← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 58

Sashe 52

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mami ajiyan zuciya ta sauƙe cikin duba lamarin Maman Kabeer, dan ba za ta yarda Banafsha tayi aure a irin wannan gida ba, ita ma babba an yi ƙoƙarin kasheta balle kuma Banafsha yarinya, duk da dai yaron na ƙaunarta(kunsan Mami bata san abin da ke faruwa ba, duka wannan staman stakanin Banafsha da Danish bata da labari), amma ba za ta iya ba, dan haka duban Abbaa ta yi ta ce, "afuwan Abbaan yara, amma magana ta gaskiya Faɗima tana da manemi, wanda zuwa yanzu izini kawai yake jira ya turo manyansa a yi maganan auren su, bai kamata nima duk da ina mace ba, amma na zama mai magana biyu, kuma dai nema cikin nema ko a addinan ce babu kyau."

Abbaa kallon Mami yake kaman ya ƙwala ihu, ya ce, "sosaima Hajiya Ramla, nema, cikin nema babu kyau, dan haka in Allah ya yarda zan yi ƙoƙari na basa haƙuri ya nemi wata, amma nima a duba tawa buƙatan, ina matuƙar ƙaunarki Hajiya Ramla, a taimake ni, idan ban same ki ba akwai mastala babba ma kuwa."

Furucin Abbaa na idan bai sameta ba akwai mastala babba, dariya ya bata, dan haka ta maste dariyanta, ta murmusa kawai, a ranta mamaki take irin na halin maza, wato manya da yara duk daɗin baki ta cika su, namiji ya dage da idan bai sameki ba kaza-kaza, amma abu mai wuyan ki amince ne ayi auren, shikkenan kin zama permanent kuma sai haƙuri, idan ba ki yi sa'a ba baƙin cikin yau daban na gobe daban, to dai Allah kyauta ya kuma haɗa kowa da sa'ar sa yayi dacen samun na gari, amma sam-sam halin wasu mazan bai haɗu ba, duk da wasu matan su suke nemawa kan su irin wannan rayuwan, Allah kyauta kawai.
Mami murmushi tayi ta ce, "Alhaji ka yi haƙuri, amma dai ni abinda ya dame ni yanzu shi ne ka dawo da Maman Kabeer."

Abbaa kallon Mami yayi cikin ido ya ce, "kin tabbata idan ta dawo za ki amince mini ki aure ni?"

Murmusawa Mami tayi ta ce, "ban yi alƙawari ba, sai dai shi Danish zai iya zuwa wajan ita Faɗima, idan sun dai-daita taga shi ya fi mata, to shikkenan Allah sanya alkairi, dan abin da yaro ke so shi za mu masa."

Abbaa sosai wannan amsa dangane da Danish ya masa daÉ—i, dan haka ya sa a rai shi ma zai ci-gaba da zuwa yin magiya, har Allah ya sa ta amince dan abin zai fi ba da armashi.

Bayan sun gama hiransu, sallama suka yi, Abbaa ya tashi yayi tafiyansa, Mami dai duniyan tunani ta faɗa, juya abubuwa da dama take a ranta, ƙiran wayan da ya shigo mata ne ya kaste mata tunanin, ganin mai kira sai ta saki murmushi ta ɗauka, cikin zazzaƙar muryanta ta ce, "Alhaji bar ka da war haka."

Alhaji Mukhtar a ɗaya ɓangaren shi ma yana murmushinsa ya ce, "Barka dai masoyiya ta, fatan kina lafiya، ya kuma yarinyata Banafsha take?"

"Duk muna nan lafiya yallaɓoi, ya ƙasar mutane?" Faɗin Mami.

Alhaji cewa yayi, "Lafiya Alhamdulillahi! Ga mu cikin ta, sai fama nake da kewanki, yanzu badan-badan ba ai da kuɗin jirgi zan miki ki biyo ni, ko kuma ma na sakoki a gaba mu taho tare, ga shi duk mutanen ƙasar masu irin kyawunki ne."

Mami cikin ƴar shagwaɓanta ta ce, "To ai ni na ɗauka ma ka dawo, sai naga ba layin Nigeria ba ne, nima kewanka nake, kwana biyu babu customers, ina ga kore su ka yi da za ka tafi, ga shi dai ni a buƙace nake, badan-badan ba nima da na biyoka."

Alhaji a nasa ɓangaren dariya yayi, dan yasan watarana Ramla na irin magannan ne da gan-gan dan ya ji haushi, amma abun da bata sani ba shi ne, wani irin soyayya yake mata wan da ko turmi da taɓarya ya kalleta da namiji, to ba zai cire masa son ta ba, shi baisan ko dan a cikin irin rayuwan ya san ta bane, amma shi a haka ma yake mugun ƙaunarta, yana kishinta ba kaɗan ba, amma a yanzu burinsa ya mallaketa sai yayi kishin yan da ya kamata, sai da ya gama dariya sannan ya ce, "Ko taurarin sun fara yin ƙasa ne mu godewa Allah, amma dai kar ki damu soon za ki ganni, suprise kawai, ki shirya ganina a ko wanni lokaci daga yanzu, tun da kina buƙatata ai zuwa ya zama dole, nima a buƙacen nake, wata biyu ba mata, ina dawowa na bai wa Hajiyata rabonta, zan wuco na zo ke ma na baki naki rabon masoyiya, duk ƙishin sai na kawar miki, ke dai ki adana mini kan ki kar na zo kuma kin riga da kin kashe ishinki ni ki kasa kashe mini nawa."

Mami murmushi tayi suka ci-gaba da wayansu cikin soyayya, ka É—auka mata da miji ne, tuni ma ta mance da wata maganan da suka yi da Abbaa, sai da suka yi sallama sannan ta ajiye wayan tare da yin murmushi, wato Alhaji Mukhtar mutum ne, tun ranan da ta yi kuka ya ce ba zai kuma mata maganan aure ba, to bai kuma ba, sai kawai Mami ta ji ya bata tausayi.

Ɓangaren Alhaji Mukhtar da ya kwashe fin wata biyu a Egypt, suna gama waya da masoyiyarsa ya murmusa tare da addu'an Allah shirya su ya dawo masa da ita hanya.

Abbaa ko da ya koma ya ƙira Danish akan zai iya zuwa wajan Banafsha, idan ta aminta da soyayyansa shikkenan sai ayi maganan aure, amma ya faɗa masa bayan shi akwai wani mai nemanta.

Danish duk da ya kwana da sanin Banafsha na da saurayi, amma ya ƙudurcewa ransa sai ya ka da saurayin nata, shi yanzu ko bin mazan da ya ce tana yi baya gani, wani mugun son ta da ƙaunarta ne yake damunsa, burinsa kawai ya mallaketa, dan haka tsaff ya shirya wannan satin ya taho Mubi.

Ɓangaren su Banafsha sun duƙufa akan karatunu musabaƙan da za su yi, gaba ɗaya yanzu ko Malam Abbo sai ya dage yake samun lokacinta, ga shi tsakaninta da Maminta indai ta mata maganan aure to ranan sai Mami ta saka ta kuka, ita ta dage sai Mami ta yi aure ita ma, ko kuwa ta koma wa danginta, sannan za ta yi aure, Mami kuma bata amince da ko ɗaya ba, ta dai dage sai Banafsha ɗin ta yi aure.

Mami bata faÉ—a wa Banafsha zuwan Abbaa ba, sannan bata mata maganan Danish ba, ta bar ta dai, idan ya mata ta ji tana son sa, to da kanta za ta yi maganan wanda take so tsakanin shi da Malam Aliyu.

Umma tana can zaune a prison har yanzu ba'a fara case nata ba, ko da Mami ta je station ɗin ma akan ta yafe mata a ƙyaleta, amma nunawa suka yi ai case ya riga da ya koma court, kuma ba daman janye ƙara, kuma yanzu a ƙarƙashin ma'aikatan prison take ba ma'aikatan station ba, dole haka Mami ta dawo ba dan ta so ba, yaya babba ko da yaji labari jinjinawa haƙuri irin na Mami yayi, Umaima ma sai ji tayi ta ƙara ƙaunar Mami, Ya Mus'ab ma har da godiya ya yiwa Mami dan sun san yanzu abin zai zo da sauƙi, tun da ta ce ta yafe, ko a court ne to abin da sauƙi.

Banafsha da ta ji wai Mami ta yafe wa Umma, sai ta samu Mami ta ce, "Mamina me yasa ba za ki bari a hukuntata ba? Yunƙurin kashe ki fa ta yi, kisa fa Mami, da yanzu na zama marainiya ban da kowa."

Murmushi Mami ta yi ta ce, "Innallaha ma'assabirin! Allah na tare da mai haƙuri Banafsha, yafe mata da nayi, sai kiga nima Allah ya dubi wasu laifukana ya yafe mini, ya kuma shirya ni ya dai-daita lamurana, Banafsha ita komai a duniya ƴar haƙuri ce idan ɗan Adam ya gane."

Kallon Mamina nayi na ce, "haƙuri Mami? Shikkenan ta yi a banza? Ni fa duk da Umman Umaimata ce amma ya kamata a hukuntata, dan wasu masu irin wannan yunƙurin su hankalta, tun da an ce gani ga wane ya isa wane storon Allah."
Chapter 52 · 0% Book details