← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 58

Sashe 1

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

𝗕𝗜𝗦𝗠𝗜𝗟𝗟𝗔𝗛𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗠𝗔𝗡𝗜𝗥 𝗥𝗔𝗛𝗘𝗘𝗠

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

Ina mai godiya ga Allah da ya bani iko da daman fara wannan sabon littafin nawa mai suna 'YAR KARUWA, Allah sa mu kammala lafiya, duk abinda ya ke ba dai-dai ba a ciki Allah ya yafemu duka, ni mai rubutawa da ku masu karatu, FAN'S ina matuƙar ƙamnarku, Uwar batoorl na mugun yinku irin sosai ɗin nan, masu daraja habibties.🥰

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NA FARKO DA KU ZAN FARA KAMAN YANDA NA YI ALƘAWARI.

Masoyiya Bealkysou
Ummu Adeel tawan

🅿️ 1 _ 5

Matashiyar yarinya ce zuƙeƙiya fara, farinta dai-dai, 'yar kimanin shekaru 20 da haihuwa, durƙushe take akan guiwowinta ta yi kneel-down a gaban wata mata wacce ko ba'a faɗa ba kasan mahaifiyarta ce duba da kaman da suke yi da kuma maganganun da matashiyar budurwan ke yi.

Cikin tsananin kuka mai nuni da stagwaran taƙaici da kuma tsaban damuwan da take ke ciki ta ce, "Haba Mami na, Mami dan Allah dan Annabi ba dan ni ba, kuma ba dan halina ba ki bar wannan rayuwa, Mami kina zubar da mutuncin kanki kina zubar da na 'yar ki, Mami da girmanki kina rayuwa irin ta yara ƙanana marassa tunani ko mafaɗi, Mami ke fa ya kamata ki stawatar mini idan kinga ina ƙoƙarin sanya kai na a irin wannan lalatacciyar rayuwan, amma fa Mami ke da kanki kike yi ba ma ni ɗin ba, haba Mami na ina iliminki da tunaninki kika zaɓa mana wannan rayuwa irin ta jahilai...."

Maganan dake baki na ne ya maƙale a maƙoshi na, sakamakon wani azababben marin da Mami na ta kifa mini, miƙewa tayi tsaye tana huci ranta a ɓace kaman ko da yaushe idan hakan ya faru tsakaninmu, idanuwanta ta zuba mini tare da cewa, "BANAFSHA har rashin kunyar ki da fistaranki sun kai haka? Ina mahaifiyarki kina sokamun baƙaƙen magana, ni kike faɗawa ina rayuwa irin ta jahilai? Ni kike ƙira jahila Banafsha? Irin tarbiyyan da na miki kenan ki nunawa duniya ni ma kin renani balle wasu? Banafsha ni kike faɗa wa haka?" Mami ta ƙarishe maganan cikin stananin ɓacin ran da har idonta na ƙoƙarin sauya kala.

Cikin kukan da ya zamo mini jiki dan in da sabo na saba, sai na ce, "Allah ya huci zuciyanki Mami na, amma wuyana bai yi ƙwarin da zai sa nayi suɓutan harshe a kan mahaifiya ta ba, koma menene ke ɗin uwa ce a gare ni kuma ko ya kike ke mahaifiyata ce, amma ina mai haɗa ki da Allah da Manzon sa Mami kiji tausayin rayuwata kibar wannan lalatacciyar rayuwan, munanan maganganun da mutane ke jifa na da shi tun baya damuna har ya fara mini ciwo, Mamina dan Allah kiji tausayin maraici na ki daina wannan rayuwan ko dan ni Mami, wallahi duk inda naje suna ɗaya ake qira na da shi manya da yara, duk inda na wuce sai ace ga 'YAR KARUWA! Mami tun ana faɗa a ɓoye har takai mutum zai staya a gabana ya ce mini hakan kuma ba ni da yacce zan yi, dan girman Allah Mami kiji tausayi na kibar wannan rayuwa mai cike da kunyan duniya da lahira, Mami ki tuna fa akwai mutuwa fa, kuma ba mu san yaushe, a ina, a wanne hali, ta yaya za ta riske mu ba, dan Allah Mamina ki daina kinji" na ƙarishe maganana cikin sigan tausayi ina share hawaye mai ɗumin gaske da ke bin kunci na.

Mamina zama tayi ta dubeni tare da cewa, "Maganar da nake faɗa miki a kullum ita ce zan ci-gaba da faɗa miki Banafsha, ni ba karuwanci nake yi ba sana'a nake yi, wanda kuma da wannan sana'a na siya gida na kai ki makaranta, cinki, shanki, suturanki, maganinki, da komai naki har kika kawo i zuwa yanzu da kuɗin sana'ar nan nake miki, me yasa kema za ki bi ta faɗin jama'a ba za ki fahimci mahaifiyarki ba? In na zauna bana komai kina ga akwai mai kula da mu? Akwai mai ɗaukan nauyin karantunki, cinki ko shanki ko suturanki? Ko da ace aikatau muka je gidan mutane to tabbas nasan za'a nemi lalata mini ke ko wulaƙanta mu, wanda ni kuma ba zan jure hakan ba, akan abu ya same ki gwanda ko duniya ne su taru a kaina su ce komai ma sannan sunan da ake ce miki 'YAR KARUWA ya bar damunki in baki fahimci mahaifiyarki ba babu mai fahimtarta Banafsha, ki dubi rayuwan yanzu da idon basira da kyau, ko bara na ce zan yi dan na kula da ke to fa tabbas za'a nemi lalata miki rayuwa ko kuma ni ɗin, Banafsha duk da ke yarinya ce, amma a wannan shekarun naki ya kamata ki fahimci rayuwa da kyau."

Kallon Mamina nayi da idanuwana da kullum cikin zubar hawaye suke na ce, "Wallahil Azeem Mami na gwammaci muyi rayuwan aikatau akan irin wannan rayuwa, na kuma zaɓi muyi rayuwan bara akan wannan rayuwa, Mamina gwanda na zama 'yar talla mu yi sana'anmu ko na rufawa kai asiri ne ya fi mini akan wannan rayuwan, sannan lalata rayuwata ba wanda yake da ikon hakan in har Allah bai ƙaddara hakan ba to babu wanda ya isa tunda kina min addu'a, kuma Allah zai kare ni dan addu'an bakin mahaifiya ba a maida shi, dan Allah Mamina ki daina, wallahi Mami akwai mutane na gari da yawa a rayuwa masu yi dan Allah ba tare da zalunci ba, nifa Mami ko baran kika turani zanyi na nemo mana abinda za muci karatu ko wani sutura na haƙura da su, mutuncinki da nawa su ne abun da nafi buƙata, wannan suna da ake faɗa mini yana sa zuciyata tana mini zafi sosai-sosai Mamina, dan Allah inma ba za mu yi wani aikin ba mubar garin nan mu koma wajan 'yan uwanki ko na mahaifi na ne kinji.....", wannan karon ba mari ne ya maƙalar da sauran maganan dake baki na ba domin kuwa Mamina rufe ni tayi da duka ko ta ina kaman an aiko ta, da ƙyar aka shigo aka karɓe ni.

Maman ƙawata Umaima ce ta shigo ta karɓe ni ta riƙe hannuna muka tafi gidanta wanda ya ke gidan su babbar ƙawata kuma Aminiyata wacce banda kamarta.

Matar da ta shigo ta karɓeni wacce muke ƙira da Ummu, kallona tayi ta ce "BANAFSHA wai me yasa kike son yawan yin sa'insa da Maminki ne da har yake kai da ga miki irin wannan dukan ne? Yanzu ba dan Allah yayi fitowa na ba kin san halinta za ta iya miki rauni, Banafsha kin girma fa yanzu ba da bane kin zama budurwa duka bai kama ce ki ba kiwa mahaifiyarki biyayya ki kuma yi haƙuri komai zai wuce kiyi ta addu'a."

Cikin tsananin kuka da ciwon da jikina ke mun na dukan da Mamina ta mini ina sheshsheqa da muryana da ta fara dishewa na ce, "Um..mu yaa..yaa.. yaya zan.. yi? Ummu, Maa..mi na, Ummu me yasa sai ni? Wan.....nann ra..yuwa..n akwai...ciwo mahaifiyar mutum ta dinga kule-kulen mazaje daban-daban, Ummu kiji fa sunan da ake qira na da shi a anguwan nan 'YAR KARUWA! Ummu hakan akwai daɗi? Ummu ya zanyi da rayuwa ta? Ya ake so nayi? ina ake son na saka kai na? Ko sai na mutu kowa hankalinsa zai kwanta?" Na faɗa ina ƙara fashewa da mastanancin kukan da zuwa yanzu sautin ma ba ya fita.

Ummu kallona tayi cikin sigan rarràshi ta ce, "komai na duniya mai wucewa ne Banafsha, ke dai ki ci-gaba da addu'an Allah ya kawo miki miji na gari kiyi aurenki wanda nake fata zuwa wannan lokacin Allah yasa komai ya wuce."

Cikin kuka na ce, "Ummu wa zai yi aure? Wa zai aure ni? Ina 'YAR KARUWA wa zai auri yarinyar da uwarta ke lalatacciyar rayuwa? A'a Ummu karki faɗa min abinda ni da kai na nasan ba zai taɓa faruwa ba, kuma nima ba zan yaudari kai na ba, nasani ni da aure har na mutu sai dai a lahira idan ana yi, zan zauna da Mamina na dinga addu'an Allah gyara mana rayuwanmu ya shirya min uwata, amma ba zan taɓa yin aure ba dan nasan ba mai aure na, kuma ko an aure ni za'a goranta mini."

Ummu murmushi tayi wanda hakan ya ɗan sauƙaƙa mini abinda ke damuna a zuciyata, dan sosai nake jin Ummu a rai tamkar mahaifiya ta, Ummu ta ce, "Banafsha ki rubuta ki ajiye ni Ummul-khultum na ce za kiyi aure in Allah ya yarda, kuma aure ne irin wanda ba ko wacce yarinya ke dacen yi ba sai wacce Allah ya ƙaddarawa hakan, za kiyi aure in Allah ya yarda wanda mijinki na tabbata zai sanya ki mance kin ma taɓa shiga wannan halin quncin rayuwa, duk bawan da ƙaddara ta stananta a rayuwarsa to tabbas gaba kaɗan idan da rayuwa zai riske alkairi mara misaltuwa, to ina so kema ki ɗauka hakan, duk da akan jarabawan rayuwa da wani ke ciki to naki ba komai bane, kuma bawan da Allah ke jarraba shi Allah ke so, kibar wannan tunanin in Allah ya yarda za ki yi aure."

Kallon Ummu nayi idanuwana har yanzun da burbushin ƙwalla na ce, "Ummu nasan da haka, amma babu mai aure na ina 'YAR KARUWA! sannan ko da nayi auren to Ummu tabbas wulaƙantaccen rayuwa zan yi dan kuwa zan zama tamkar mujiya ko saniyar ware yacce ake nuni dani yanzu haka can ma za'a yi, za'a dinga gorantamini a ce ni Ƴar karuwa ce a dinga wulaƙantani, Ummu ni ko kaɗan ma bana ƙaunar maza, Ummu na tsani maza gani nake kowa irin halin sa kenan bin mata."

Cigaba da rarrashina Ummu tayi har
Ƙawata Umaima ta shigo ta same mu a haka, ganina kawai da tayi ta fahimci me ke faruwa dan ta sani tabbas labarin gizo baya wuce na ƙoƙi, dan kusan aikin kenan kullum ni da Mamina, idan ba'a yi da safe ba za'a yi da yamma.
Chapter 1 · 0% Book details