← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 58

Sashe 42

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Abbo da fara'a yana sunkuyar da kai ya ce, "Nine Umma, barka da gida."

Mami ta ce, "ka iso ko."

Malam Abbo bayan Mami ya bi ya shiga palourn, stugunnawa yayi zai gaisheta sai Mami ta ce ya zauna bari ta kawo masa ruwa, yana cewa da ta bari, amma Mami ko nuna ta ji bata yi ba ta wuce, ta kawo masa abun sha, sannan ta zauna, Malam Abbo durƙusawa yayi ya gaisheta.

Mami ta amsa tana murmushi ta ce, "Sannunka da zuwa Malam Haidar, ya kuma haƙuri da su Faɗima."

Malam Abbo baki kaman zai yage dan murmushi, sai sunkuyar da kai yake yi irin ana gaban surkuwan nan, cewa
yayi, "Ba komai Umma, Allah ne da haƙuri da mu, Malama Faɗima yanzu kam Masha Allah, kwana biyu da bata zo ba ma, Malama Ummu-khultum ta faɗa mini cewa bata ji dad'i ba ne, fatan jikin da sauƙi?"

"Da sauƙi sosaima Malam Haidar, dan yanzu haka ma suna boko, mun gode sosai-sosai fa, Allah yayi albarka Allah ya taimaka, dama ita Faɗima indai makaranta ce to sai ciwo ke hanata zuwa, shiyasa wancan lokacin ma na je makarantar naku da kai na dan ka zo ka mata faɗa, bata taɓa irin haka ba sai hankalina ya tashi sosai."

"To Allah ya kiyaye na gaba Umma, Allah ƙara mata lafiya Alfarman Annabi SAW."

"Sallallahu Alaihi Wasallam, Ameen Malam Haidar, ga shi kun yi saɓani bata nan" faɗin Mami tana murmushi dan ta jima da fahimtan akwai abu tsakanin Banafsha da malaminta.

Malam Abbo ƙara duƙar da kai yayi ya ce, "Umma daman wajanku na zo, ita kam mun gama magana da ita."

Mami ganin bai sha ruwan ba yana jin kunyanta, sai ta miƙe ta ce, "To ka sha ruwa bari na zo" tana gama faɗa ta shige ɗakinta, tana shiga ta saki murmushi tare da ɗaga hannu sama ta ce, "Allah ka tabbatar mana da alkairi."

Malam Abbo Mami na tafiya, ya buɗe ruwa ya kwankwaɗa dan kada ta ce ya ƙi sha, kuma saboda ya samu ƙwarin guiwan faɗa mata komai, yana zaune ba jimawa Mami ta dawo ta samu waje ta zauna, sannu da fitowa ya mata ta amsa.

Mami ta ce, "yauwa Malam Haidar ina sauraranka."

Malam Abbo ƙasa yayi da kansa cikin kunya ya labartawa Mami yanda suka yi da Banafsha, duk abinda ya kamata ya faɗa mata ya faɗa, kansa a ƙasa sosai ya ɗaura da cewa, "Umma ki yi haƙuri, amma ni ina son Faɗima a ko yaya take, amma ta dage da faɗa mini ba za ta yi aure ba, dan Allah Umma a taimaka mini a saka mana baki."

Murmushi Mami tayi, wanda kana ganinsa kasan na tsantsan farinciki ne da take ciki, hamdala take kawai a zuciyanta, abinda take hasashen ya tabbata, kuma tasan in Allah ya yarda Banafsha ta samu miji wanda zai nusar da ita duniya da lahira, tana kan murmushin ta ce, "Masha Allah! Tunaninka na ka zo da kanka ka same ni yayi sosai Malam Aliyu, kuma ba komai Insha Allah zan yi magana da ita Faɗima ɗin, sannan ka yi haƙuri da abubuwan da ta faɗa maka, Faɗima ta girma ne kawai amma babu wayo, yaranta har yanzu yana damunta sai a hankali, in Allah ya yarda in har ita rabonka ce to za ka sameta."

Malam Abbo ya kasa ɓoye farincikinsa, shi daman ya sani indai ya yiwa Umma magana, to Insha Allahu in ba dai akwai wanda aka bawa ita ba ne, to zai sameta, cikin farin ciki ya ce, "Nagode! Nagode! Nagode! Umma, Allah ya ƙara girma, Allah ya saka da alheri Umma, Allah ya ja kwana ya ƙara girma, Allah ya saka muku da aljanna mafificiya, in Allah ya yarda zan yi wa manyana magana, daman ina son idan muka dai-daita ne ba wani ja'inja a ciki sai na sanar musu."

Mami ta ce, "shikkenan ba mastala, zan yi waa wanda za ku nema auran nata a wajansa magana, duk abinda ake ciki za ta faÉ—a maka, kar ka damu, Insha Allah FaÉ—ima matarka ce."

Malam Abbo saboda farinciki ji yake kaman ya tashi ya sha juyinsa a gaban Mami, amma kunyan surkarsa yake, sai dai dole ya É—ebowa Sayyada Roohinsa shoki akan wannan abun murna da farin cikin.

Malam Abbo sallama ya yi wa Mami ya tashi ya fice q palourn, ba abinda yake yi sai aikin washe baki, kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki, kaman wanda aka ce masa anÉ—aura an kai masa Banafsha É—akinsa.

Banafsha na ƙoƙarin shiga gidan, shi kuma Malam Abbo na ƙoƙarin fitowa, saura kaɗan su yi karo ya masta da sauri yana faɗin, "subhanallah! Sayyadata afuwa."

Ni kuwa baya nayi ban shiga cikin gidan ba, sai da na kalli ƙofan gidan su Umaima da gefen ido, na tabbatar Ya Danish na wajan kuma da alama idanuwansa a kai na suke, murmushi na sakarwa Malam Abbo na ce, "Ba komai Sayyadi."

Malam Abbo ƙara washe baki yayi ya fito gaba-ɗaya ya ce, "Sannu da dawowa Sayyadata, a je a huta nima bari na wuce gida daman na zo gaishe da Umma ne."

Murmushi na kuma yi na rausayar da kai na ce, "To nima a gaishe mini da su Umma."

Murmushi tayi cikin nisto a kogin ƙaunar Banafsha ya ce, "Za su ji" yana faɗa ya wuce yana sakin murmushi.

Ni kuwa sai da na kuma satan kallon ya Danish, sannan na ja staki na taɓe baki na shige gida da sallama.

Ya Danish tunda suka yi magana da Abbaa shikkenan ya kasa gane wa tunaninsa, yarinyar da yake da burin aure yanzu haka kawai ta fice masa a rai, tun da Abbaa ya masa magana in har zai yi tunanin matan aure to Banafsha ke faɗo masa a rai, ko weekend ɗin da bai zo last ba ma abinda ya hana shi zuwa kenan, zuciyansa ke dage masa akan tana son kallon Banafsha, amma shi sai yana yaƙi da hakan, wannan karon ya kasa haƙura shiyasa da sassafe ya baro Camaroon, dan isowansa bai jima ba aka yi sallahn juma'a, kuma tun da yayi sallahn la'asar yake zaune a ƙofa, zaman jiran yaushe su Banafsha za su dawo, a kan idonsa Malam Abbo ya shiga gidan su Banafsha, da yake kuma ya ganesa, tun da ya ga shigansa sai haushi ya rufe sa.

Haka dawowan su Banafsha ma a kan idonsa, tun da ya kalleta kuma ya ji wani irin yanayi mai kama da nustuwa ya lulluɓesa, kaman jinjirin da ya wuni bai samu nono ba sai yanzu, haka ya ji da ya ganta, duk da haka kokuwa yake da zuciyansa yana son ya ƙalubalanci wannan abun da yake ji a kan ta, amma bai tabbatar da ba zai iya hana zuciyansa wannan tunanin ba sai da ya ga murmushin da take yiwa wani daban ba shi ba, ji yayi ina ma shi take yi wa wannan murmushim.

Ya Danish kaman ya kamo Malam Abbo ya shaƙesa haka yake ji, har ya wuce abinsa, ajiyan zuciya Ya Danish ya sauƙe, a fili ya furta, "Allah kar ka ɗaura mini son yarinyar nan, ni da kai na nasan na ci mata mutunci, Allah idan ka jarrabeni da soyayyanta nasan wahala zan sha, Allah ka hanani son ta, ka sa ba son ta nake yi ba."

Ya IB da isowansa kenan, da mamaki yake kallon Danish ya ce, "Kai kuma tun ɗazu kana ta sumbatu kai kaɗai lafiya kuwa? Wacece ta taɓo ka haka da kake wannan addu'an Allah ya sa kada ka so ta, wacece za ta zarar mana da kai."

Hararan Ya IB yayi ya ce, "kai dai da son gulma kake kaman wani mace."

Murmushi Ya IB yayi ya ce, "Idan ta yi stami za mu ji, kuma dai in baka da labari ka sani yau, gulma ya jima da kauracewa mata ya koma kan maza, dan mata yanzu ba sa raya sa da kyau, gulma sai maza alaji je majalisa ka ga yanda ake baza hajar mutane kaman shinkafa da kaza a tire, Allah kyauta kawai, yanzu ma kamata yayi ace sheÉ—an ya fara storon maza ba iya mata ba."

Danish abinda ya damesa shi ne damuwansa, ko ta maganan Ya IB ba ya yi.

Banafsha na shiga gida ta samu Mami na É—age ruwan da ta kawo wa Malam Abbo, ganin Banafsha sai ta murmusa tare da amsa sallaman ta ce, "Æ´ammatan Mami an dawo."

Jinjina kai na nayi, ina murmushi na amsawa tare da gaishe da Mami, ta amsa, sai na ce, "Yanzu na haɗu da Malam Abbo ma a ƙofa."

"Eh! Daman nima nayi tunanin kun haÉ—u a waje ai" faÉ—in Mami tana zama.

"Mami wai gaishe ki ya zo yi in ji sa, haka ne?" Na faÉ—a ina rausayar da kai.

Mami dafe goshi tayi ta ce, "Allah shiryaki Banafsha, ki bari idan kin huta sai ki zo ki mini wannan tambayan, tun da shi da ya faÉ—a miki ba ki yarda ba."

Tura baki nayi na wuce É—akina, ni dai jikina bai bani gaishe da Mami kaÉ—ai ya zo yi ba, addu'a nake Allah ya sa ba maganana ya mata ba, kuma ko maganan nawa ne to ba zan yi aure ba inhar Mamina bata yi ba.

***
Ba zan baku haƙuri na rashin yawan page ba, saboda rashin sharhinku ya sa na yi sa kaɗan, ku ma ku ji idan da daɗi 😁

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

ƳAR KARUWA update group fan's, kowa da kowa uwar batoorl na ƙamnarku.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 71 _ 75

Sai da na wasta ruwa nayi sallah sannan na fito, samun Mami nayi tana zaune har yanzu, abinci ta saka ni na É—ibo na ci, har na ci na gama shiru Mami bata ce mini komai ba.
Chapter 42 · 0% Book details