← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 58

Sashe 13

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Abbo daman idanuwansa na kai na, kuma ko da na ɗago kai na idanuwanmu sun haɗu, kuma ina da tabbacin ya hango damuwan da ke cikinsu, ajiyan zuciya ya sauƙe kaman yanda ya ke a nawa ɓangaren, a karo na biyu ya tambaye ni me ya hanani zuwa makaranta, amma nan ɗin ma shirun na masa kawai tare da girgiza kai, ganin haka sai ya jinjina kai dan yana da tabbacin wani abun nake ɓoye masa, ko kuma ba zan iya faɗa masa ba, bai kawo komai a ransa ba kawai ya ce, "To shikkenan na fahimta Malama Faɗima, Allah rufa mana asiri duniya da lahira, Allah ya iya mana a lamuranmu, abu na gaba kuma da zan faɗa wanda shi ne babban dalilin zuwana, maganane akan musabaƙa, kinsan dai halin da ake ciki, ɗalibai masu gabatar da karatun musabaƙa anjima da zaɓansu, amma kuma da kuka same ni da maganan kuna son ku yi, sai na sama muku gurbi tunda makaranta gaba-ɗaya an sheda da irin ƙoƙarin ku da hazaƙan ku, to kina neman kawo tangarɗa a lamarin, ko kuma na ce kin riga da kin kawo, tunda hankalin hukaman makaranta ya dawo kanku, musamman ma dai ke, kuma maganan shiganku jerin masu musabaƙa anyi cancel nashi, kuma saboda rashin zuwanki, hukuman makaranta na batun sallamanki dan kina son basu kunya ko kawo musu wani naƙasu a tafiyansu, na zo ne in sanar da ke abinda ake ciki kuma makaranta ce da kanta ta turo ni, idan ba ki koma akan lokaci ba to komai na iya faruwa, da naso faɗa wa Malama Ummu-khultum ta isar miki da saƙon amma kuma sai makaranta ta bukaci da nazo da kai na."

Wani irin bugawa ƙirji na ke yi zufa na ƙeto mini, jin wai an ciremu a masu yin musabaƙa kuma makaranta na son sallamana, mu da muke ƙoƙarin haɗawa a yayemu ba da jimawa ba in Allah ya yarda, kuma dai duk da ba dan abinda zan samu zan yi musabaƙa ba, amma na gama saka wa a raina in Allah ya yarda zan yi nasara, idan Allah ya ƙira mu muka samu zuwa ƙasa mai starki na samu na yi wa mahaifiyata addu'a, ai dole abin ya dame ni, kaman zan yi kuka na ɗago kai na, muryana na rawa na ce, "Malam dan Allah ka yi haƙuri, dan darajan Annabi SAW kada ku cire mu a masu yin musabaƙan.'

Malam Abbo ajiyan zuciya ya sauƙe ya kawar da kansa daga kallona ya ce, "Ni dai ban da yacce zan yi kuma a ƙara baku wata daman, wannan ku ne ya kamata ku ƙoƙarta ku samawa kanku wata damar."

"Malam duk abinda ya kamata muyi za muyi in Allah ya yarda, amma ku yi haƙuri kada ku cire mu" ma faɗa hawaye na taruwa a idanuwana.

Numfasawa yayi ya ce, "To yanzu dai ni shawara guda zan baki, maganan zuwa makaranta duk rinsti duk wuya kada ki ce za ki aje karatu a gefe, ko me ya samu bawa ko kuma ya faru to muƙaddari ne daga Allah, ki dage da karatu sannan kije makaranta, ina tunanin hakan zai sa hukumar makaranta ta fasa abinda ta yi niya, idan aka ga kina zuwa kuma kin dage da karatun, to dole za su buƙaci yin tafiyan da ke."

Lumshe idanuwana nayi, hawaye suka gangaro akan kumatuna, ba tare da na goge su ko na hana su gangarowa ba na sauƙe ajiyan zuciya da kuma hamdala, ko babu komai zan ji sanyi a rai na idan nayi hawayen, tun ranan na kasa kuka balle hawaye har yau, kuma zuwa makaranta ya zamo mini dole, sannan dagewa da karatu ya zamo mini dole shi ma, a hankali na buɗe baki da muryana da ke rawa na ce, "Malam zan je makarantar Insha Allah, kuma zan dage sosai, mun gode Allah saka da alkairi."

Murmushi Malam Abbo ya saki wanda nima Uwar batoorl bansan na me bane, amma dai da alama da wani abun, cewa yayi, "ki mini magana da Umma zan tafi."

Tashuwa nayi na nufi ɗakin Mamina, da sallama na tura ƙofan na shiga, bayan ta amsa mini, na faɗa mata Malaminmu na mata magana zai tafi, Mami ta amsa akan tana zuwa ni kuma na juya na koma palourn, samun Malam Abbo nayi har ya miƙe ma, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai na faɗa masa tana zuwa, ban gama rufe baki ba sai ga Mamina ta iso, Malam Abbo durƙusawa yayi yana faɗa wa Mami zai tafi, ni kuma gaba nayi na fice ma a palourn gaba-ɗaya ina yabawa da girmama Mamina da Malam Abbo yayi, sosai naji daɗin yanda yayi ba tare da girman kai ba.

Mami ganin na fice a palourn sai ta buƙaci Malam Abbo ya tashi, tashuwa yayi ya zauna ita ma ta zauna, kansa a ƙasa cikin ládabi ya ce, "Umma mun gama magana da Malama Faɗima, kuma nayi duk abinda ya dace wanda nasan zai sa ta dawo normal, Insha Allah ina da tabbacin har makarantar bokon za taje."

Mami farinciki kaman tayi yaya, tana murmushi da jinjina ƙoƙarin Malam Abbo ta ce, "Nagode sosai Malam, Allah saka da alkairi, Allah maka albarka, Nagode sosai."

Malam Abbo miƙewa yayi bayan sun gana magana ya fice, Mami sai godiya take masa, ta miƙa masa kuɗi ma ya ƙi amsa, a stakar gidan suka same ni staye, Mami ta dubeni ta ce, "Banafsha sai ki takawa malamin naku ko."

Amsawa Mami nayi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida cike da farin ciki, ko ba komai yanzu 'yar ta za ta saki ranta, ta daina saka damuwa a ranta.

Ni kuma kaman yanda Mamina ta faɗa hakan nayi, tare muka fice da Malam Abbo a gidanmu, yana min faɗa, cewa yayi, "Malama Faɗima, komai na rayuwa da kike gani haƙuri ake yi da shi, kuma ƙoƙari ake yi wajan ganin mutum ya cinye jarabawan mahaliccinsa, saboda samun gwaggwaɓan rabo da sakamako mai kyau a duniya da kuma ranan karɓan sakamako, ita kuma jarabawa a zagaye da mu take ko ta ina, a iya karatunki nasan kin sani, ayoyi da dama na ƙur'ani sun kawo hakan, sannan akwai wasu hadisan ma da suka kawo haka, Malama Faɗima hatta rayuwa da kike gani da Allah ya mana ya kuma azurtamu da lafiya to shi ma jarabawa ne, Allah ya jarabce mu da lafiya ne dan ya ga ya za mu yi da lafiyan, aljanna za mu nema da shi ko kuwa za mu dage wajan saɓa masa ne, rashin lafiya ma jarabta ce dan ya ga mutum zai yi haƙuri ya yarda da Allah ne ya ɗaura masa cutan ko kuwa zai dinga zargin mutane akan da saka hannunsu, haka zalika akan dukiya da rashin dukiya, akan haihuwa da rashin haihuwa, akan tashuwa ka rayu da iyayenka da kuma rayuwa ba tare da su ba, haka akan aure da rashin yin aure, komai da yake zagaye da ɗan Adam na jarabta ce daga mahaliccinsa, kuma Allah na so ne mu ci wannan jarabawan, ina fatan kin fahimta kuma za ki dage wajan ganin kema kin cinye naki jarabawan?" Faɗin Malam Abbo da ya dakata da tafiya ya zuba mini idanuwansa dai-dai mun shige ƙofan gidan su Umaima, kuma cikin rashin sa'a sai ga Ya Danish a waje shi da abokinsa kasancewan yau Lahadi yana gida bai koma ba tukunna.

Ya Danish yana zaune a bayan motansa, sai abokinsa É—aya na zaune a plastic chair, da kuma Ya Farooq shima yana zaune a kujeran roba, ya Farooq É—an farin Ummu ne, kuma kusan sa'a haka suke shi da Ya Danish, shiyasa suke yawan zama tare, muddin Ya Danish na gari to za ka gansu tare da wannan abokin nasu mai suna IB.

Ya Danish tun fitowanmu idanuwansa suka sauƙa a cikin nawa, wani irin kallon banza kallon tsana yake jifana da shi, ni kuwa ganin ya zuba mana ido sai na dinga sakarwa Malam Abbo murmushi, har dai muka tsaya ɗan gaba da su kaɗan, wani kallo na yiwa Ya Danish wanda shi kaɗai yasan fassaranshi ta 'yar staman da ke tsakaninmu, sannan na mayar da hankalina kan Malam Abbo ina masa magana, Ya Danish kuwa a nasa ɓangaren wani wawan dogon staki ya ja, wanda sai da Ya Farooq da ya IB suka tambayesa menene, amma ya musu banza.

Idanuwana akan malam Abbo ina ƙayataccen murmushi na ce, "in Allah ya yarda Malam zan dage, wajan ganin na cinye tawa jarabawar, sannan na maka alƙawarin dagewa a karatu da zuwa makaranta, nagode sosai Malam, Allah ya biya ka da mafificin alkairi, Allah ya biya iyayenka da aljanna, Allah ya sa ka rabu da su lafiya nagode sosai."

Tunda na fara magana Malam Abbo ya zuba mini idanuwansa masu É—auke da sinadaran da ke saka ni jin kunya, amma duk da haka ban kawar da nawa idon ba sai ma wani murmushin da nake sakar masa, wanda duk saboda Ya Danish na daure nake yin hakan, shi kuwa Malam Abbo tuni ya susuce wajan kallona, inada tabbacin ya tafi wata duniya ta daban, ganin kaman hankalinsa ba ya wajan sai na É—an mosta yastuna a gaban idanuwansa na ce, "Malam muje ko."

Firgit Malam Abbo ya dawo daga duniyan da yake, yana mai dannewa dan kada na fahimta, ganin har yanzu da murmushi akan fiskana sai shi ma ya sakar mini tare da faÉ—in, "Malama FaÉ—ima rakiyan ya isa haka, ki juya nagode ko."

Ba tare da musu ba na gyaɗa kai tare da masa addu'an a koma lafiya na ƙara da godiya, ban juya ba sai da Malam Abbo ya juya ya fara tafiya, na ɗaga masa hannu sannan ganin ya ɓacewa ganina sai na juyo ina ta murmushi ni kaɗai, har na mance da abinda ke damuna domin kuwa nasihan Malam Abbo ya shiga jikina ba kaɗan ba.
Chapter 13 · 0% Book details