muka idar sannan na kalli Umaima cikin damuwa na ce, "masoyiya dan girman Allah dan darajan Annabi ki faɗa mini abinda ke faruwa, idan ma wani laifi na miki ai sai na baki haƙuri, idan wani abun ne ai gwanda na sani zai fi, masoyiya ki tuna fa, duk abinda ke faruwa da ni kin sani, wanda ba ki sani ba ma ina sanar da ke, mastayin Aminiyata na baki, banda wacce zan nuna na ce ƙawata ce sai ke, masoyiya da ke nake shawara, ke ce abokiyar kukana kuma abokiyar dariyana, to me ya sa abu zai faru ke ba za ki faɗa mini ba, sai ki dinga shashshareni, ko dai ke ba ki bani mastayin da na baki ba ne?" Na ƙarishe maganan ina kallon cikin idanuwanta.

Umaima murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi, bata ce mini komai ba sai hijabinta da ta É—aga ta nuna mini dansten hannunta, ban dawo daga duniyan da nake ba ta kuma nuna mini gadon bayanta, cikin damuwa na ce, "Umaimaaaa!! Me ya same ki? Wannan shatin bulala ne fa, wa ya miki wannan duka? Naga dai banji mostin Ya Danish ba wannan weekend É—in, dan Allah me ya sameki Umaima" na faÉ—a kaman zan yi kuka.

Murmushin Umaima ta kuma yi, ta buɗe baki za ta yi magana kuma sai ga hawaye, ganin kukanta nima sai hankalina ya tashi, ga shi dai-dai lokacin malamai sun sauƙo juma'a, an koma mana aji, haka na lallasheta muka koma class.

Sai wajan ƙarfe biyar aka tashemu, muna fitowa class Umaima ta labarta mini abinda ya faru har kwanciya a asibiti da ta yi, tana bani labarin har muka samu mashine muka shiga, ni kuwa cikin tausayi da damuwa nake sauraranta, uwa dai uwa ce amma wani abun sai a hankali, lallai dole Allah ya ce a duk halin da kake ka gode masa, kuma kowa da tasa jarabawan da Allah ke jarabtansa, ga ni dai mahaifiyata tana rayuwan da ba kyau har ana ƙirana ƴar karuwa, ina damun kai na bayan wannan shi ne jarabawana, indai Mami ta sa hannunta a jikina to fa ni ce na nema, garin faɗa mata gaskiya na faɗa mata maganan da bai mata ba, amma bayan haka Mami ko hararana bata yi, to ga Umaima wacce mahaifiyarta ba ta da wani mugun tabo, tana da mutuncinta a gidan aurenta, amma akan abinda bai kai ko stawa a yiwa mutum ba, Umma ta mata wannan mugun duka, to Allah kyauta ya raba mu da iyayenmu lafiya.

Mashine na sauƙe mu, muka fara tozali da Ya Danish zaune a bayan motansa idanuwansa a kan hanya kaman mai jiran isowan wani abu, ina ganinsa na ji gabana ya faɗi haushi ya turnuƙe ni, tuni na haɗa fiska ko kallonsa ban yi ba muka yi sallama da Umaima na shige gidanmu, ita ma ta shige nasu gidan bayan ta gaishe da Ya Danish da idanuwansa ke kai na.

Malam Abbo da ya gaji da bin Banafsha zai zo zance, ta ƙi basa dama sai abin ya damesa, dan haka daman yana da shirin yi wa Mami magana akan Banafsha, sai ya shirya staff abinsa, yana dawowa sallahn juma'a ya nufi gidan Mami, cikin takunsa na nistuwa yake tafiya har ya isa, da kansa ya shiga gidan yayi sallama.

Mami da ke zaune a palour ta sha wankan juma'an ta, amsa sallaman ta yi ta yafo mayafinta ta leƙo, ganin Malam Abbo ne tana murmushi ta ce, "Kai ne Malam Haidar."
Chapter 41 · 0% Book details