Sashe 36
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ameen Mamina" na amsa ina murmushi, haka na gama shiri muka fice da Mami muka karya, yau ma ba iya zuwa makaranta zan yi ba Mami ta ce na bari sai wani Monday kawai, muka zauna muna hira Mami na ƙara mini faɗa.
Haka rayuwa ta dinga tafiya har aka cinye wannan sati Banafsha bata je makaranta ba, kuma sai da ta cika kwana bakwai ciff sannan ta samu sauƙi ranan Lahadi, Umaima ma duk sauran kwanakin bata je makaranta ba, kwanan su kusan huɗu a asibiti sannan aka sallamesu, har Ya Mus'ab ya zo shi ma daga Camaroon duba jikin Umaima, Ya Kabeer su ya Sadeeq su ya Farooq duka, kowa duk ya ji abinda Umma ta yi amma ba daman magana sai ido, Abbaa ma idon ya zuba dan shi ya gama ɗaukan nasa matakin, Ummu kuwa bata da bakin magana tunda gori Umma ke mata ko ta yi magana ta ce ai ba ƴar ta ba ce, haka ta dinga jinyan Umaima har ta warke, ya Danish ne kawai bai zo ba kwata-kwata ga shi har weekend ya ƙare yau Lahadi.
Æangaren Malam Abbo kuwa ganin Umaima ma ta daina zuwa makaranta kwana biyu ba ya jin halin da masoyiyarsa ke ciki, tuni hankalinsa ya tashi, haka a daddafe ya daure har sati ya cika, ranan Lahadi da yamma ya sha wankansa ya chakare ya shirya rass ya nufi gidan su Banafsha, farinciki kawai yake ciki da É—auki gani yake ba ya isa da wuri saboda yanda yake É—aukin son ganin abar Æ™aunarsa, Sayyadarsa, Malama FaÉ—ima.
â
Bunayd hutawa yayi sosai ba wanda ya san yana sashinsa a gidan, sai da General ya ƙirasa a waya sannan ya faɗa masa ai yana cikin gida ma tun da ya dawo ya taho gidan, General mayar da wuƙan yayi ya kashe wayan yana sakawa Man nasa albarka.
General layin Suhail ya kuma ƙira yana ɗauka ya rufe shi da faɗa ya ce, "Suhail ina ce dai ba gidan ubanka ba ne a Turkish ɗin nan ko? To idan ka kuskura gobe ba ka dawo ba sai na ƙwace har jarin da yayan naka ya baka, sai naga ta inda za ka zauna a ƙasar mutane babu kuɗi."
Suhail murmushi yayi da haÉ—aÉ—fiyar muryansa ya ce, "sorry General! Na gama shirin komai jirginmu da asuba zai tashi."
Ƙwafa General yayi ya ce, "Idan ma baka dawo ba kasan abinda zan iya yi, dama har yanzu ban huce da ƙin aikin soja da ka yi ba, kuma ka zo kana zuga mini yarona Nabeel."
Suhail dariya yayi ya ce, "Ni kuma ka yafe ni ne General? Ko da yake ni da nake da yaya CAS Bunayd ko General ya yafeni normal ne, daman ni yaya ne babana."
General murmushi yayi ya ce, "Za ka dawo ka same ni, daman shi yake É—aure muku wajan zama."
General haka yake da yaransa maza kaman abokanayensa, musamman CAS Bunayd, kwata-kwata General ba shi da zafi, kuma haka matar sa Hajiya Huraira.
Momsee da ke zaune a gefe dariya tayi ta ce, "Dear gaskiya yarannan su maida ka kaka."
General kansa ya shafa ya ce, "Alhamdulillahi kawai za mu ce, yara arziƙi ne tunda Allah ya bamu, dole mu jawo su jiki dan mu ji daɗin nuna musu dai-dai da ba dai-dai ba, yiwa yara zafi bai da wani fa'ida, illa ya saka yaro ba zai sake da kai ba balle kasan damuwansa, ko yayi shawara da kai, Allah dai ya musu albarka ya kare su a duk inda suke."
Da, "Ameen" Momsee ta amsa, suka cigaba da hiransu.
Bunayd yau daurewa yayi bai je ko ina ba, ba dan yaso ba sai dan General bai cika son yawan fitansa da dare sosai ba, idan ba kamawa tayi ba, amma idan ba saboda General ba sam-sam Bunayd baya son zama, shi zuwa wajan chasu a jininsa yake, ko da ba zai yi komai ba sai dai ya bawa idonsa abinci yayi catching fun's, sai da ya gama hutawansa sannan ya shigo palourn nasu na ƙasa, su Suhaila suna ganinsa suka fara washe baki, shi kuma haɗe fiska yayi dan ya san ba zai wuce su ce yawo da daren nan ba, fiska ba Rahama ya ce, "Ku kawo ƙur'anan ku."
Stuttt! Duk suka miƙe suka je suka ɗauko, General da isowansa palourn kenan murmushi yayi ya ce, "Kaman haɗa fiskan da gaske ne, ai ina ga yaran nan sun gama lashe maka zuciya, musamman Suhaila da Nabeela."
Bunayd shafa kiston kansa yayi bai ce komai ba, ya fara sauraran karatun ƙannensa sai ga Nabeel ya shigo, kallo ɗaya Bunayd ya masa tuni ya gane nufinsa, shi ma ɗauko nasa ƙur'anin yayi da littafin da suke yi na addini, Bunayd sai da ya duba karatun ƙannensa duka ya musu ƙari, sannan ya kuma suka zauna hira ana raha, bai cika magana sosai ba amma idan da ƙannensa ne kuma yana mood to duk shirmen su yana biye musu.
Da dare ya ja sosai sai General ya kora su kowa ya kwanta, da safe a fara shiri sai Kano in Allah ya yarda.
Bunayd yana komawa sashinsa sai ga ƙira, ganin mai ƙiran sai ya taɓe baki, a fili ya ce, "Yoruba people akwai reni, to nima ba zan yi attending naka ba sai gobe." Yana gama mitansa ya kashe wayansa ya kwanta.
Cikin dare ya tashi yayi nafilfiulunsa yanda ya saba, sannan ya koma ya kwanta.
Washe-gari Suhail da wuri ya iso, lokacin kuma kowa ya gama shiryawa, ba jimawa suka kamo hanyan Kano amma ta Flight, jirginsu na sauƙa motoci uku suka zo ɗaukansu daga gidan Alhaji.
Shigan su Bunayd gidan yayi dai-dai da shigowan motan Hajiya Sa'adatu da sai yau ta dawo daga inda ta je, su Suhaila duk da ba wani sake musu Hajiya Sa'adatu ke yi ba amma duk sun yi hugging nata, a yastine ta amsa, General da Momsee duk sai su suka ɗaga mata gaisuwa, sannan ta amsa a gadarance, da yake General ma da nasa part ɗin a gidan, sai suka wuce duka can, Majeeder tunda ta ji zuwansu ta fito ta rungume sister's nata mata, da kuma General da Momsee, tunda ta maƙale wa Bunayd ko mostawa zai yi tana riƙe da shi, ba ƙarya Bunayd ma yayi mugun kewan ƙanwar tasa dan ya kwana biyu bai zo ba.
Alhaji da kansa ya saka masu aiki suka kai wa su General abinci, sannan da waÉ—anda za su musu aiki har su koma.
Hajiya Sa'adatu tunda ta shige ko leƙowa bata kuma yi ba, sai kawai cin magani take yi kaman ba ɗan uwan mijinta da yaransa ba ne suka zo, kaman wasu bare daban.
SU WAYE WANNAN AHALI?
MENENE FARKON LABARINSU?
waiwaye adon tafiya, Inshà Allah a next page za mu ji taƙaitaccen tarihin wannan ahali.
Not edited again, ayi haƙuri da typing errors, Uwar batoorl jikin sai a hankali.
Masu Sharhi ina matuƙar Godiya 👠Uwar batoorl taku.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# ð˜¾ð™¤ð™¢ð™¢ð™šð™£ð™©
# ð™‡ð™žð™ 𙚠&
# ð™¨ð™ð™–ð™§ð™š
👄'YAR KARUWA👄💅
Officially
ð˜½ð™®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Hafsat Umar
Æingel kabi
Masoyiya bealkysou
Habiba muhammad Yusuf
Ameera
اللهم صلى Ùˆ سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤ðŸ¤
ðŸ…¿ï¸ 61 _ 65
ALHAJI SULAIMAN ILYASU KWALLI!
Shi ne kakan Bunayd, Sulaiman kwalli wanda aka fi ƙira da Sule kwalli shi asalin ɗan jihar Sokoto ne, a ƙaramar hukumar Binji, su biyu iyayensu suka haifa shi da ƙanwarsa mai suna Rahama, Sule da Rahama sun taso cikin gata da soyayyar iyayensu, saboda iyayensu na da rufin asiri Masha Allah, su Hausa-Fulani ne, bayan kiwon dabbobi da mahaifinsu Ilyasu ke yi har da sana'ar hannu yana yi wacce ta danganci nau'in su kwalli, Sule da Rahama duk iyayensu sun saka su a makaranta ta muhammadiya da kuma ta ilimin zamani(boko), lokacin da Sule yayi nisa a karatu sai shi ma ya ɗau sawun babansu Ilyasu kwalli ya fara sana'a irin tasa, cikin ƙanƙanin lokaci da ikon Allah shi ma ya staya da ƙafansa, a lokacin ne kuma ya samu mata mai suna Hauwa'u ƴar gidan wani babban mutum ɗan siyasa a cikin birnin Sokoto.
Bayan neman da suka yi na ɗan lokaci sai aka yi auransu, bayan biki ba jimawa Sule kwalli ya samu haɗaɗɗen gidansa a cikin birnin Sokoto, nan ya nemi da su koma duka da iyayensa amma sai iyayensa suka ƙi su sun fi son zaman Binji, haka Sule ya tattara da Amaryarsa Hauwa'u suka koma cikin birnin Sokoto da zama, sai dai sa'i zuwa lokaci su dinga kai wa iyayensa ziyara, Hauwa'u matar Sule bafulatana ce gaba da baya, kuma kyakkyawa ce ta ƙarshe ma, dan haka suna zaune lafiya da mijinta, a sanda auransu ya cika shekara a lokacin ne kuma ta haihu ɗan ta namiji santale mai matuƙar kama da mahaifinsa Sule, ranar da ya cika kwana bakwai yaro ya ci sunansa Mukhtar, kuma a wannan lokacin Rahama ƙanwar Sule ta dawo gaban Sule da zama tana kan karatunta, saboda akwai ratan shekaru sosai stakaninta da yayan nata.
Mukhtar na da shekaru biyar a duniya sai Hauwa'u ta kuma haihuwan yaronta kyakkyawan gaske namiji mai matuƙar kama da ita, kaman kakinsa ta yi, ranan bakwai yaro ya ci sunansa Sufyan, zuwa wannan lokaci Ilyasu ya manyanta sosai kuma matarsa Salamatu na fama da cutan ajali, shi kuwa Sule ya zama mai kuɗin gaske, kullum sintirin asibitin neman magani suke da mahaifiyarsa amma kwana ya riga da ya ƙare babu dabara, haka saƙon mutuwanta ya riske su, a ranan suka tattara suka tafi Binji, bayan an yi bakwai suka tattaro suka dawo, sai da aka yi arba'in sannan Ilyasu ya yarda ya dawo gidan Sule da zama.