← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake Mami ta kan shigo gidan sa'i da lokaci idan irin haka ta faru, kuma ta san ɗakin da nake zama idan na shigo, sai ta wuce ɗakin da muke, da sallama ta shigo, Umaima ce ta amsa da ƙarfi, amma ni ciki-ciki na amsa kuma ba tare da na buɗe idanuwana ba, Mami ganina a kwance bata kawo komai a ranta ba ta murmusa tare da ƙarasowa bakin gadon, sai da ta amsa gaisuwan da Umaima ke mata sannan ta ce, "boɗɗin Maminta taso mu tafi ko."

A hankali na buɗe idanuwana da suka kumbura ga kuma hawaye kwance a cikinsu na zubawa Mamina su, ban ce komai ba kuma ban mosta ba dan bana jin zan iya tashuwa balle tafiya, Mamina tana kallon yanayi na ta shiga damuwa dan bata san banda lafiya ba ne, a rikice ta zauna bakin gadon ta taɓa jikina, da yake zuwa lokacin zazzaɓin ya sauƙa, to zafin jikin ba sosai ba, amma duk da haka da ɗumi, Mamina duk ta bi ta rikice, kaman za tayi kuka ta ce, "boɗɗi me ke damunki?"

Nan ma shiru nayi ban ce komai ba, Mamina cikin damuwa ta ce, "Banafsha ki daina saka abu a ranki, ki saki ranki mamana, ki dinga taya ni da addu'a kawai dan wani abin nima ba da son raina nake yi ba, tashi muje gida kiyi wanka."

Yanzunma dai ban ce komai ba sai ƙoƙarin miƙewa da nayi ina runste idanuwana dan har yanzu kai na yana mugun sara mini, amma tunda Mami ta ce mu tafi ba zan iya mata musu ba dan Allah ma ya gani ina ƙaunar mahaifiyata ina son mahaifiyata fiye da yacce nake son kai na, duk wani mafarki na da buri na ita ce ba wanda na sani sai ita ba wanda ido na ya taɓa gani da za'a nuna ace ɗan uwanane ko wani nawa sai ita, ita kaɗai gare ni shiyasa bana haɗa soyayyan da nake mata da na kowa.

Miƙewa nayi amma ganin jiri na neman yasar da ni sai Mamina ta hau da ni bayanta kasancewar ba wani nauyi ne da ni ba duk da dai in ka ganni za ka ɗauka nafi shekaruna, ko na kai irin ishirin da ɗori hakannan.

Fitowa muka yi a ɗakin ina bayan Mami na lafe abuna, Ummu ganin mu sai ta girgiza kai tare da yin murmushi ta ce "Yau kuma taɓaran Banafsha ya tashi, har goyo ya kai a mata, ah lallai ƴar gidan Mami jin daɗi ya zauna miki."

Umaima tana murmushi ta ce "Nima Mami biyo ki zan yi a goya ni nima dan masoyiya ta fini nauyi ma."

Mamina murmushi tayi wanda ako da yaushe yake zama makari sannan sirri na kyau da Allah ya mata, dan in ka kalli Mamina za ka ranste balarabiya ce ko bafulatana amma kuma duk ba abinda ya haɗa mu da yare biyun, bayan su Ummu sun gama zolayansu Mami ta fice da ni a bayanta tana murmushi muka yi gidanmu, kasancewan ba nisa tsakanin gidanmu da na su ƙawata Umaima.

Jahar Adamawa a ƙaramar hukumar Mubi anguwan Kwaccam, nan ne anguwan mu, anguwa ne na masu saka ido da kuma damuwa da rayuwar da bata shafe su ba, mutane masu kiwon mutum ba dabba ba, komai aka yi idanuwansu na kai, ɗan madai-daicin gidanmu flat ne mai ɗauke da center palour sai kuma ɗakuna guda uku wanda ko wanne akwai banɗaki a ciki sannan daga gefe akwai kitchen, ba abinda Mamina bata saka mana ba na more rayuwa a gidan, dai-dai buƙatan talaka mai rufin asiri, wanda in ka samu irin sa dole ka ce Alhamdulillahi! dan kuwa wani ko kwatan-kwatansa nema yake bai samu ba, a filin gidan namu akwai kitchen a waje sannan da banɗaki, gidan bashi da wani faɗi sosai kuma ciki duka interlock ne.

Har É—akin da yake nawa Mami na ta kai ni ta kwantar da ni a kan madai-daicin gadona, juyawa tayi ta fice a É—akin sai can ta dawo da abinci a plate da ruwa a cup da kuma magani.

ÆŠagani tayi ta zaunar da ni tana jero mini sannu ta ce, "FAÆŠIMAH tashi ki ci abinci ki samu kisha magani, kinji ko Æ´ar albarka ta Maminta."

Miƙewa nayi na zauna tare da zuba wa Mami idanuwana, kallon mahaifiyata nake yi ina mai jin ƙaunanta na ƙaruwa a raina yana tsigar mini a ko wani sassa na zuciyata, ina jin ina ma muyi rayuwanmu mu biyunmu a haka ba tare da wasu sun shigo ciki ba, ina jin ina ma shikkenan Mamina ta daina wannan rayuwan, mu zauna haka abunmu ta kula da ni nima na kula da ita, amma sai dai kashh! nasan hakan ba mai yiwuwa bane, tana ƙaunata tana tausayina amma wannan rayuwa ya zamo ƙaddara a garemu ni da ita, kuma amsa sunan 'YAR KARUWA ƙaddara na ne, sai dai na yi haƙuri na karɓe sa da hannu bibbiyu.

A baki take bani abincin ina ci kaman zan yi kuka, saboda a rayuwata ni bana ƙaunar cin abinci wanda ta wannan dalili ne har ulcer yayi nasaran mini mugun kamu, amma a haka Mami ta cigaba da bani har na kawar da kai na ƙoshi, sannan ta ɗau magani ta ɓare ta miƙo mini, nan fa gizo ke saƙar dan kuwa wannan ga'bar ita ce daru, nan na fara hawaye ina kuka ina girgiza kai banason sha.

Kallona Mami tayi cikin lallashi da ta saba min a duk lokacin da zata ban magani ta ce, "Haba Sayyada Faɗimah shugabar mata, Nana Faɗimah, Fatima Bintu, batooler, Faɗimatu zahra'u, Sadiƙa, yarinyar kirki jaruma, da girmanki ai sai dai magani ya ji storonki, takwara ga ɗiyar ma'aiki SAW, yi haquri kibar kukan ki karɓa kinji zan baki abu mai daɗi."

Ina kukan ina yarfe hannu na karɓa na sha, ajiyan zuciya na dinga jerowa kamun na koma na kwanta amma Mami ta tashe ni wai na wasta ruwa, langwaɓe kai nayi cikin shagwaɓa na ce, "Mami nikam ba zan iya ba sai anjima."

Kallona tayi ta murmusa sannan ta É—aga ni ta fara cire min kayan jiki na, tana gamawa ta É—aura min towel tana cewa, "Yanzu Banafsha da girmanki kike so ki ce sai na miki wanka, kin fa zama budurwa yanzu, shekaru ishirin 20 ba wasa ba, ko in na aurar da ke haka zaki sa surki na sai ya dinga miki wanka kullum kaman bai da aikin yi?"

Tura baki nayi idanuna har ya kawo ƙwalla dan maganan da tayi na ce, "Mami ni ki bari bana so, ba ruwana da maganan nan, kuma ba ruwa na da namiji balle aure."

Mami ajiyan zuciya ta sauƙe kamun ta zauna tana kallona cikin yanayi na muhimmin magana za ta yi, sai ta ce, "Banafsha, na hane ki wannan magana, banda abinda ya ragemun a rayuwata a yanzu sai ganin na aurar da ke, domin kuwa aure shine mutunci ko wacce ɗiya mace kuma buri ga iyayenta suga sun miƙata gidan miji lafiya cikin mutunci, in Allah ya yarda mijin da zai auri Banafshan Mami sai ya kasance mai matuƙar sa'a, wanda ba shi da stara, in Allah ya yarda za ki rayu a gidan mijinki rayuwa ta matar Sarki."

Wannan magana da Mamina tayi ba ƙaramin fama min ciwon dake zuciyata yayi ba, kuka ne ya ƙwace mun ba tare da nayi niyan kukan ba, cikin kukan na ce, "Mami ashe mutuncin ko wacce ɗiya mace aure ne? Mamina kinsan da hakan amma me yasa kika take sanin? Mami kema fa kina da iyayen amma me yasa ke ba zaki cika musu nasu burin ba ki riƙe mutuncinki, sannan kuma ki zauna a gidan miji, meyasa Mamina? Meyasa kika zaɓar mana wannan rayuwa? Why Mami?" Na ƙarishe maganan cikin matsanancin kuka mai cin rai."

Miƙewa Mamina tayi ranta a matuƙar ɓace, wanda na tabbatar rashin lafiyan dake damu na shine kawai ya cece ni daga samun sadakan mari ko kuwa duka daga Mami, a fusace ta nuna ni da yasta cikin fushi da ɗaga murya ta ce, "Banafsha, kar ki yarda ki tunzura ni har ɓacin rai yasa na miki baki."

Kallon Mamina nayi ina kan kuka na ce, "Mami wallahi ko kin stine mini ba zai taɓa kama ni ba har abada in dai akan wannan maganan ne, domin Allah ya faɗa ba ya kama bawansa da laifin da bai aikata ba, Allah ba azzalumi bane, sannan Allah ya sani gaskiya ce kuma Allah da kansa ya ce ko iyayenmu ke yin ba dai-dai ba mu faɗa musu gaskiya komin ɗacinta, dan Allah Mamina kiyi haƙuri gaskiya ce na faɗa, amma in har na ɓata miki rai to ki yafe ni, kada kiyi fushi da ni, Allah huci zuciyanki Mamina."

"Tashi kije ki wasta ruwa kuma kina fitowa ki tabbatar kin yi sallah kamun ki kwanta" Mami na gama faÉ—an haka ta fice a É—akin.

Tashuwa nayi na shiga banɗaki ina cike da tunani dan zuwa wannan lokaci idanuwana sun kafe ba hawaye, kukan yau kuma ya tsaya sai kuma na gobe, dan wannan wani abu ne gare ni da kullum shine sana'a ta kuma ƙalubale na, ba ranar da gari zai waye har rana ya faɗi ban yi kuka akan halin Mamina ba ko wani abun idan ta mini.
Chapter 3 · 0% Book details