← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 58

Sashe 21

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momsee ganin Bunayd na ƙoƙarin yin bacci sai tayi murmushi ta ce, "To muje a ci abinci dama kai muke jira."

Duk miƙewa suka yi suka sauƙo dinning na ƙasa, kowa ya samu waje ya zauna, yaran mata ne guda uku suka fito, kyawawa da su masu kama da General, kuma daman Bunayd da General yake kama shi ma, ɗaya a cikinsu ba za ta haura shekara sha tara ba 19 mai suna Ramla, sai ɗaya ba za ta haura 17 ba ita kuma sunanta Suhaila, sai kuma autar cikinsu da ba za ta haura 14 ba mai suna Nabeela, duk a niste suka gaishe da Bunayd ya amsa fiskan nan a sake yana musu murmushi, General ne yayi magana ya ce, "table manners, kowa ya ci abinci ayi shiru."

Duk stitt suka yi baka jin ƙaran komai, sai na spoon da plate da suke karo, yayin da CAS Bunayd kuwa rabin hankalinsa ke kan wayansa yana sakin murmushi.

⭐⭐
Banafsha suna dawowa daga wajan musabaƙa aka sallami kowa ya koma gida bayan an ƙara ƙarfafa musu guiwa su dage, tunda sun ga yacce rashin ƙwarin guiwa ke sa wasu faɗuwa, babu confidence.
Malam Abbo ne ya biyo su Banafsha yana taka musu, yana ƙara basu shawarwari yanda za su yi karatunsu hankali kwance ba tare da yawan idanuwan jama'a a kansu ya dame su ba, ko ya hana su yin nasara, su Umaima dai suna ta sauraronsa har ba su ankare ba suka fara hango gida, Malam Abbo ma na farga ba ashe ya biyo su har gida, kuma tun daga nesa Umaima da Banafsha suka hangi Ya Danish a ƙofan gida kuma ya kallesu.

Malam Abbo sallama ya musu zai juya, sai Banafsha ta langwaɓar da kai ta ce, "Malam ba ka faɗa mana abinda ya hanaka zuwa ba, in rashin lafiya ne ai sai mu dage da addu'a, Allah bawa malaminmu lafiya."

Umaima duk ta sture ko sauraran su Banafsha bata yi, kuma ta kasa tafiya tabar Banafsha, ga shi Ya Danish ya zuba musu na mujiya ko ƙiftawa ba ya yi, kuma fiskan nan a haɗe, kana gani kasan yau akwai bala'i.

Malam Abbo yana murmushi ya ce, "Na É—an yi tafiya ne urgent zuwa Borno, afuwan ko Malama FaÉ—ima."

Banafsha murmushi ta sakar masa mai rikitasa ta ce, "tunda Malam ya dawo lafiya Alhamdulillahi, sannu da gajiyan hanya, gobe kada a mance mana tsarabanmu Malam", ita fa Banafsha duk saboda Ya Danish ya ƙulu take yi.

Malam Abbo da ya susuce, murmushi kawai yake sakarwa Banafsha kaman ba lafiya ba, har ya buɗe baki dan faɗa mata akwai maganan da yake son faɗa mata, amma sai ya fasa kawai ya dake, ya musu sallama ya juya, zuciyansa cike da wani irin ƙaunar ɗalibarsa Faɗima.

Banafsha da gangan ta staya tana yiwa Malam Abbo bye-bye, duk da ya riga ya juya, amma yi take dan Ya Danish, har da É—aga hannu sama ta yi alaman love, Umaima da ta gaji da haukan Banafsha sai wucewa tayi ta ce, "Sai kin iso, tunda ba ki san ruwan da ke gaban mu yana jiranmu ba, yau nasan nidai na gama yawo na kaÉ—e, Ya Danish zai targaÉ—a ni.

Banafsha na murmushi ta juyo, daga inda take ta harari Ya Danish sannan ta bi Umaima da sauri tana faÉ—in, "jirani Umaimaty, zan je wajan Ummu."

# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKI NE

Hareeyh (Uwar batoorl)🤣
Masu Sharhi sun ƙare, dole na bawa kai ka page, nima na ɗana ladan typing.

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 41 _ 45

Umaima tuni tayi nisa da tafiya ko jin Banafsha bata yi.

Sai da suka iso dai-dai wajan su Ya Danish sannan Banafsha ta ce, "Umaima na fasa binki."

Ai da sauri Umaima ta ƙankamo hijabin Banafsha ta ce, "wallahi kin yi kaɗan Masoyiya, tunda kika ja mana ruwa dole ruwan nan ya dake mu tare, ba inda za ki je."

Banafsha na danne dariyanta, suka gaishe da su ya Farooq, Umaima ce kawai ta gaishe da Ya Danish, amma Banafsha ko kallon inda yake bata yi ba, nunawa tayi ma kaman bata san da halittansa a wajan ba, shi kuwa Danish aikon masifan da ya ƙulla ko gaisuwan Umaima bai amsa ba, buri yake kawai Banafsha ta shiga gidansu, yau sai ya seta mata hankali ya gyara mata wajen zama, ga shi Abbaa ba ya gida balle ya ƙwace ta, dan cike yake da haushin abinda ta masa ranan, kuma tsaff ya shirya muguntan da zai mata, ta yacce ko da kuɗi aka haɗa ta akan ta ƙara faɗa masa magana ba za ta iya ba.

Umaima haka ta maƙalƙale Banafsha sai da suka shiga gidan tare, suna shigewa Danish ya mike stamm! Ya rufa musu baya yana sakin murmushin mugunta, cikin dabara ya faɗawa su Farooq bari ya ɗauko abu a ɗakinsa ya dawo.

Yana shiga ya samu har sun shige cikin gida, ƙwafa yayi tare da sakin murmushi ya wuce part nasu na maza da yake ta bakin ƙofa yana jiran fitowanta.

Umaima suna shiga cikin gidan ta saki hamadala tare da cewa, "To nidai na stira, saura ke mai fita ki koma gida, Allah shiga tsakaninki da masifan da ke bakin ƙofa yana jiran fitowanki."

Banafsha Murmushi kawai ta sakar wa Umaima, ta nufi ɗakin Ummu, amma a bakin ƙofan suka kusa yin karo da Nana ta ce, "Banafshaty, ai Ummu ta bi Abbaa sun je asibiti dubiya tun ɗaxu."

Umaima ma fitowa tayi a ɗakinsu ta ce, "sorry masoyiya mancewa nayi ban faɗa miki Ummu bata nan ba, duk storon Ya Danish ne ya cika ni, matar abokin Abbaa ce babu lafiya، shi ne suka je gaisheta a asibiti."

Harara na aikawa Umaima dan taban haushi, storonsa sai ka ce ya zama wani mala'ikan mutuwa, ba tare da na saurareta ba na juya zan fice, Umma da fitowanta ɗaki kenan, ƙwafa tayi ta ce, "Idan na kuma ƙara ganinki a cikin gidannan ni nasan abinda zan miki, yarinya gaba-ɗaya bata da zuciya, wato har gida kike bin kabeeru ko? To kuwa zan baki mamaki idan kika ce za ki ɗaura shegun fistararrun idanuwanki akan yarana, ki ƙare can ke da karuwar uwarki, kuma idan ma shanyewa yarinyata zuciya kika yi take binki a baya kaman bindi, to ki sani ina dai-dai da maitanki, idan baki ƙyale mini yara kin fita harkansu ba to ba shakka zan saɓa miki."

Umaima ta buɗe baki za tayi magana sai Umma ta kwashe ta da mari, saurin juyowa nayi rai na a ɓace saboda maganganun Umma, idanuwana akan Umaima na mata alama da ido kada ta ce komai, matar babban yaya ce ta aiko mini da harata tare da yin staki ta ce, "Wallahi idan baki fita harkan mijina ba sai na miki illa, shegiya, ƴar iska, ƴar karuwa..."

Kamun ta rufe baki tuni na dira gabanta na kwasheta da maruka biyu ba ruwana da cikin jikinta, amma kamun na ɗago tuni Umma ta kwashe ni da marin nima ji kawai kake tassss! tasss!, cikin masifa Umma ta ce, "Dan uwarki har kin isa ki taɓa mini surka yar gidan mutunci? Kina ƴar karuwa, ƴar shege"

Ba tare da na tankawa Umma ba, na kuma ɗaga hannuna na kwashe matar yaya babba da maruka, zuciyana na tafasa na ce, "ki bari manyan da babu yacce na iya da su suyi, dan su zan iya ƙyale su, idan ma basu riƙe girmansu ba to ni san basu mastayinsu, amma ke kika ce za ki shiga stabgata zan iya fige miki gashin mugun waje, ni ɗin nan ban da kirki ban da mutunci, kibar ganin wasu nayi ina shiru ki ɗauka ke ma za ki ci banza, wallahi kika masta a lamarina sai na saka zuciyanki ta buga, ƴar iskan kai na ce ni ɗin nan, mijinki da ya mini to ko kallonsa ba za kiyi ba balle ya aure ki."

Umma kuwa jin abinda na faɗa, a fusace ta iyo kai na tana masifa, amma sai Umaima ta tare ta tana kuka tana cewa, "menene haka Umma? Dan Allah ki bari, da ƴar cikinki kike haka, wallahi idan Banafsha ta rama marin da kika mata ba ruwana ba zan ji zafi ba ke kika nema...." Bata rufe baki ba amma ta hankaɗata gefe ta iyo kai na, matar yaya babba kuwa da taji mari tuni ta zauna daɓas da cikinta a ƙasa ta kasa yin magana, ga haushina ga kuma shakka na.

Wani irin kallo na yiwa Umma tun kamun ta iso gareni, sannan na juya, sai ji na nayi na ci karo da mutum, idanuwana a rufe ban damu da wa nayi karo ba na ci gaba da tafiya, sai ji nayi an riƙe hannuna anyi baya da ni, a hasale na ɗago jajayen idanuwana cike da masifa, amma sai tozali nayi da yaya babba, rai na ƙara ɓaci yayi na ƙwace hannuna na juya, bi na yayi yana cewa, "kiyi haƙuri Banafsha, kada ki tafi a haka.."

Umma cikin ɓacin rai ta ce, "kabeeru idan ka kuma taku ɗaya sai na stine maka, dan Ubanka me haɗin ka da ita? daman gaskiya Hindatu ke faɗa mini kenan? Tunda ga shi har haƙuri kake bata, bayan rashin kunyar da ta mini, ta kuma mari matarka da juna biyu a jikinta."

Babban yaya stayuwa yayi rai a ɓace bai cewa Umma komai ba, dan shi Banafsha ta masa dai-dai ko me ta musu su suka nema da kuɗinsu, kwafa yayi yana bin matar sa da mugun kallo, domin kusan duk abinda ya faru akan idonsa ya faru, kuma yasan laifinta ne, daman tun ranan ya fara ganin take-takenta, Umma ma harara ta aika masa da shi ta ce, "idan ka kuma yiwa yarinyar nan magana sai nayi mugun ɓata maka rai wallahi."
Chapter 21 · 0% Book details