← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 58

Sashe 11

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Abbo kuma cigaba da dudduba takardun yayi, dan yana azumin kamawan sabon watan musulunci dan haka sai yamma zai koma yayi wanka ya dawo kamun É—alibai sun zo tunda ranar weekend safe da yamma ne makarantan nasu.

Cikin farinciki Umaima da Banafsha ke tafiya, Umaima ta ce, "heehuhuuu! wa ya ga su Ummu-khultum ɗin Abbaa an zama Hajiya, hhhh! Hajiya Umaima sama, Hajiya Umaima ƙasa, ai wallahi kullum cikin dariya nake dan haƙori yayi ta qyalli, ga mu da wushirya dukanmu, ya kika hango mu masoyiya?"

Murmushi nayi na ce, "Kai Umaima kin cika zumuÉ—i wallahi, yanzu in bamu samu ba fa?"

Ɓata fiska Umaima tayi ta harareni ta ce, "Kai amma masoyiya a'uzubillah da wannan mugun fatan, ai in Allah ya yarda mu ne za mu cinye, dan haka in Allah ya yarda zuwa Makka very soon, Madinatul Munawwara is loading."

Kallonta nayi na ce, "Amma kinsan wannan na iya cikin Mubi ne ko? Ba lallai mu samu kujera ba, dama dai na jiha da jiha ne ko kuwa ƙasa da ƙasa, wannan kam in Allah ya yarda za'a samu."

Murmushi Umaima tamun ta ce, "koma dai menene in Allah ya yarda mun kusa zuwa Makka...." Maganan dake bakinta ne ya maƙale sakamakon abinda muka ji ana faɗa a bayanmu.

''ƳAR KARUWA ! Woooo!! 'YAR KARUWA!!! mai kyawun ɗan maciji, asa hijabi kaman musulman ƙwarai a je makaranta da najasa a jiki, ake ɗaukan Qur'ani wa ma ya sani ko malaman ma raba musu majalisar ake yi, 'YAR KARUWA!! WOOOO!!!!"

Cikin taƙaici muka juyo dukanmu ni da Umaima, murmushin da yafi kuka ciwo ne ya ƙwacemini ganin Garba ne ke maganan kuma ga yara kusan uku a gefen sa yana sanya su faɗin ƴar karuwa, suna taya shi yin haukan nasa wanda a tunaninsa yayi dan ya ƙuntata mini ne, bai san yayi a banza ba domin a yanzu ina jin zan iya danne zuciyata ko ma me za'a ce mini, saboda sosai na ji faɗan da Umaima ta mini.

Umaima za tayi magana sai na yi saurin taran numfashinta na ce, "Umaima ki ƙyale sa da ƙaramin haukansa, dan ina fara magana ko kuwa kika tanka masa to wallahi sai na kwaɗa masa mari, kinsan halina, muje kawai ki ƙyale sa."
Hannunta na kama muka ci gaba da tafiya ina mata hira kaman ba abinda ke damu na amma ita kuma kana ganinta kasan ta sanya abun a rai, ni ake yiwa isgilin amma ita yake damu, Umaima tawa kenan, ina mugun ƙaunarta.

Tun daga nesa da muka hango ya Danish tare da abokin sa na yi gefe, ganin bai ganmu ba sai nayi saurin sake hannunta tayi gaba ina bin bayanta ina magana kaman taƙi kulani, saboda kada na ja mata faɗa duk da sai da na lallaɓata, sannan ta yarda da hakan, ina binta a baya ina cewa, "haba Umaima me yasa ba zaki staya mu tafi tare ba? Yau duk kin ƙi kula ni me na miki ne wai?"
Har muka isa wajan da yake staye da abokinsa abinda nake faɗa kenan kuma da ƙarfi yanda zai iya jiyo mu, Umaima da ke ƙunshe dariyanta, tana wuce su ta shige gida tana dariya har da kama ciki, idanuwansu duka biyu na kai na har na iso dai-dai su ina magana, na nufi hanyan gidansu Umaima zan shiga sai ya sakarmun wani gigitaccen stawa ya ce, "Keeeeeeeeeeeeeee...! Kar ki sake ki shigar mana gida, tunda kuna da naku ɓace mana a gaban gida."

Murmushi nayi wanda ya kawar da damuwan dake raina sannan na juyo na tako har inda suke dan dama ina da cikin sa, stayawa nayi a gabansa ba tare da na kalli abokin sa ba na ce, "Mai digiri a iskanci tun da ba gidan ubanka kai kaÉ—ai bane sai na shiga, kuma Allah ya sa ma muma muna da gidan kai ma ka sani, mtswwww!", Juyawa nayi na shige gidansu Umaima hankalina kwance, rai na fess na ci masa mutunci a gaban abokinsa, shi ma yaji idan da daÉ—i.

Rai a mugun ɓace ya juya zai biyo ni amma ganin Abbaa sai ya fasa ya tsaya yana huci, ni kuwa ganin bai biyo ni ba ko da na leƙo naga Abbaa na ƙofan ai cikin sauri na fito na wuce gidanmu dan dama na riga na gaishe da Abbaa, kuma dan nasan Abbaa na gida shiyasa na masa haka, saboda ba zai taɓa bari ya taɓa ni ba.

Abokinsa yana dariyan abinda ya faru ya ce, "Danish wacece yarinyar nan haka?"

Ya Danish wani mugun staki ya ja, cikin taƙaici da haushina ya ce, "Mtsww! Dauda ka yi shiru kar ka tambayeni komai, Hmmn! Har ni yarinyar nan za ta dage da qira ɗan iska bayan ga ta cikakkiya tunda uwarta karuwa ce, to wallahi ni nasan abinda zan mata" ya Danish kaman zai daki babu haka ya dinga huci, abokinsa sai dariya ya ke, shi kuma duk ya bi ya cika yayi fam kaɗan yake jira ya fashe.

Mun yi hutun weekend cikin kwanciyar hankali da farincikin kasancewanmj cikin masu musabaƙa, dan kuwa Malam Abbo (haydar) ya tsaya mana komai da mu ake damawa, taƙaicin rayuwa kuwa ba abinda ya ragu sai ma ƙaruwa dan bazan fita na dawo gida ba tare da an jefe ni da mugun magana ba, tsakanina da ya Danish kuwa ba komai sai tarin stana da kuma burin quntatawa juna bai ƙyaleni ba, nima ban ƙyalesa ba, ba ya tausayina ni kuma bana storonsa ko zai kashe ni sai na masa abinda na ga dama.

Yau da yake Monday muka shirya muka tafi makaranta, bayan mun gama class bayan azahar muka dawo ba hutu muka shirya 4:00pm muka tafi Tahfiz, mu ne bamu dawo ba sai 6:30, muna dawowa Umaima ta shige gidansu, nima nayi namu dan kuwa yau ya Danish baya gari dama daga juma'a zuwa Lahadi kaÉ—ai ake ganinsa a gida.

Bayan wata guda abubuwa sun taru sun mini yamun yawa, yanzu ya zamana ma banda lokacin yawan yin tunani ko kuka dan kuwa exam's ne a gabanmu na fita aji biyu a makaranta, sannan ga musabaƙa ya zo shi ma saura sati biyu, exam's kuma Monday mai zuwa za mu fara wanda yau yake Thursday, Allah ya so dai a satin da muka gama exam's,sati mai kamawa shi ne na musabaƙan.

Zaune nake a palourn mu daga ni sai under-wear da vest na baza hangout a gaba na ina kan duba wa, kai na ba ɗan kwali kiston ebra da Umaima ta mini manya da qanana jelar har kusan ƙugu na, ba tare da naji sallama ko mosti ba kawai naji hannun mutum a kai na yana jan jelar gashi na, ɓata fiska nayi na ɗago dan duk a tunanina Umaima ce za faɗa mata bana so, domin nasan ita ce mayyar gashina idan tamin kisto sai ta dinga damuna kenan sai na kulle kai na nake hutawa, maganan dake baki nane ya maƙale ganin wani babban dattijo da shirgegen ƙaton cikinsa yana washe mini bakin da na tabbata haƙoransa sauran babu, yana murmushin da ke ƙara masa muni ya ce, "Yarinya kin yi kyau ƴar shila da ke haka."

Cikin taƙaici na miƙe na ɗaga hannu da niyan kwaɗa masa mari, sai kuma na tuna babban mutum ne ya yi jika da ni ma ba ƴa ba, ƙwafa nayi tare da jefansa da mugun kallo na tsana na ce "Stohon banza da wofi wanda bai san daraja da mutuncin ƴa mace ba, kai dube ka fa sa'an kaka na kana wani washemun shaddan bakinka stohon najadu kawai, wallahi ka ci albarkacin musulunci da stufan ka, da abinda zan maka ba za ka iya ɗauka ba", ina gama magana na rarumi hijab nawa na saka, na sunkuya ina tattara takaddu na.

Muryansa na ƙara stinkayowa yana cewa, "Haba ƴar shilah ai kyawunki ne ya ja kuma bar ƙira na da stoho, nan da kika ganni sai na miki abinda yaro ɗan shekara 30 ba zai miki ba domin kuwa kayan aikin da ƙarfinsu ko mamarki bata sharewa a buga wasa da ni."

Ɗagowa nayi idanuwa har sun kaɗa dan baqin ciki da taƙaicin maganansa na ce, "Wallahi idan har kana da kunya to kaji kunya, kuma ka yi asara dan daka ganni nan nafi ƙarfin ka kuma uwata ma daga yau ina tabbatar maka ba kai ba ita" na faɗa ina wucewa ɗakina tare da banko ƙofana.

Ina cire hijab na zube kan gado ina jin kuka nason ƙwace mini, sai kawai naga mutum ya shigo min ɗaki daga shi sai boxer da vest, tashuwa nayi a storace cikin in'ina na ce, "kaa kaaa, memm... me.. ya kawo ka ɗaki naa?" Na faɗa murya na rawa ganin stoho ba kaya ga kuma wani abu da nake hangowa a wandon sa ya miƙe kaman katako aka sanya masa a cikin wando.

Kai na ya iyo yana washe baki, kamun na buɗe baki da niyan lwala ihu na ji muryan Mami na cikin mugun stawa ta ce, "Alhaji sabooooo! Yarinyar tawa za ka ƙetawa mutunci a gidana?"

Cikin razana stohon ya juya yana rarraba ido ganin Mamina, ai da gudu nayi wajanta na ɓoye a bayanta ina sakin marayan kuka, rungumeni tayi taja hannuna muka fice a ɗakin ta yafamun mayafin jikinta, ba tare da ta ce mini ko ƙala ba.
Muna zaune a palourn sai stohon ya fito yana sussunne kai, ya buɗe baki zai yi magana Mamina ta miƙe ta kifa masa mari, cikin mugun ɓacin rai ta ce, "Kai Sabo mara mutunci, mastiyaci, ɗan iska, stohon da baisan daraja da mutuncin yara ba, ka fice mini a gida tunda bada kuɗin ubanka na gina ba, ko kuwa na ƙira maka hukuma yanzun nan, kai ba hukuma ma ni nan na ishe ka, indai a kan wannan yarinyar tawa ce to zan iya kashe mutum."
Chapter 11 · 0% Book details