← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 58

Sashe 50

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bunayd sun isa Kano da wuri wajajen ƙarfe biyu na rana, komai da yake ready sun wuce asibitin da shi, kuma an ƙara yi masa abin da ya kamata, sannan Bunayd ya bar asibitin ya koma gidansa dan shirin zuwa ɗaurin aure.

Babban gidansa da ke anguwan Dala GRA ya nufa, gida ne haɗaɗɗe har ya gaji da haɗuwa fan's, wanka yayi da wur-wuri ya shirya cikin manyan kayansa, idan ka kallesa ka ɗauka shi ne angon ma, masallacin da za'a ɗaura auren a can ya nufa, yana zuwa kuwa ana idar da sallah aka gabatar da ɗaurin aure, da yake ya faɗawa iyayen Abeed, kuma su ma sun yi wa iyayen Nusaiba bayani, duk an amince ba komai tun da kowa yasan ƙaddara, balle ma ga soja, kuma yarinya ta ce tana son mijinta a haka.

An É—aura auren CAPTAIN ABEED TASI'U ADAMU & NUSAIBA YAKUBU NASHE akan sadaki Naira dubu É—ari biyu, bayan É—aurin aure kuma, Bunayd da sauran abokanaye duk suka yi abinda ya kamata.

Abeed kuwa a asibiti ana gama ɗaurin aure ya farka, ko da Bunayd ya zo wajansa sai da ya saka shi ya kira masa Amaryansa Nusaiba, Bunayd dariya ya dinga yi wa Abeed ya ce, "stautsayi ta rista da Ango mai jiran Palace, sorry Captain Abeed, amma kai ma ai da nine kai ba zan je wannan aikin ba atou, haka kawai ga shi an maka baƙin cikin yin mopping na Palace from corner to corner, kai gaskiya ma dole kamilarka ta renaka, yo baka goge mata hadda a take ba ai ba wani suna mai daɗi da za'a ƙara maka, kai in kana son ganin asalin soyayya da girma a wajan Amarya to a ranan da aka kai ta, kada ka bari ta kwana lafiya, balle ma ta kai Sunday, a ranan Friday ka sha hidima ka yi disko, ka kwaso shoki, ka yi har da Apro dance duka a Palace, nan za ka ga wani irin ruwan ƙauna, ai ba abinda ke saita mace ka ga ta ji duniya babu ya kai irin Dragon, ka bata blessfull milk ka kwashi gifted water, ni ana fara maganan aure na ko nan da can ba zan je ba, ƙarshe ma General ne zai je ya ɗauro auren a kawo mini Amaryata, yanzu dai dole ku cinye wata guda babu ko romancigin, ai hidiman cherge a Palace ta wuce Friday to duk buge ce, dan a ranar ma ake son ka jefa ƙwallo a raga, za ka ga albarkataccen baby da za'a haifa maka, wanda ya amsa sunan sa ɗan halak, ranan da aka biya sadaki da ɗuminsa aka same shi, tun sadaki bata huce ba ta salafce" Bunayd ya ƙarisa zancen yana dariya kaman ba lafiya ba, kana gani kasan dariyan mugunta ce.

Abeed saboda haushi ji yayi ma ya warke, hararan Bunayd yayi ya ce, "ɗan jagaliyan musulmi, bakinka ya sari ɗanyen kashi, in Allah ya yarda zuwa Sunday na warke, wato tun da baka ƙaunata dole ka mini fatan na kai 1 month a kwance, kuma Allah ya kai mu lokacin naka auren, za mu ga ko za ka gujewa abin da Allah ya hukunta" ya ƙarishe maganan tare da yin ƙwafa, dan ko shi a ransa ba haka ya so ba, irin soyayyan da suke da Nusaibarsa, irin burin da suka ci wa wannan rana ai ba haka ba, amma ba yanda mutum ya iya da ƙaddaran Ubangiji.

ACM Bunayd dariyansa ya ci gaba da yi, har da wata English music yake na babu hidimar Palace, sai da ya stagaita dariyan ya ce, "Amma ai da sauƙi tun da raunin ba'a Dragon ba ce, kawai dai tun da a cinya ne ba buga harka yan da ya kamata, sai dai a lallaɓa, ka ga fa'idan auren gantalalliya da nake faɗa maka ko, yanzu da ace ba kamila saliha ka aura ba, ai ba ka da mastalan komai tun da Dragon na lafiya, da kana kwance za ta gabatar da hidima ta yi su doro bucci, su gwara-gwara, a gwargwarawa Dragon chergy."

Abeed mai da kansa yayi ya kwanta yana cewa, "Sai kuma ka yi ai, ni dai idan ba za ka ƙira mini ita ba, miƙo mini wayana."

Bunayd yana murmushi ya miƙa wa Abeed wayansa, bayan ya masa dialing na layin Nusaiba Amarya.

Ƙira na shiga, kaman daman Amarya jira take, ɗauka tayi cikin farin ciki da ƙaunar mijinta ta ce, "Alhamdulillahi ala kulli halin na zama mallakin My Captain, sai addu'an Allah ba wa mijina lafiya."

Lumshe ido Abeed yayi yana jin wani irin abu, a hankali ya ce, "babyloff am so sorry."

Guntun murmushi Nusaiba ta yi ta ce, "sorry for what Captain? Ƙaddara ce, kuma da yardan Allah mun ma cinye ta, Allah baka lafiya, nikam lada kwasha-kwasha, tun yanzu zan fara cika bankin lada na, ana wastewa zan zo nayi jinyan Captain na."

Murmushi Abeed yayi ya ce, "Masha Allah! Alhamdulillahi! Na gode wa Allah da ya mallaka mini ke, tun yanzu ma indai aljannarki a ƙasan ƙafata take, to na ɗage miki, lada kam kina kan samu tun da aka ɗaura albarka nake saka miki, saura albarkan bed kawai."

Cikin jin kunya Nusaiba ta dinga amsawa Abeed, suka yi wayansu cikin farin ciki, suna gamawa Abeed ko kallon Bunayd da ke masa dariya, ya ƙi yi, gyara kwanciyansa yayi yana tunanin Nusaibarsa, ba dan ciwo ba ai da zuwa yanzu ko ɗan taɓe-tabe haka da ya yi.

Bunayd miƙewa yayi ya ce, "Captain kar ka saka ƴar mutane a corner, ka bari ciwonka ya warke, yau da gobe duk ɗaya ne", yana gama magana ya fice.

Ƙwafa Abeed yayi ya ce, "ɗan renin hankali, ana sallamana a ranan ba ɗaga ƙafa wallahi, kuma kai ma lokacinka na zuwa zan rama ne ai.

ACM Bunayd komawa gidansa yayi ya shirya, daman freind's na su suna gidan sa, suna jira a kai Amarya kamun su wuce, dan dinnern da za'a yi an mayar da shi sai idan Abeed ya warke, sai yayi fixing time ayi, shi yayi arranging na komai, aka ɗau Amarya aka kai ta gidanta, duk wani abun buƙata da za'a yi Bunayd ake tambaya, ya tsaya ciff akan komai, har aka yi aka waste ranan Lahadi.

Abeed ya ce Nusaiba ta kwana a gida tukunna ta huta, sai washegari litinin ta zo, amma sam firr ta ƙi yarda, dan haka shiryawa tayi Bunayd ya je ya ɗauko ta ya kawo ta asibitin, kamun isowansu kuma tuni Abeed yayi wanka ya yi sharr abin sa, kaman ba mai jinya ba, da yake ƙafan da sauƙi ma.

Bayan sun shigo ɗakin, tuni Abeed ya buɗe hannu wa Amaryansa, Nusaiba sunne kai tayi wai tana kunyan Bunayd, shi kuwa taɓe baki yayi ya ce, "kin yi a iska Amarya, kunyan mara kunya asara ne, yi abunki lokacinki ne, mu idan namu ta zo har da cherger Palace idan ta kama zan yi a gabanku ba ruwana" ya faɗa yana ɗage kafaɗansa, irin ko a jikinsa.

Nusaiba Amarya murmushi kawai ta yi, ta koma wajan mijinta ta zauna, amma bata yi hugging nasa ba, Abeed hararan Bunayd yayi ya ce, "Sai a bamu waje ai, kasan yanzu iyali gare ni, ni ba gauro ba."

Murmushi Bunayd yayi ya ce, "Ni ba zan ce komai ba, amma dai ka bi a dai-dai, dai-dai kaman mai slow motion, dan wani ciwon baya yake komawa idan aka charger Palace bai warke ba", yana gama magana ya fice kaman ba shi yayi maganan ba.

Abeed murmushi kawai yayi, tare da jawo Nusaiba jikinsa, wani irin ajiyan zuciya suka sauƙe a take, nan suka fara kallon juna cikin soyayya, har Nusaiba ta gaji ta kawar da kan ta, kalaman soyayya suka fara ɓari, daga ƙarshe Abeed haɗe bakinsu yayi, yana mata wani irin kiss mai isar da saƙon zuciya zuwa ga masoyi.

Sai da suka yi sati guda a asibiti sannan aka sallamesu, kuma kullum Nusaiba tana can, wanka kawai da girki ke kai ta gida, duk da ma Bunayd na yawan musu takeaway, ga kuma wanda ake kawowa daga gidan iyayen Abeed, da nata iyayen, Abeed kullum sai yayi kiss amma bai taɓa wuce kiss ba, yana daurewa ko yayi yunƙurin wuce kiss sai ya fasa, ya ce sai an sallamesi.

Ko da aka sallamesu Bunayd hidima bai ƙare ba, shi ya kai su gidan su, ko da Nusaiba ta shige ciki, tsayar da Abeed yayi ya ce, "Abeed ka bi a slow motion fa, serious ciwo bai cika son ana charging ba, ba ta warkewa da wuri."

Abeed hararan Bunayd yayi ya ce, "Idan kai ka biyan mini sadaki to sai ka hana", yana faÉ—a yayi gaba.

Bunayd ɗage kafaɗa yayi, ya wuce abinsa yana faɗin, shi ya gama nasa yayi duk abin da ya kamata, idan ya jawo wani abun ma su suka jiyo, amma gefe guda na zuciyarsa na cewa, "faɗa gaskiya ACM ko kai ne ba za ka ƙyale ba, sabuwar Amarya no be play", murmushi kawai yayi ya ci-gaba da driving abin sa, gidan Papi ya nufa ba gidansa ba.

Abeed yana shiga gida ya saki hamdala, ganin Nusaiba na gyare-gyare, ƙarisa wa yayi tare da rungumeta ta baya, a hankali ya kai hannayensa kan na shanunta, wani irin gigitaccen ajiyan zuciya ya sauƙe, a hankali ya ce, "My life saver's, babyloff bar aikin nan, ladansa kaɗan ne, muje ki yi mai lada da yawa."

Nusaiba ajiyan zuciya ita ma ta sauƙe, ta ce, "My Captain ba ka warke ba fa."

Abeed shi kaɗansa a zuciyansa ya ce, "Ashe gaskiyan ACM Bunayd, wato dai har faɗa mini take ban warke ba, ta rena Dragon, shikkenan ai za ta same sa yanzu kuwa", yana gama zancensa a zuciya, ya mata dabara, yana tattaɓeta har ya ja ta suka yi ɗaki, gaba-ɗaya Abeed notin kam sa ya warware.
Chapter 50 · 0% Book details