← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

General murmushi yayi tare da kashe wayansa, CAS Bunayd kuwa cikin gidansa ya koma, wanka ya kuma fesawa ya saka wani armless ɗin da 3qauter, feshe turarensa yayi ko ta ina sai ƙamshi kawai yake yi na fitan hankali, yana fitowa wasu sojoji da gudu-gudu suka ɗauko motoci kusan guda goma, CAS Bunayd kallonsu yayi ya taɓe baki fiskan nan a haɗe, kaman an haɗo baƙar hadari, da mamaki na ce ashe dai mutuncin da fara'an wa iya abokinsa ne, waɗannan sojoji Aradu suna ganin rashin mutunci wajan wannan Bunayd ɗin, cikin isa ya ce su ƙyalesa zai je shi ɗaya, amma suka ce ina, saboda baya son dogon magana da su, motan da ke tsakiya wanda ya fi ko wanne haɗuwa suka buɗe masa ya shiga, duk da gudu-gudu suka shige nasu motocin, a saba'in suka bar cikin gidan, motoci biyar a gaban nasa, biyar a bayan nasa, sai stula gudu suke a cikin garin Lagos, gudu na Allah stine uwar mai ƙarya, domin ba laifi su ma sojojin, suna fesa rashin mutuncinsu a kan kwalta, idan ka sake ka kusto gabansu to rip gare ka, dan kaman ba su da birki, ga mugun gudun stiya, shi dai CAS Bunayd yana hakimce a bayan haɗaɗdiyar motansa, sai lasta wayansa yake hankali kwance ko ɗago kai baya yi, kuma daman wannan al'adansa ne, shi abinda yake gabansa kawai yake yi, in za ka shekara staye a kansa ko a gefensa, sai ya shekara bai dago ya kalleka ba, ko kuma bai juyo ba.

Victoria Island suka nufa, nan ɗin ma anguwan wasu manyan kusoshin ƙasa ne, anguwan manyan yan kasuwa, manyan masu kuɗin ƙasa, da kuma sojoji da ƴan siyasa.

A gaban wani katafaren kantamemen gida suka buga wata mahaukaciyar horn, kaman za su tashi garin Lagos da bala'i, wannan gidan ma sojojin ne ko ta ina kaman kayan banza, ana buÉ—e musu, suka danna hancin motocinsu ciki, Masha Allah! Wannan gida ma ta haÉ—u ta tafi da zuciyata, ba dan gidan manya ba ne to da tabbas motocin CAS Bunayd ba za su samu mastugunni ba, amma da yake wannan gidan ma ya amsa sunansa, to kaman ba motoci goma sha bane suka shigo, kuma akwai wasu arnun motocin a gidan ma, waÉ—anda suke mallakin mai gidan.

Suna gama parking, wani soja ya zo da gudu ya buɗewa CAS Bunayd ƙofa tare da ƙamewa ya sara masa, amma bawan Allah sai da ya kusa mintuna biyar a cikin mota sannan ya jeho ƙafa guda a waje, can da ya gama iyayinsa sai ya fito gaba-ɗaya, wannan karon har da glass ya maƙalawa fiskansa da babu annuri, cikin isa yake takunsa na ƙasaita, hannu guda a aljihu hannu ɗaya riƙe da wayansa mai stadan gaske na yayi, ga kuma uban headphone a kunnensa, a haka ya shiga gidan da sallama kansa akan wayansa, ba ruwansa da an amsa sallaman ko ba'a amsa ba ya haura sama direct, a palourn sama ya samu General a kwance Matarsa Hajiya Huraira tana masa tausa, duk da shigowan CAS Bunayd bata bari ba, ci-gaba tayi ta aikinta tana sakarwa yaron nasu murmushi.

Waje CAS Bunayd ya samu ya zauna, cire glass nasa yayi, sannan cikin girmamawa da maganarsa ta yanga ya ce, "General barka da gida, Momsee sannu da aiki."

Hajiya Huraira wacce suke ƙira da Momsee, tana murmushi ta ce, "Yauwá, sannu Bunayd, fatan ka dawo lafiya?"

"Alhamdulillahi Momsee" ya faÉ—a yana mai É—an kishingiÉ—a.

General ya ce, "My Man, yaushe ne ka dawo?"

Cikin shagwaɓa kaman ƙaramin yaro ya ce, "Yau na dawo."

"Good! Sannu da hanya Man, wai me yasa baka son zama anan gidan ne? Ka yi gida a gefe ka koma can da zama menene damuwanka? Ko dai rashin ji kake shukawa?" FaÉ—in General idanuwansa akan Bunayd.

CAS Bunayd shafa kiston kansa yayi dan ya fahimci nufin General na cewa wai ko rashin ji yake shukawa, murmushi yayi mai stadan gaske ya ce, "General ni ba wani abinda nake shukawa, just small boy like me ai babu abinda zan iya yi, ba mace ko É—aya a gidana, kuma wasu ayyuka nake yi, amma zan dawo, nima ba daÉ—in zaman can É—in nake ji ba."

General yana kallon Bunayd cikin soyayyan da yake masa ya ce, "Kai ne small boy? Anyway shikkenan, I trust you, nasan ba za ka shuka rashin ji ba, yanzu dai ko baka kammala aikin ba, ba inda za ka koma, ka dawo kenan, bana son zamanka kai kaÉ—ai a gida."

Haka ya ƙara marairaicewa kaman ɗan goye ya ce, "General zan dawo da gaske fa", magiya Bunayd ya dinga yi da gaske, sannan General ya amince akan idan ya gama ya dawo, sosai General yake ƙaunan Bunayd, shi ya sakalta shi, ya shagwaɓa shi.

General ya ce, "To kai ka ce small boy ne kai, yaya kuma ya ce aure za kayi, dan kada ka shuka rashin ji, dan nasan dai ba lalacewa za ka yi ba, sai dai shuka rashin ji É—in."

Murmushi CAS Bunayd yayi ya ce, "General ka ƙyale Sir, ni har yanzu gaskiya banga wacce ta mini ba."

General ya ce, "Amma dai kasan halin yaya ba, staff zai aura maka wata, gwanda kawai ka nemi nistasttiya tun wuri ku dai-daita, ni bana son a maka abinda baka so."

CAS Bunayd ɓata fiska yayi ya ce, "General to gaskiya da ace Sir yasan irin macen da nake so, ai ba mastala ya zaɓa mini, amma ga shi kai ma da muke tare kana cewa nistasttiya balle kuma Sir, ai sai ya ce shi kuma kamila mai kwana da hijabi tana guma Palace zai nema mini, gaskiya a barni na nemi irin wacce nake so."

General cikin soyayya da lallashi ya ce, "To wacce irin mace kake so my Man? Ka ce ba nistasttiya ba, kuma ba kamila ba, Ustaziya kake so kenan?"

CAS Bunayd ji yake kaman ya ƙwala ihu dan taƙaici, kaman zai yi kuka ya ce, "General ni ko ɗaya ba su nake so ba."

"To wai wacce irin mace kake so?"

"Gaskiya General ni bana son mata masu saka hijabin nan, ƴan ƙauye ne, gaskiya ni banason nistasttiyan mace."

Da mamaki General da Hajiya Huraira (Momsee), suke kallon Bunayd, Momsee ce ta ce, "To Bunayd wace irin mace kake so? Kowa na fatan samun nistasttiyan mace amma ka ce ba haka ba."

"Momsee ni nafison mace wacce ta waye tasan rayuwa, tasan duniya, amma nistatststun nan basu san kan rayuwa ba, basa bada Palace yanda ya kamata."

General ya ce, "shi kuma Palace É—in menene? Ai mace nistasttiya ita ce jin daÉ—in duniya."

"General ni nafison wacce take nan tantiriya-tantiriya, ko gantalalliya-gantalalliya haka nan, ko stagera-tsagera ko kuma wayayyiya wacce dai ba kamila ba, wacce dai tasan rayuwa, nistasttiyan nan cutan ta zan yi, kaga ni ba nistastte bane, kuma ni Soja ne, nistasttiya ai sai malamin islamiyya, ustazu."

Momsee dariya kawai ta yi, shi kuwa General sake baki yayi ganin ikon Allah, ganin da gaske CAS Bunayd ya dage shi iya gaskiyansa yake faÉ—a, abinda yake so yake faÉ—a, ikon Allah, da mamaki ya ce, "ubanwa ya ce maka kai ba nistastte bane?"

Bunayd ya ce, "Abeed ne ya faÉ—a General."

Girgiza kai kawai General yayi, tunda yasan Abeed kuma ya san waye Bunayd ɗin da rashin jin sa, kawai soyayyan da yake masa ya saka yake lallaɓasa, rarrashinsa ya dinga yi amma ya dage firr shi baya son nistasttiya, in kuma Alhaji zai sama masa wacce yake so, to ya basa zaɓi, shi normal ne kawai, ai damuwansu yayi aure ne, to zai yi kawai a samu kalar wacce yake so, General dai kama haɓa yayi yana ganin ikon Allah, amma tunda dai ya amince zai yi auren da sauƙi, kuma daman hakan na ɗaya daga cikin abinda yasa yake son sa sosai, Bunayd baya musu da su ko kaɗan, kuma yana jin maganansu yana musu biyayya, halayyansa masu kyau ne, dan ya fi ƙannensa har da matan jin magana, shi dai bar shi da abin raha, ita kuwa Momsee ba abinda take yi sai dariya, ganin Bunayd ya girma da gaske amma kuma ƙuruciya na damunsa, dan idan ba ƙuruciya ba mutun ya dage baya son kamilar mace saliha, ya ce sai gantalalliya.

General ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, "To daman ma babban abinda ya sa na ƙira ka, ba akan ka dawo bane, dan nasan muddin baka yi niyan dawowa ba tuni ka kanainaye ni da magana na ƙyaleka, ga shi kuma na haƙura dan dole, Man kai kam ai mace bata isa ta maka daɗin baki ba, Allah shirya mana kai."

CAS Bunayd na murmushi ya ce, "Ameen Ya Rabbi my General."

General sai da ya dara kawai ya girgiza kai ya ce, "akan maganan ƙannenka ne, da farko Suhail na kai sa makarantar sojoji shi ma ya gado ni, amma yaron nan ya gudo haka na kylesa, aka tura sa Turkish ɗin da yake so, ya karanto duk shirmen da yaga dama, yanzu kuma Nabeel ya ɗau ƙafansa, dan tsabar yaran nan duk sun mai da ni abin wasansu wai shi ɗin ma yaro da shi yana cewa ba zai je ba, baya so, bansan mene mastalansu da aikin Soja ba, yara duk basa kishin kansu balle ƙasar su, ba za su tsaya su kare ƙasar su yanda muke fafatawa ba."

Bunayd murmushi kawai yayi ya ce, "General wallahi ba ko kaffara, Suhail ne ya zuga Nabeel wai wahala ake, amma ba komai zan yi wa Nabeel É—in magana."

"Good boy! Allah muku albarka duka my Man, idan kuma yaƙi ji ka kai sa guard room ba ruwana" faɗin General yana murmushi.

CAS Bunayd ya ce, "Ba za'a je ga guard room ba ma General."

Dariya General yayi ya ce, "Daman nasan haka za ka ce ai, tunda ka fi kowa son ƙanne a duniya, duk kai ma ka sakalta yaran nan, amma dai tunda suna jin magananka da sauƙi, ni na rasa ya ake suke storonka ma yanda kake buɗe musu haƙorankan nan."

Murmushi kawai CAS Bunayd yayi bai ce komai ba, ya shafa kistonsa yana lumshe idanuwansa kaman mai jin bacci.
Chapter 20 · 0% Book details