Sashe 44
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙara tamke fiska Mami tayi ta ce, "Kinsan bana wasa da ke ko? To maza ina sauraranki faɗa mini abinda na tambayeki."
Tura baki nayi cikin shagwaɓa na ce, "cewa yayi yana so na zai aure ni" ina faɗan haka sai nayi shiru.
"Da ya faÉ—a miki hakan, sai ke kuma kika ce masa me?" Mami ta tambaya tana jefa mini mugun kallo.
Kaman zan yi kuka na ce, "Mami Allah gaskiya na faÉ—a masa, ya ce yana so na zai aure ni, sai ni kuma na faÉ—a masa gaskiya ba aure zan yi ba, ai gaskiya ce Mami, ni ba zan yi aure ba, tun yanzu ana mayar da ni saniyar ware akan jarabawan da Allah ya mini, idan nayi aure dangin miji da miji su dinga gallazawa rayuwata kenan su ma.."
Wani mugun stawan da Mami ta buga mini, shi ya sanya ni yin shiru na haɗiye sauran maganata, cikin tsawa ta ce, "Idan ba ki yi aure ba dan ƙaniyanki me za ki yi? Banafsha ki fita a idona na rufe, kada ki bari rai na ya ɓaci fa zan saɓa miki, idan ba ki yi auren ba so kike na saka ki a gaba kaman television ina kallonki ko kuwa na kwaɗaki a tire kaman kwaɗo na cinye? To ki mai da hankalinki."
Tura baki nayi, ciki-ciki na ce, "Ni dai ba auren da zan yi, haka kawai a dinga ce mini Æ´ar mace, a ce mini Æ´ar karuwa, ni rayuwata gaba-É—aya ba wani farin ciki kenan."
Mami ta ce, "Banafsha kinsan Allah zan saɓa miki a kan wannan maganan, ke baki san cewa Allah ma da kansa yana tausayawa duk budurwa ko saurayin da suka mutu ba aure, kuma sun kai yin auren ba, idan ba ki yi auren ba me za ki yi? Me damuwanki da maganan mutane? Banason shashanci da rashin hankalinkin nan."
Tura baki nayi na ce, "Ni dai ba wani auren da zan yi, aka masta mini kuma shikkenan sai na shiga duniya, daman gado ba karambani ba."
Ranƙwashi Mami ta mini mai kyau ma kuwa, sannan ta ce, "To zan gani cikinmu wa ya isa da wani, tun da har kin yi girman da ina faɗa kina faɗa, kuma ki tabbatar Inshà Allah tun yanzu za ki fara shirin aure, muddin ya ce yanzu za'a yi auren, to ko bokon ma stayar da ita za'a yi, aure zan miki."
Kuka kawai na saka ina bubbuga ƙafa, cewa nake, "nidai ba auren da zan yi sai an kai ni wajan dangin babana, su za su aurar da ni, kawai in ana so naji magana nayi biyayya a kai ni wajan dangin babana, ai ba'a jikin bishiya aka ɓanɓaro ni ba, nidai dangin babana."
Mami ikon Allah ta staya gani, saboda Banafsha dagewa tayi ita sai dangin babanta za'a kai ta sannan ya yarda ta yi aure, numfasawa Mami tayi ta ce, "Banafsha ko kina so ko bakya so za ki yi aure Insha Allah, indai ni ce mahaifiyarki kuma na isa da ke, dangin ubanki kuma kibar maganansu idan ba haka ba zan saɓa miki, zan yi shawara da wanda ya kamata a je neman aurenki wajansa, ke kuma ki saurari Malam Aliyu, idan ba haka ba ni da ke ne, sai na niƙa ki a gidan nan."
Tura baki nayi na ce, "nidai ko dole za'a mini to a haɗa ni da dangin ubana tukunna, sai an mini abinda nake so sai na yarda, kuma idan ba haka ba sai dai ke ma Mami ki yi haƙuri ki yi abinda kike so nayi."
Mami wani kallo ta aika mini da shi ta ce, "tashi ki bani waje kamun na karyaki, ai kin girma yanzu wuyanki ya kai yanka, duk maganan da kike so faÉ—a mini kike yi."
Miƙewa nayi sumui-sumui na wuce ɗakina, ina shiga na saki murmushi, domin ni ko kaɗan maganan auren Malam Abbo ba baƙin ciki ba ne gare ni, maganan auren Malam Abbo alkairi ne gare ni, domin da wannan batu zan yi ƙoƙari wajan gani lamuran Mamina sun saitu, alhamdulillahi! Daman Allah subhanahu wata'ala ya ce, FA'INNA MA'AL USRI YUSRAH, duk wani tsanani na tare da sauƙi, to yanzu ina ganin na fara tinkaro stanin sauƙi da kuma farin ciki na rayuwata, a haka ina zancen-zuci ina murmushi ban ankare ba, har ɓarawon bacci yayi gaba da ni.
Washegari Lahadi muka je makaranta safe da yamma duka tare da Umaima muka dawo, kuma duk ya Danish na nan yana kallonmu bai ce mata komai ba, ni kuma ko gigin shiga gidan su ban yi ba dan bana ko ƙaunar kallonsa balle haɗa inuwa da shi, stakanina da Mamina kuma bata ƙara mini maganan Malam Abbo ba, illa iyaka da ta ce mini na sauraresa.
Wannan karon Ya Danish bai koma ba har sai washegari Litinin, a hakan ma wai dan Umma tana surutun bata gane ma abinda ke damunsa shiyasa ya shirya zai koma, dai-dai lokacin da muka fito tafiya College shi ma ya fito, ni da Umaima tafiyanmu muka yi za ku nemi mashine, amma sai ya tsaya a gabanmu ba tare da ya juyo ya kalle mu ba ya ce, "ku shigo."
Kallon sama da ƙasa na yi wa motar sannan na kawar da kai, Umaima jin ya ƙara magana sai ta riƙo hannuna ta ce, "masoyiya ki yi haƙuri mu shiga ya sauƙe mu."
Hararanta nayi ban ce komai ba, na sake hannunta na yi gaba, Umaima kaman za ta yi kuka, ta kalli Ya Danish ta kalleni, Ya Danish kwallon Umaima yayi tare da yin ƙwafa ya ce, "Sai ku taka da ƙafanku ai" yana gama faɗa yayi gaba da mugun gudu, yana wuce inda nake na ja staki tare da hararansa shi da motan nasa.
Umaima da ɗan sauri ta iskoni tana faɗin, "Masoyiya mu godewa Allah yanzu ya sha nistojin ya daina bala'i, idan ba haka ba ai da tuni ya shuka mana, ke ma me ya sa za ki ƙi shiga?"
Hararan Umaima nayi na ce, "banason magana ki ƙyale ni, tun da dai naga ban hanaki shiga ba ke da motan yayanki, aikin banza aikin wofi, kina wani cewa na shiga sai ka ce baki san irin abinda yake mini ba, ko da ya ke ba laifinki ba ne, daman aka ce naka sai naka, ni bare ce stakaninku."
Umaima dariya tayi sosai ta ce, "rai na bai ɓaci ba sai ki fama, anji ɗin ke bare ce, mutum sai ka ce kububuwa, rashin kirkin naki yau ni za ki yi wa kenan? To Allah huci zuciyanki."
Hararanta nayi na ce, "oho muku ke da yayanki, kuma dan ki ji mun ɓata ma kowa yayi hanyansa."
Murmushi Umaima ta yi ta ce, "Daman wallahi kaman kin san zaman lafiyanmu yayi yawa, ana ƙawance ana ɓatawa ya fi daɗi da ƙargo, amma kullum ni baki haƙuri, ke kuma yin haƙuri, ya kamata ai ko casuwa mu dinga yi, ko da yake ai ma Ummu ta ce mun yi dambe da muke yara, amma ni nake saka ki kuka."
Dariya maganan Umaima ya bani, dan haka na dara muka tari mashine muka wuce makarantar, muna zuwa muka ci karo da kyakkyawan labari, an manna dodon bango, Umaima ta damu mu je mu gani, amma na ce ta bari ba yanzu ba, tasan yanda muke Æ´an sturut É—in nan sai a maste mu ko a cika mana ciki da warin hammata, ga kuma wani na stamin zafin da ake yi.
Sai da aka tashi sannan muka samu ganin result namu, amma duk da haka ba mu muka duba ba, dan duba mana aka yi, alhamdulillahi dukkanmu result yayi kyau yanda ake so Masha Allah.
Muna komawa kowa yayi gidansu, da farin ciki na faÉ—awa Mami, har da É—agani Mami tayi dan farin ciki, saboda result yayi yanda ake so, sai godiya ga Allah.
Haka muka cinye wannan satin ma cikin farin cikin kyawun result namu, sannan a hadda an fara bitan karatun musabaƙan da za mu yi a cikin jimeta da sauran makarantu na local government's ɗin Adamawa State, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ina sauraransa amma dai bana sake jiki da shi sosai, dan har yanzu ina kan bakana kar abu ta kwaɓe gaba ya ce na cutar da zuciyarsa ko kuma na yaudaresa, akwai abu guda da ke burgeni da Malam Abbo, sam-sam a makaranta baya nuna ma akwai wani alaƙa na daban stakaninmu, Malami da ɗalibarsa kaman baya haka muke, kuma ba ya zuwa zance sai ranan Lahadi ko kuma Alhamis, da yake ba mu zuwa makaranta ran Alhamis, sam-sam ba ya takura mini, tun da ba ni da waya, ta nan ɓangaren ma ba ya takura mini.
Tun da na fara sauraran Malam Abbo, sai kuma wani shaƙuwan ta shiga tsakanimu, mastayinsa da kiman da nake basa kullum ƙaruwa yake yi, Malam Abbo ya iya soyayya yan da ko wacce mace za ta buƙata, kuma yana ƙoƙarin mini nasiha da tunatar da ni rayuwa, alhamdulillahi sai fatan alkairi stakaninmu.
Har aka cinye wannan hutun ƙarshen makon Ya Danish bai zo weekend ba, muka shiga wani satin wanda a wannan weekend ɗin wa'adin da Abbaa ya ba su zai cika, da kuma wa'adin da ya bai wa Mamina na ta yi tunani, har juma'a ta yi ba Ya Danish ba alamansa, dan haka Abbaa waya ya ɗaga ya ƙirasa, sai da ya sollesa tass sannan ya faɗa masa ya zo ko ransa yayi mugun ɓacuwa, ba shiri ya Danish ya shirya ya kamo hanyan zuwa.
Da ya ke Umaima ta yi zazzaɓi kwana biyu, sai Mami ta shirya da yamma bayan an yi la'asar ta shiga gidan su Ummu, da sallama ta shigo gidan, ta samu Ummu zaune a palour tare da Ya Farooq, cikin fara'a ya Farooq ya gaishe da Mami ta amsa, sannan suka gaisa da Ummu, tana murmushi ta ce, "Mamin yara sai yau aka samu daman leƙo gidan namu."
Murmushi Mami ma tayi ta ce, "ai gidan naku ne yana neman fin ƙarfin shiga na, yanzu ma dai yarinyata na zo dubawa da jiki shiyasa."
Dariya Ummu ta yi ta ce, "Mu da muke addu'an a shigo din-din-din, ina wanda ya isa ya ce ba za ki shigo ba."