← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 58

Sashe 30

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umaima ta ce, "Abbaa wai fa Banafsha ce tun ranan asabar rabona da ita, ranan Lahadi har yau litin kwata-kwata bata je boko ba, kuma ba ta je tahfiz ba, shi ne nace zan je dubota na faÉ—awa Ummu, har ta barni naje kuma ta ce za ta faÉ—a maka, amma sai Umma ta hanani, kuma ta ce idan na tafi makaranta na bi gidansu bata yafe mini ba.......", Umaima ta faÉ—awa Abbaa duk yanda aka yi, kaman za ta yi kuka."

Girgiza kai Abbaa yayi ya ce, "Mai hali ba ya fasa halinsa, Allah ya kyauta, ki yi haƙuri ko, yanzu ki je ki jirani ina zuwa sai mu shiga gidan nasu tare, Allah ya sa tana lafiya, ki ƙyale Ummanki kar ki ce mata komai, duk abinda dai ta ce miki kiyi ko kar kiyi, idan bai saɓa addini ba kiji magananta, ita mahaifiyarki ce, kuma sai an anrabu da iyaye lafiya ake dacewa."

Umaima jinjina kai tayi sannan ta tashi ta fice ta koma cikin gida, Abbaa kuwa wasta ruwa yayi ya saka jallabiyansa ya feshe jikinsa da turare sannan ya shiga cikin gidan, duk matan sannu suka masa ya amsa, sannan ya ƙira Umaima ya saka ta a gaba suka fice, suka nufi gidansu Banafsha.

Ɓangaren Banafsha haka ta kwana ranan Lahadi da ciwonta, Mami sai tattalinta take yi, Alhaji ma dai tausayin yarinyar yake yi, har washe gari Litinin haka suka wuni, Banafsha zuciyanta cike da kewan Umaimatynta ga shi bata shigo ta duba ta ba, amma ta mata uzuri tasan ba zai wuce ya Danish ba ne ya hanata zuwa, sai bayan azahar Alhaji ya sallami Mami, bayan ya ajiye mata kuɗi masu yawa dan jinyan Banafsha, Allah ƙara sauƙi ya mata sannan ya fito ya shige motansa, ya nufi Yola daga nan kuma sai Kano Kanawan dabo.

Sai da Mami tayi Magrib sannan ta Lallaɓa Banafsha ta yi wankanta da kanta a daddafe ta gyara jikinta chass da ita, abinci ma da lallami ta ci Mami na bata a baki, ana ƙiran isha'i Mami taje tayi sallah, Banafsha kuma tana kwance a palourn idanuwanta akan TV amma hankalinta ba ya kan TV, hankalinta na can yana tunano mata Malam Abbo nata, har Mami ta idar ta fito bata sani ba, sai da ta taɓa ta ta ce, "shalelen Mami me kike tunani haka?"

Murmushi na sakarwa Mamina na ƙarfin hali na ce, "bakomai Mamina."

Mami ta ce, "Ban yarda ba, amma dai ina son ki daina saka damuwa a ranki, komai na duniya mai wucewa ne, watarana ciwon nan zai barki kaman ba kiyi ba, Allah dai ya baki miji nagari Banafsha wanda zai kula mini da ke sosai fiye da ni."

Ajiyan zuciya kawai na sauƙe tuna maganganun Malam Abbo, kawar da tunanin nayi tunda nasan ba mai yiwuwa bane na ce, "Mamina bansan me ya hana Umaima shigowa ba kwata-kwata, Allah ya sa ita ma lafiya."

Murmushi Mami tayi ta ce, "Insha Allah! Lafiya lau take, may be wani abun ne, karki damu za ta shigo, kinsan dai Umaima na ƙaunarki."

Murmushin nima na yi da na tuno Umaima, na yi shiru tare da É—aura kai na a cinyan Mamina da ta sha nata wankan muna kallo, ba jimawa kuwa muka jiyo sallamana Umaima, daga ni har Mamina da murmushi muka amsa, hannuwana na buÉ—e na ce, "oyoyo Umaimatyna."

Umaima rungumeni ta yi ta ce, "afuwan masoyiya."

Hararanta nayi na ce, "Na janye oyoyon ma fushi nake da ke."

Umaima gaishe da Mami tayi ta ce, "Tare Da Abbaa muke Mami."

Washe baki Mami tayi ta ce, "To shi ne kika bar Abbaan naku a waje Umaima saboda yaranta? Ki ce ya shigo mana."

Umaima miƙewa tayi ta fice, tana murmushi ta ce, "Abba ka shigo inji Maminmu."

Abbaa na murmushi ya biyo Umaima da sallama suka shigo, duk amsawa muka yi, na miƙe daga kwanciyan da nayi ina murna na ce, "Sannu da shigowa Abbaanmu."

Murmushi shi ma Abbaa yayi ya ce, "Sannu FaÉ—ima."

Mamina da mayafinta ita ma ta yiwa Abbaa sannu da shigowa ya amsa yana fara'a bayan ya zauna, gaishe da Abbaa nayi ya amsa, sannan na miƙe cikin dauriya, muka shige ɗakina da Umaima muka bar Abbaa da Mamina a palourn.

Muna shiga É—aki Umaima ta ce, "ki yafe mini masoyiya, na yi kewanki sosai."

Murmushi na sakar mata na ce, "Nima haka Umaimatyna, wallahi kekam marana ke ciwo tun ranan asabar da dare shiyasa, kuma nasan ba zai wuce ya Danish ne ya hanaki shigowa ba, bakomai wallahi, ya karatu? Fatan dai ba'a ba da assignment ko presentation ba? Tahfiz ma normal ko?"

Umaima murmushi tayi ta ce, "Nasan ai babu dalili ba za ki ƙi zuwa makaranta ba, mayyar karatu, kina fama da kanki kina tambayan wani presentation ɗin buhun uba, ni fa na stani presentation ɗin nan wallahi, amma normal ba'a ba da komai ba, tahfiz ma lafiya, Malam Abbo ya ce na ce yana gaisheki kuma yayi kewanki" ta faɗa tana kyalkyalewa da dariya.

Murmushin yaƙe kawai nayi a nawa ɓangaren na ce, "Masha Allah! Ina amsawa, amma tunda ya Danish ya koma jiya Sunday, me ya hanaki shigowa da safe yau Monday?"

Tura baki Umaima tayi ta faÉ—a mini yanda suka yi da Umma, murmushi kawai na kuma yi na ce, "Allah ya kyauta, bakomai, Allah raba mu da su lafiya."

"Ameen masoyiya Banafsha" faÉ—in Umaima tana kwanciya a kan gadon."

Wani abu na faɗa mini na faɗawa Umaima yanda muka yi da Malam Abbo, amma wani abu na ce mini a'a, sai kawai na ƙyale nayi shiru, nima kwanciyan nayi, muna hiranmu da yake ciwon maran da sauƙi.

Mamina bayan mun shige É—aki sai ta kawo wa Abbaa ruwa, bayan ya sha suka gaisa, ya ce, "kwana biyu bana ganin giftawan FaÉ—ima fatan dai lafiya?"

Mami ta ce, "Lafiya Alhamdulillahi Abbaansu, dama bata ji dad'i bane amma da sauƙi."

"To Masha Allah! Haka ake so, Allah ƙara afuwa, Umaima duk ta bi ta ishi mutane da rigima shi ne nace bari mu taho tare ma."

Mami dariya ta ɗan yi ta ce, "Yaran nan ai rigimansu ya fi ƙarfinsu, ita Banafsha ma tana kwance tana fama amma sai mita take wai Umaima bata shigo ba yanzu ma mun gama maganan kenan sai ga sallamanta."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Masha Allah! Ai haka ake so, Allah ƙara haɗa kawunansu, kinga sai a bar miki su ki haɗa duka biyu."

Mami ta ce, "Waii! Wane ni, ai Ummu ba za ta bar mini yarinyarta ba, da dai za'a ce a haÉ—a mata su ne ita za ta yarda."

Dariya Abbaa yayi suka ɗan taɓa hira da Mami sosai da yake daman can sun ɗan mutunci, Abbaa mutum ne da bai da damuwa sam-sam, da yayi tunanin baje wa Mami sirrin ƙalbinsa amma sai ya fasa ya bari zuwa gobe, tunda yanzu dubiyan Banafsha suka zo.

Sai da suka ɗan ɗau lokaci sannan Abbaa yayi ƙiran Umaima ta zo su koma, amma rigima ta saka ita za ta kwana, ba musu Abbaa ya ce su kwana lafiya ya juya yayi tafiyansa bayan sun yi sai da safe da Mami, Umaima da farinciki suka fito da Banafsha suna kallo duka da Mami har dare tayi suka wuce suka kwanta, Mami ma tayi nata ɗakin ta kira Alhajinta suna wayansu cikin soyayya tana masa sannu da hanya dan ya koma gida.

Abbaa yana komawa dai Umma sai zubawa bayansa ido ta ke ta ga ɓullowan Umaima amma shiru, daganan ya fahimci inda suka je, wato Umaima faɗawa mahaifinta tayi shi ne suka je tare, daman mai neman kuka ne aka jefe sa da kashin akuya, ya ce zai auro karuwa ga shi ya samu daman zuwa zance ma dan cin fuska, ƙwafa Umma ta yi ta ce, "Idan na kamaki Umaima sai ɗan buzunki."

Ummu kuwa ta tambayi ina Umaima ya faɗa mata ya baro ta gidansu Faɗima, Ummu ta tambayi ya jikin nata, ya amsa da sauƙi, ta ce ita ma gobe za ta je dubo ta, Abbaa ya ce, "Ba damuwa Allah ya kai mu, Kinga sai ki raka ni zance mu dai-daita, tasan da amincewnki, dan inaga idan ba ki ce kin amince ba, zai yi wuya ta yarda saboda kar ta ci amanan ƙawance."

Dariya Ummu tayi ta ce, "Allah ya kai mu Abbaansu."

Sai da safe ya yiwa Ummu ya wuce É—akin Umma da yake ita ce da girki.

Washe-gari da safe Umaima daga gidan Mami ta shirya ta je tahfiz, bayan anyi karatu an tashi Malam Abbo ya kuma tambayanta, ta faɗa masa bata jin daɗi ne amma da sauƙi, hamdala yayi tare da yi mata addu'an samun sauƙi, sai yanzu hankalinsa ya kwanta, kuma yana kan lissafi sati guda ranan asabar nayi zai koma ya kuma jin hukuncin da ta yanke, Umaima kuwa tana dawowa ta kuma shiryawa daga gidan Mami ta wuce school ta saka uniform na Banafsha, ko da ta dawo bata tafi gida ba har sai da Ummu ta shigo, bayan sun gaisa da Mami ta tambayi jikin Banafsha Mami ta amsa da sauƙi, sannan ta saka Umaima a gaba suka koma gida, bata haɗu da Umma ba daga nan ta shirya ta koma tahfiz na yamma.

Abbaa yau ma bayan ya dawo ya shirya tsaff ya nufi gidan Mami dan ya sanar da ita abinda ke ransa.

Alhaji Mukhtar ya koma gida lafiya, ya samu Hajiya ta tafi Dubai akan business nata, gaba-ɗaya ya ji ba daɗi amma yayi haƙuri yana addu'an Allah sa ta gyara halinta, Allah kuma ya mallaka masa Ramla.

Yana zaune a palourn sama yana ayyukansa a system nasa, Majeeder ta shigo da sallama, amsawa yayi yana murmushi ya ce, "zauna Maman babanta."

Majeeder zama tayi ta gaishe da Alhaji sannan cikin shagwaɓa ta ce, "Papi ni wallahi na gaji, gida kullum shiru, dan Allah nima a mayar da ni gidan Affa General."
Chapter 30 · 0% Book details