← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 58

Sashe 45

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaƙe kawai Mami tayi ta ce, "Ina yarinyar tawa?"

Ummu ta ce, "ai Umaima ta ji sauƙi Mamin yara, ina ga tana sallah ne ma, da yanzu kin gan ta..." Ummu bata gama rufe baki ba sai ga Umaima ta fito tana murmushi, ta buɗe baki ta ce, "Mamina ayoyoo, sannu da shigowa..."

Umaima bata gama magana ba, ta stinkayo muryan Umma na faɗin, "kika ƙara faɗan wani kalma ran ki zai ɓaci, wuce ki koma ciki, shashashan yarinya kawai.

Daga Ummu har Mami da Ya Farooq duk da kallo suka bi Umma, Umaima rau-rau ta yi da idanuwanta kaman za ta yi kuka, wani kallon Umma ta jefe ta da shi ta ce, "koma ciki na ce."

Umaima juyawa tayi ta koma ciki, Ya Farooq dai da mamaki yake kallon Umma, ƙarshe tashuwa yayi ya fice dan baison ganin abin kunya.

Mami murmushi tayi kaman ba komai ta ce, "Umma Kabeer barka da yamma, ya jikin Umaiman?"

Wani irin kallon banza, kallon stana Umma ya jefawa Mami tare da sakin dogon tsaki ta ce, "Munafuka kawai, wato kin biyo mu har gida ki ƙwace mijin namu, amma tun da yake ke ɗin ƴar bariki ce dole ki lauye da duba yarinyata, to ba'a buƙatan gaisuwan an yafe miki, tashi ki fice mana a gida, ƴar ƙwace kawai."

Mami murmushi ta kuma yi ta miƙe tare da kallon Ummu ta ce, "Ummun su sai anjimanku, Allah ƙara sauƙi."

Ummu nauyayyan ajiyan zuciya ta sauƙe ta ce, "ki yi haƙuri Mamin yara, ke kuma Maman Kabeer gaskiya abin da kike yi bai kamata ba."

Umma a hasale ta hayayyaƙo wa Ummu ta ce, "To babbar munafuka algunguma, an faɗa miki duk abinda ke faruwa ban sani ba ne? Wallahi can ya ƙare miki a maste-mastinki, ƙarya kike a auro wata balle ki samu daman haɗe kai da wata a gidan nan."

Murmushi Ummu ta yi ta girgiza kai tare da cewa, "shi dai kishi ba hauka ba ne, dan haka kisan me ke fita a bakinki, kada ki ga ina miki shiru, ba storonki nake ji ba, gudun tashin hankali nake yi, kuma Insha Allah sai ya aurota."

Umma na ƙoƙarin yin magana sai Mami ta yi saurin taran numfashinta ta ce, "Dan Allah kuyi haƙuri dukanku, in Allah ya yarda ma ba abin da zai haɗa ni da mijinku balle wannan tashin hankali ta faru, kuma ni ban shigo dan haɗa ku faɗa ba, dubiya na zo yi kuma na yi zan tafi Allah ƙara sauki" Mami na gama magana ta juya ta fice a gidan, cikin damuwa, ita ko ta rasa mijin aure me ya kai ta haɗa hanya da Umma, balle har su haɗa miji, ita auren da ma gaba-ɗaya babu shi a lissafinta.

Umma kuwa da harara ta bi Mami da shi har ya fice a gidan, sannan ta juyo ga Ummu ta ja staki tare da cewa, "aikin banza aikin wofi, kuma wallahi dan ki ji ba gwaninta kika yi ba, tunda abin ba ni kaÉ—ai ta shafa ba, miji nawa ne kuma naki."

Ummu murmushi tayi ba tare da ta tankawa Umma ba ta shige É—akinta, tana koÉ—a halin kishi irin na Umma.

Mamina ko da ta koma gida, ɓoye damuwanta ta yi, ban ga alama ba kuma bata sanar da ni ba, ɓangaren su Ummu ma ba wanda ya yiwa Abbaa maganan abin da ya faru, Umaima dai ba yanda ta iya da halin Umma, ko mene mahaifiya ce dole ta ji magananta.

Washegari asabar sai ga ya Danish da sassafe, sai da Abbaa ya dawo sannan suka zauna shi da Ya Danish, Ya Farooq da kuma babban yaya.

Abbaa ne ya fara magana ya ce, "Farooq da Danish na baku lokaci, kuma ga shi lokacin kun cinye sa murƙus, ba wanda ya bani amsa mai kyau a cikinku, hukuncin nawa kuke so na zartar ko?"

Danish ƙasa yayi da kansa yana sosa ƙeya, shi kuma Farooq murmushi yayi, sai yaya babba ya ce, "A yi haƙuri a ƙara musu lokaci Abbaa, kasan yanzun lamarin daga matan har mazan sai a hankali."

Wani kallo Abbaa ya yiwa yaya babba ya ce, "To ubana ba zan ƙara musu lokaci ba, kai da kake da mata yanzu baka jin ka cika mutum, baka jin wani nustuwa ta daban? Ai duk namijin da ya kai riƙe mata muka ba shi da ita, to ba'a niste yake ba, kawai a gansa haka ne a ƙyalesa, an faɗa maka gauranci daɗi ne da ita? Balle kuma ga wanda ke ƙoƙarin ƙewata ƴar mutane mutunci, to ba lokacin da zan ƙara musu, ko su fidda mata aje a tambayo musu ko kuwa ni da kai na nayi musu matan, idan ma idanuwansu sun makance ne, to nawa a buɗe suke tarr! Ai duk cikinsu ba wanda zai ce ba shi da budurwa, to ba za'a yaudari yaran mutane da ni ba dan haka kun ji me na faɗa ai, babu ɗaga ƙafa."

Ya Farooq ƙasa yayi da kai ya ce, "Abbaa ni dai ina jira ne daman ka ƙira mu, amma mun gama magana da wacce nake nema, iyayenta kuma sun ce na turo manyana daman."

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce,"To ka taimaki kan ka, inba haka ba kuwa za ka ga yanda ake yiwa namiji auren dole, to kai kuma Malam Danish ina sauraranka ya muke ciki? Ka samu ne ko na bada sadakanka?"

Daga Abbaa da yayi maganan, har su yaya babba ba wanda maganan bai sa dariya ba, ya Danish sosa ƙeya yayi ya ce, "Abbaa nima dai na ba da kai na sadaka wa wata."

"To Masha Allah! Duk Allah ya muku albarka, kun taimaki kan ku" Abbaa ya faÉ—a yana murmushi.

Yaya babba ya ce, "To sai ku faÉ—a mana yaran gidan waye ne, dan a shirya maganan zuwa magana da iyayensu."

Ya Farooq ya ce, "Sunanta Ruƙayya gidansu na anguwan Kaban."

Abbaa jinjina kai yayi ya ce, "Madalla! Allah tabbatar da alkairi, kai kuma Danish fa."

Danish sosa kai ya fara yi, yana in-ina, "uhmñ...umn..am..dama...daman ba..am Abbaa dama dai ni ba wai mun dai-daita da ita ba ne, izini za'a nema mini tukunna."

Kallonsa Abbaa yayi ya ce, "To malam Danish, masu bin starin addini yanda ya kamata, hakan ma yayi ai Allah muku albarka, wacece, in ya so gobe ko jibi sai a tambayo maka."

Danish ƙasa yayi da kai ya ce, "am Faɗima ce, ina...ina..ina nufin Banafsha."

Ba iya Abbaa ke kallon Danish da mamaki ba, hatta ya Farooq da babban yaya kallon mamaki suke bin Danish da shi, gani suke dai kaman bai san abinda yake faɗa ba, kamun Abbaa yayi magana tuni yaya babba ya ce, "Amma dai Danish baka san sunan wa ka ƙira ba ko? Banafsha dai kake nufi ƙawar Umaima, yarinyar Mami?"

Abbaa ya É—aura da cewa, "Banafsha da ka mayar da ita kuran wasanka Æ´ar gidan amaryan da zan aura Ramla, ita kake nufi ko wata daban?"

Maganan Abbaa duk dariya ya basu wai ƴar gidan Amaryan da zai aura, amma suka maste kawai suna sauraran Danish, shi kuma cikin tabbatarwa ya ce, "Ita dai Abbaa, ka yi haƙuri, wlh ita nake so."

Jinjina kai Abbaa yayi ya ce, "riƙe haƙurinka idan ka je wajanta zai maka amfani, ni ai mai farin ciki da hakan ne, zan yi addu'an Allah tabbatar da alkairi, Uba ya auri uwa, ɗan sa ya auri yarinya, Masha Allah, in Allah ya yarda zan yi magana da ita idan na je zance."

Ya Danish murmushi yayi yana addu'an komai ya zo da sauƙi, shi ya rasa irin Soyayyan Banafsha da ya mara diran mikiya, ya Farooq dai mamaki yake har yanzu, yana kuma tunanin yanda za'a kaya da Umma idan ta ji wannan magana, yaya babba kuma dai kallon Danish bai san abinda yake ba yake masa, saboda ko shi da yake namiji idan aka ce shi ne suka wannan ƴar stama da mutum to ba zai yarda ya so shi ba balle aure, lallai akwai aiki a gaban Danish, haka zaman nasu ya waste bayan sun ɗan tattauna abubuwan da ya kamata.

Ya Danish washe-gari da sassafe ya bar gari baya son ma ya haÉ—a ko ido da Umma, dan yasan idan ta ji labari to akwai yin ta, amma bai da mastala tun da Abbaa ya yarda kuma zai tsaya masa, yanzu a yanda yake ji ba abinda ba zai iya yi ba akan soyayyan Banafsha, Allah-Allah yake a tambayo masa ya fara zuwa ya samu ya kori wannan saurayin nata, shi ana tambayo masa to kusan kullum sai an gansa a Mubi.

Ranan Lahadi kaman kullum Malam Abbo ya zo muka sha hiranmu, ya ce zai turo amma na ce masa ya dakata tukunna, haka ya haƙura ba dan ya so ba, Mami ta ƙira mini Alhaji mun gaisa na faɗa masa result na yayi kyau, ya tambayi abinda nake so, amma na ce sai ya dawo, idan ya zo zan faɗa masa, haka muka yi sallama akan ba zai wuce wata guda ba zai dawo, Mamina kuwa ko da ta ƙara mini maganan aure to abin da na faɗa mata ranan shi na maimaita, sai kuma ta koma lallashina ganin na dage.

Mun ci-gaba da zuwa makaranta boko da tahfiz tare da Umaima har yau da ta kama Alhamis, da yake ba mu da class da safe, to ba mu je da wuri ba, sai wajan ƙarfe goma muka bar gida muka tafi College.

Abbaa ya ƙara wa Mami sati guda akan watan da ya bata, to yau Alhamis ya yanke ranan juma'a zai je wajan Mami, sai ya ce bari ya sanar da su Umma maganan auren Danish dan su san da shi, don abun ya yiwa Abbaa daɗi ko ba komai hakan ma zai ƙara nistar da Umma.
Chapter 45 · 0% Book details