← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 58

Sashe 53

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Mami ta kuma yi ta ce, "Ba na yafe mata saboda wasu su ji daɗin aikatawa bane, a'a na yafe mata ne saboda waɗanda aka wa laifi irin nawa ko fin nawa, su ji daɗin yin yafiya da nufin su ma Allah ya yafe musu wani yanki na zunubansu, Banafsha akwai wani kissa daga Manzon Allah SAW kan cewa, watarana a gaban Allah ranan tashin ƙiyama, akwai wani mutum da za'a tattara ladansa a biya bashuka, zalunci, munafurci, ha'inci da sauran su, duk za'a biya haƙƙonƙin jama'a da ya ci, da ladan ayyukansa na alkairi, sai ya zamana dai-dai da ƙwayan zarra ba shi da lada ko guda, to ana cikin haka kuma wani mutumin zai ƙara ɓullowa ya faɗawa Allah, ai shi ma yana bin wannan mutumin bashi dan haka asaka shi ya biya sa, idan Allah ya ce wa wannan mutumi mai laifukan ya ji abinda wannan ya faɗa, sai ya kama murmushi, ko da Allah ya tambayi dalilin murmushin nasa, sai ya ce ai gani yayi bai da lada ko ƙwayan zarra, duk ladan an biya jama'a da shi, yanzu ba shi da komai sai zunubi, Allah ya kuma duban mai kawo ƙara ya ce kai ma ka ji abinda ya faɗa ai ba shi da lada, sai mai kawo ƙara ya ce, in mutumi mai laifin bai da lada, to ai shi yana da zunubi, dan haka a ɗiba, zunubinsa gwargwadon haƙƙinsa da ke kan mutumi mai laifin, a ƙara masa akan nasa zunuban, Allah zai ƙara kallon mutumi mai laifin ya faɗa masa ya ji abinda mai ƙaransa ya faɗa, sai mutumin yayi murmushi ya ce ya ji ya amince, sai Allah ya sa a nuna wa mai laifin yan da jahannama ta ke, idan ya kalli jahannama sai hankalinsa ya tashi, daga dariya ya koma kuka, idan Allah ya tambayesa yana dariya kuma mai yasa ya koma kuka tun da ya yarda, mutumi mai laifin cikin tsananin kuka da tashin hankali zai faɗawa Allah yana son yayi magana da wannan mai ƙaran nasa, to Allah zai basu wata farfajiya su magantu, wannan mai laifin yana kuka zai haɗa mai ƙaransa Allah da Annabi ya taimaka ya yafe masa, idan ya ce a ƙara masa zunubinsa zai ƙara masa azaba ne, kuma idan yana da zunubai da yawa to shi ma ba zai hanasa shiga wutan ba, dan haka sai wannan mai ƙaran ya yafe masa, su koma gaban Allah mutumi mai ƙaran ya faɗawa Allah ya yafe ma mutumi mai laifin, idan Allah ya tambayi dalili sai ya faɗa masa ai shi ma yana da zunubi, dan ya ce a ƙarawa wani zunubinsa ba zai hanasa shiga wuta ba, kawai ya yafe, sai yayi haƙuri, to saboda wannan yafiyan da ya yiwa mutumi mai laifin ya kuma haƙura, sai Allah ya yafe musu duka ya saka su a aljanna, saboda Allah ya ce yana ƙaunar masu haƙuri, to sai Sahabbai suke mamakin yan da ake wannan al'amari duka a gaban Allah, Manzon Allah SAW ya faɗa musu abinda ake nufi da wannan al'amari shi ne haƙuri, Allah na tare da mai haƙuri, Allah na son mai haƙuri, Allah yana sakawa ga mai haƙuri, saboda Allah shi ne ahkamul hakeemin, shi ya fi kowa iya hukunci..."

Tun da Mamina ta fara wannan bayani na stura mata idanuwana ko kiftawa bana yi, har sai da ta kai aya, sannan na sauƙe ajiyan zuciya tare da lumshe ido na ce, "To Allah ba da lada Mamina, Allah kuma ya yafemu baki ɗaya, Mami amma dan Allah me yasa kika kasa haƙuri da danginki? In kuma ke ce kika musu laifi me ya sa ba za ki je, ki basu haƙuri ba tare da nusar da su fa'idan haƙuri da yafiya ya za su miki, Mami shi kuma mahaifina me ya miki? Ina yake? Mamina dan Allah dan darajan Annabi SAW ki taimaka ki amsa mini waɗannan tambayoyin."

Mami murmushi tayi tare da ƙarisa wa da salati Manzon Allah SAW, ta ce, "Insha Allah Banafsha zan ba ki duk amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma ba yau ba, ban faɗa rana na amma na kusa sanar da ke komai kin ji, ki yi haƙuri ki ƙara haƙuri."

Kwantawa nayi a jikin Mamina ban kuma cewa komai ba, wannan mutumin da muka haÉ—u da shi a asibiti ne ya faÉ—o mini a rai, tura baki nayi lokaci guda kuma na murmusa, tuno abinda ya faru, Mamina kallona ta ce, "Lafiya da murmushi haka gudalliyan Maminta."

Murmushi nayi ba ɓoyel-ɓoyel na ce, "Mami bansan me ya same ni ba lokacin da kika yi rashin lafiyan nan, amma gaba ɗaya na zama kaman parrot a surutu, wannan Soja da Abbaa ya faɗa miki shi ya biya kuɗin komai, Allah haka kawai na dinga masa masifa na rasa me ya sa, sai kuma yanzu abin nake tunawa, ni da ba halina ba, meyasa na masa haka oho، kuma fa bai biye mini ba, ce mini kawai yayi idiot" na ƙarishe maganan ina tura baki.

Shafa kai na Mami tayi tare da sakin murmushi ta ce, "Allah ya amsa albarka ya saka masa da alkairi, ga shi ko sunansa ba mu sani ba, wannan su ne masu yin abu dan Allah, fisabilillahi, ke kuma Allah shirya mini ke, ai daman Banafsha bakya ji, kin cika stiwa da manyance."

Tura baki nayi, muka ci-gaba da hiranmu da Mamina tana shafa kai na, gaba-É—aya hasaso wannan bawan Allah kyakkyawan soja nake ina murmushi, har ban sani ba bacci yayi gaba da ni.

Danish kuwa tun da ya zo ya ji labarin abin da ya faru, ba ƙaramin damuwa yayi ba, musamman da ya kasance shi ne sanadin komai, haƙuri ya bai wa yaya babba, bayan ya masa faɗa sosai, tare suka shirya suka tafi wajan Umma, amma da ƙyar aka bar su suka kalleta, nan ma sai da Danish ya bada kuɗi masu yawa na cin hanci.

Duk maganan da suke yi Umma ko ƙala bata ce musu ba, bayan amsa gaisuwansu da ta yi, tambayan Umaima tayi da kuma matar yaya babba ko ta haihu, bayan sun bata amsa shiru ta ƙara yi, gaba-ɗaya sai tausayin mahaifiyarsu ya rufe su, ta zama abin tausayi ta rame ta yi baƙi, shiru ta musu har lokacin su ya cika, suka tashi za su tafi, sannan Umma ta buɗe baki ta ce, "idan yayi ku kawo mini Autana Umaima na gan ta."

Cikin tausayin Umma, yaya babba ya ce, "Insha Allah Umma za'a kawo miki ita."

Ficewa suka yi suka tafi, daga nan kuma suka ci-gaba da tattaunawa akan yan da za su yi Ummansu ta fito.

Gaba-ɗaya mun zama busy a maganan makaranta, ko kaɗan duk ƙoƙarin Ya Danish na ganin ya samu daman stayuwa da ni ta ƙi samuwa, har ya cinye weekend nasa, yau Sunday zai koma, dan haka yau ya dage komin dare to kamun ya koma sai ya haɗu da ni.

Ni da Umaima mun je tahfiz na yamma, mun dawo, muka yi wa junanmu sallama, ta shige gidansu nima na wuce namu, kai na a ƙasa ina sakin murmushi ni kaɗai, saboda hiran Soja muka gana yanzu da Umaima, ba tare da na kula ba na ji nayi karo da mutum na yi baya zan faɗi, sai aka riƙo hannuna, idanuwana a lumshe nayi hamdala sannan na buɗe su na ɗago ina faɗin, "Na gode....", maganan baki nane ya maƙale ganin wanda na yi karo da shi, kuma ya riƙe ni ban faɗi ba.

Haɗe fiska nayi na ce, "Allah ya isa na, hannuna da ka taɓa."

Maimakon na ga ya ɓata rai, ya fara ci mini mutunci yan da ya saba, sai naga saɓanin haka, murmushi yake sakar mini tare da faɗin, "Afuwan gimbiyata."

Ƙara kallonsa nayi dan na tabbatar da shi ya faɗi abin da kunnena ya jiye mini, murmushi ya sakar mini tare da ɗaga gira guda.

"Hmmn!" Na faÉ—a tare da jan dogon staki, fiskana a haÉ—e na ce, "let me have my way."

Murmushi yayi ya ce, "faÉ—a da hausa gimbiya."

Wani bansan harara na aika masa da shi, sannan na ce idan ya na yiwa Allah da Manzonsa ya bar mana ƙofan gidan mu.

Ya Danish ko a jikinsa, ya ce, "Nima ya zama gidanmu ai, please Beb ki saurare ni, da farko ku yi haƙuri da abin da Umma ta yi, duk nine na ja, amma dan Allah a yafe mata, ki taya ni bai wa Mami haƙuri, Insha Allah next week zan shiga na bata haƙurin da kai na, and beb please ki yafe mini abubuwan da suka faru, ba da intention nayi ba, sharrin shaiɗan ne da kuma soyayyanki."

Maganansa dariya ya bani, amma duk da haka na maste, ko kallonsa na ƙi yi, har Ya Danish ya gama shirmen maganganun sa ya tafi ko ƙala ban ce masa ba, yana barin wajan na ja dogon staki na shige gida, ina faɗin, "Ni za'a renawa wayo ɗan iska mara kirki, in ma da wani salon ka zo to duk ina dai-dai da su."

Ya Danish cikin farin cikin ya bulbular da abin da ke ran sa ya tafi bayan ya ce mata, "ILOVE YOU BEB", ko cikin gida bai koma ba, ya ja motansa yayi gaba, shi ko haka ma Alhamdulillahi ya gode wa Allahn da ya jarabce da da soyayyanta.

Ni kuwa mita na dinga yi, har Mami ta gaji ta buge mini baki, tana tambayan menene ya faru, faɗa mata nayi, maimakon ta goyi bayana, sai naga tana murmushi kawai, ganin haka ƙara kuluwa na yi, a haka kuma da fushina nayi bacci, Allah ya so ma idan na tuno soja inajin kukan ya tsaya sai kuma dariya akan abin da ya faru ranan.

Tun daga ranan duk bayan kwana biyu sai na ga ya Danish a Mubi, kuma idan ya zo ya dinga takura mini kenan, wulaƙancin da ya mini, ba irin wan da ban rama ba, har ma da alakoro na masa, amma ko a jikinsa.

Mami ta dage da maganan aurena, yau Alhamis muna zaune, Mamina ta ci kwalliyanta, daman jiya ta yi kistonta har da ƙunshi, ba tare da ta kalleni ba ta ce, "Faɗima."

Murmushi nayi na ce, "Naam Mamina."
Chapter 53 · 0% Book details