Sashe 56
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amsa Mami tayi, tana jin kaman ta rungume Alhaji, amma tasan ba zai so haka ba dan yan da yake gudun abinda zai saɓawa Allah, ita kuma ba za ta masa abin da bai so ba, dan haka cewa tayi, "To ka zo mu karya rankashidaɗe."
Alhaji miƙewa yayi da murmushi ya bi bayan Mami, ni ma Mami ƙirana ta yi, duk muka karya, na godewa Alhaji sosai, amma ya nuna ba komai nima ƴar sa ce.
Mami kuwa kayan a Alhaji ya kawo mata, dogayen riguna ne na Egypt masu shegen kyau kusan kala biyar, sannan da wani haɗaɗɗen waya ta yayi Redmi, ga turaruka, ita ma har da sarƙanta na diamond, da takalma, sai kuma wasiƙan soyayya da ya jefa a ciki, Mami duk da ba wannan bane karo na farko da Alhaji ke mata kyauta, amma farinciki kaman ta yi kuka, musamman kalaman da yayi amfani da su a wasiƙan nasa.
Washe-gari Lahadi, muna zaune da Alhaji da Mami sai aka mana sallama, Alhaji ne ya fita ganin mai sallaman, gaisawa suka yi, da ya faɗa masa ya zo gaishe da Mami ne sai ya masa iso, tun da ya shigo nake kallonsa da mamaki, Ya Danish a cikin gidanmu, yau wace rana, amma sai na dake na miƙe na shige ɗakina ban ce masa ko sannu ba.
Mami cikin fara'a suka gaisa da Ya Danish, ya tambayi jikin Banafsha ta amsa masa da sauƙi, suka gaisa da Alhaji kuma, sannan ya ajiye ledan da ya kawo da kaya niƙi-niƙi na dubiya, sallama ya yiwa Mami ya tashi zai tafi, sai Mami ta ce, "Banafshan tana zuwa ko."
Ya Danish a waje ya staya jirana, ni kuma ina ɗakina kwance ina danne-danne a system na(🤣su Banafsha duniya sabuwa, ƴan gayu ƴan uwan masu nuƙud), Mami shigowa tayi da sallama, tun da na kalleta na tura baki dan nasan ba zai wuce ta ce naje ba, ai kam hakan ne kuwa, fiska a haɗe ta ce, "kin ga mutum kin tashi kin gudo ɗaki, ko gaisuwa babu kuma kin san wajanki ya zo ko, to maza kamun na ɓata miki rai ki tashi ki je waje yana jiranki, kuma idan kika amsa rashin kunya sai na saɓa miki, yarinya hankali sam-sam babu, wa ya faɗa miki ana wulaƙanta ɗan adam, maza tashi ki wuce", Mami na gama magana ta fice tana ƙwafa.
Ni kuwa tura baki nayi, sannan na miƙe, mayafi kawai na yafa na fice, fuuu! Haka na wuce su Mami a palour na yi waje, a cikin haraban gidan mu na tarar da shi, ƙara haɗe fiska nayi sannan na ƙarisa wajan da ya ke tsaye, ko kallonsa ban yi ba balle ya sa ran zan masa magana.
Ya Danish cikin damuwa ya ce, "dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mini, haka nan ki kulani Banafsha, wallahi da gaske nake son ki, kibar tunanin wani abu, idan kuskuren da na aikata rana ne ma wallahi ba da niya na yi ba, kuma ko da ace Abbaa ba su iso sun same mu haka ba wallahi ba zan iya ƙeta wa wata mutunci ba balle kuma ke, ki yi haƙuri."
Tsaki na ja na ce, "Dole ka ce ba da niya ba tun da dole aka saka ka, ka yage mini hijabi, ka haɗa jikinka da nawa, har da bakinmu ka haɗe, sannan a haka ka ce ba niya? Ka dai ji baiwa ne a jikin sai ka ga gwanda ka yaudareni ka aure ni ko, to bari kaji ko maza sun ƙare ba abinda zan yi da kai, ballema ina da wanda nake so, kuma kwanannan za ka ji an yi aurenmu."
Danish ji yayi kaman ta wasta masa ruwan zafi ne a zuciyarsa da wannan kalaman, kaman zai yi kuka ya ce, "Wallahi sharrin zuciya ne, saboda irin kalaman da kike faÉ—a mini.."
Saurin dakatar da shi nayi na ce, "nake faɗa maka ko kake jifana da su? Ko ka mance ka ce mini ƴar iska mai bin maza? Ko ka mance cewan da ka yi bana da abin da za ka taɓa? A haka ka yi kokarin ƙeta mini mutunci ka kuma zo yanzu da niyan aurena wai a faɗanka, duk ka mance abin da ka faɗa ne? Ta ina naga abinda za ka taɓa? Sannan ka ƙirani da mara tarbiya, shashasha ƴar iska, ka sanya hannunka a jikina kuma da sunan duka, ban da duk waɗannan ma abu mafi muni da na stana a duniya, sunan da bana son sa bana ƙaunarsa, sunan da yake ƙaddara ga rayuwata, ka ƙira ni da shi Danish, ƳAR KARUWA MARA TARBIYA, ka faɗa mini, sannan a haka kake tunanin na so ka har na aureka? To tabbas ka yi wa kanka ƙarya, dan na staneka! Na staneka! Na staneka! Bana ƙaunarka bana son ka, bana son kallonka, ko mai irin sunanka bana ƙauna, kai ka sa na stani maza na stani aure, amma Alhamdulillahi yanzu da nayi gwanina mai ilimi da sanin ya kamata to naji ina son aure kuma zan aure sa."
Ya Danish runste ido yayi kaman wan da aka kikkifawa mari, guiwansa ya saka a ƙasa ya ce, "Duk abinda kika faɗa ba sharri na faɗe su kuma na yi su, baki ƙara komai ba sai ma ragewa da kika yi, kuma nasan na yi ba dai-dai ba, ban kyauta ba, bayan haka uwata ta yiwa mahaifiyarki illa, dan Allah da Manzonsa ki yafe mini, dan darajan Annabi ki yafe mini, duk abin da na miki kuma idan ba ki manta ba, babu wanda baki rama ba a take ma kuwa, sannan ga shi Allah ya ɗaura mini soyayyanki, ki yi haƙuri Banafsha, ina sonki ina ƙaunanki dan Allah, ko da baki aure ni yanzu ba, zan zauna dakon jiranki har idan Allah ya sa ke rabona ce, to mijin zai bar mini ke ko kuwa zai mutu na aureki."
Jikinane yayi sanyi saboda yan da ya haɗa ni da Allah da Annabi, wan da ya halicce ni da kuma wan da aka halicci dubiya baki ɗaya saboda shi, Allah ya wuce komai ya wuce abin wasa, sannan kana ɗan Adam bai kamata a ce ka yi abu dan Allah ko Annabi ka ƙi yi ba, sannan na tuna maganan Mamina na ranan akan haƙuri, dan haka ajiyan zuciya na sauƙe tare da faɗin, "Na yafe maka duniya da lahira, komai kuma ya wuce, amma dai ka sani ina da wan da nake so, kuma in Allah ya yarda idan ya aure ni mutuwanma tare da shi zan yi", ina gama faɗan haka na juya na shige gida.
Ya Danish ajiyan zuciya ya sauƙe jin na yafe masa, sai ya ji wani abu mai nauyi ya sauƙa masa a zuciya, domin kuwa tun ranan da yayi ƙoƙarin ƙeta mata mutunci shikkenan abin yake damunsa, tun da yasan nan gaba shi ma uba zai zama.
Ni kuwa ina shiga gida na wuce É—akina, ko ta kan ledan da Mami ta nuna mini ban bi ba.
Alhaji dai ya kasa haƙuri sai da ya yiwa Mami magana Danish, faɗa masa komai ta yi bata ɓoye masa ba, har da akasin da suka samu da mahaifiyar sa, da kuma son ta da Abbaa ke yi, Alhaji ya ji kishi jin wani na son Mami har ga yaronsa ba son Banafsha, sai ya ji ina ma shi da yaronsa ne za su mallaki Mami da ƴar ta, amma dai Alhaji sai ya ɓoye bai nuna ba, addu'a yayi kawai da fatan alkairi.
Ya Danish a ranan da yamma-yamma ya koma wajan aikinsa, cike da É—imbin soyayyan Banafsha, musamman ma da ta ce ta yafe masa.
Bayan sallahn isha'i kuma sai ga Malam Abbo, Alhaji da yake ya sheda sa shi kam, gaisawa suka yi, suka gaisa da Mami sannan suka bamu waje, sai da na ɗan shafa kwalli da man baki sannan na fito, cikin fara'a muka gaisa da Malam Abbo, nan ya fara baza hajar soyayyansa yanda ya saba, kalamai masu shiga jini da jijiya, su tsaga ƙashi da ɓargo su kai maka har ƙwaƙwalwanka, gaskiya wan da ya ce ustazai ba su iya soyayya ba sai wa'azi to gaskiya yayi kuskuren fahimta, gaba-ɗaya Malam Abbo idan yana kalamansa tafiya yake da tunanina.
Malam Abbo ya jima sannan ya mini sallama ya tafi, ni kuwa na shige É—akina cikin dimbin tunanin Malam Abbo da soyayyar sa da nake ji yana kama ni.
Washe-gari Litinin, Alhaji sai da ya ajiye ni a makaranta sannan ya wuce zai koma gidansa, wannan karon bai jima ba saboda yana da shungulla, ina makaranta Malam Abbo ya zo suka gaisa da Mami ya faɗa mata batun tafiyanmu Yola musabaƙa, Mami ta yarje ba komai bayan ta musu addu'an nasara, da kuma roƙon a kula musu da yara, kada a ci amanan iyayen yara a ɓata musu tarbiyya.
Bayan na dawo makaranta, Mami ta faÉ—a mini, sai lokacin ma na tuna nikam, na faÉ—a mata ai muma an faÉ—a mana na sha'afa ne, murmushi kawai Mami ta yi ta ce, "je ki wasta ruwa ki ci abinci, idan kun dawo makaranta zuwa anjima za mu yi magana ko."
Amsawa nayi na miƙe n shige ɗakina, ruwa na watsa sannan na ci abinci na yi sallah, shirin tahfiz kuma na yi, sallama na yiwa Mami na fice muka tafi tare da Umaimata.
Bayan mun je mun dawo, zuwa dare muna zaune da Mamina ta dubeni ta ce, "Banafsha!"
Da murmushi a fiskana na ce, "na'am Mamina."