Sashe 33
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tura baki nayi jin wai Mamina dan ni take komai, yanzu ba abun na ce idan saboda ni take wannan rayuwa mara fa'idan to ta bari na yafe ba, amma nasan sai ma Mami ta dakani duk da banda lafiya, jan bakina nayi tare da yin shiru, can na miƙe na ce, "Mami bari na sauya pad."
"To ammatan Maminta a fito lafiya", Mamina ta faÉ—a tana murmushi, ni kuma na shige É—akina cikin jin kunya.
Banafsha na shiga ɗaki bai jima ba sai ga sallaman Abbaa, Mami da fara'a ta amsa tare da masa iso, wucewa ɗaki tayi ta sako mayafi sannan ta dawo suka gaisa cikin mutunta juna, Abbaa ya tambayi jikin Banafsha, Mami tana murmushi ta ce, "Da sauƙi sosai ma, yanzu ta tashi ta shiga ɗaki."
Abbaa yana murmushi ya ce, "To Masha Allah! haka ake so."
Palourn sai ya ɗau shiru na mintuna daga Abbaa har Mami ba mai magana,can Mami sai ta miƙe tare da cewa, "Bari na ƙira maka Faɗiman tunda ta shiga ɗaki ta zauna shiru."
Abbaa na maza yayi ya daure saboda Mami sosai ta masa kwarjini, cikin jarumta ta ce, "A'a ƙyaleta ta huta, daman dai wajanki na zo."
Mami murmushi tayi tare da komawa ta zauna, bata kawo komai a ranta ba ta ce, "Allah ya sa dai ba laifi na yi ba."
Abbaa murmushi yayi ya ce, "ai kuwa laifi kika yi, irin gungumemen laifin nan, dan ko a kotu ya wuce civil case sai dai a ƙira sa da criminal case."
Mami ɗan waro ido tayi ta ce, "ahh! Ba sai an kai ga kotu ba ma, haƙuri zan bada, yanzu dai a faɗa mini laifin nawa na ji sai na bada haƙuri yanda ya kamata" ta faɗa tana murmushi.
Abbaa gyara zama yayi tare da gyaran murya ya ce, "Ai haƙuri ba zai goge wannan laifin ba, saboda criminal issue ne, sata kika mini irin babban satan nan da idan aka riga aka maka shi sai abinda Allah yayi kawai."
Mami da bata harbo jirgin abinda Abbaa ke nufi ba, da mamaki ta ce, "haƙuri kuwa ya zama dole na bada, Allah baka haƙuri Abbaansu, me na sace haka nayi gaggawan dawo da shi?"
Abbaa murmusawa yayi ya ce, "ai sacewan shi ne dai-dai Mamin yara, idan an sace ba'a dawo da shi sai dai a riƙe da kyau, Mamin yara maganan gaskiya da gaske nake kuma da gaske nazo sannan a shirye, a taimaka wa bawan Allah a kula mini da zuciyata da aka sace, tun ranan farko da na fara ganinki naji kin kwanta mini a rai kin mini, kin tafi da imanina, na daure na kusan shekaru goma sha, amma yanzu abin ya fi ƙarfi na a taimaka mini a tausaya mini, da gaske kuma na zo idan kin amince ko juma'an nan ban ƙi a kawo mini ke gidana ba, kuma kada ki yi tunanin alaƙanki da Ummul-khultum, domin ban zo ba sai da duk suka amince suka kuma yarda, dan Allah ki taimaki marayan Allah mai mata biyu, na jima ina dakon soyayyanki Hajiya Ramla."
Mami tunda Abbaa ya fara magana ta ɗauke wuta na ƴan mintuna, zamowa tayi kaman photo kawai tana kallonsa ta rasa ma me za ta ce ko me za ta yi, mamaki kawai ya tafi da ita a zaune, kallonsa take kuma ba ta ko kiftawa, har ya gama magana bata iya mosta laɓɓanta ba balle ta ce wani abu, dan bata san ma me za ta ce ba.
Abbaa murmushi ya sakarwa Mami ganin ta kafesa da kallo, a hankali ya ce, "Hajiya Ramla ke na ke saurare."
Mami wani irin dogon ajiyan zuciya ta sauƙe, sai sannan ta kawar da idonta a kan Abbaa, wani irin murmushi ta saki tare da buɗe baki ta ce...
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# ð˜¾ð™¤ð™¢ð™¢ð™šð™£ð™©
# ð™‡ð™žð™ 𙚠&
# ð™¨ð™ð™–ð™§ð™š
👄'YAR KARUWA👄💅
Officially
ð˜½ð™®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Ashe zamu ga juna fan's club
Adamsy fan's club
Sarauta's Library
Asmabaffa official novels
Fan's masu Sharhi a wannan groups, Uwar batoorl na godiya, wannan page naku ne.
اللهم صلى Ùˆ سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤ðŸ¤
Ba editing ayi haƙuri da typing errors.
ðŸ…¿ï¸ 56 _ 60
Mami ta ce, "Alhaji abinda kunnuwana ke jiye mini kana faÉ—a haka ne ko kuwa mafarki nake?"
Abbaa yana murmushin ya samu karɓuwa ya ce, "ba mafarki kike ba Mamin yara haka abin yake, nine dai na ce a taimaka mini a tausaya mini kar na mutu da soyayyanki, kuma ko nan da sati kika buƙaci ayi biki to a shirye nake."
Mami murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo tayi sannan ta ce, "ka yi haƙuri Alhaji ba wai na ƙi ka bane, a'a aure ne kawai ba ya gabana har yanzu, wanda nayi a baya ya isheni."
Abbaa cikin damuwa yake kallon Mami ya ce, "Me yasa Hajiya Ramla? Ki faÉ—a mini gaskiya idan nine ban miki ba ko kina tunanin wani abu ne akan mata na."
Girgiza kai Mami tayi tana mai iya ƙoƙarinta wajan ganin wannan magana bai sa ta yiwa Abbaa rashin mutunci ba ta ce, "Ko ɗaya Alhaji, nice kawai ba aure a gabana."
Abbaa ya ce, "Duk ɗan sunna ai ba ya ƙin aure Mamin yara, nasan dole dai kina da wani dalilin naki, Allah huci zuciyanki amma dai ina sonki, kuma zan baki lokaci dan jiran amsar da za ki bani, yanzu ban ɗauki wannan a matsayin amsa ba, daganan har wata guda na baki duk ki yi shawara ki yi tunani, duk abinda kika yanke ki sanar da ni, musamman in maganan bikin ne to sati guda kawai za'a yi Insha Allah sai ki fara shiri tun kamun ki gama tunanin" Abbaa ya faɗa yana sakar wa Mami murmushi ƙayatacce.
Gululun baƙin ciki ne ya tokare Mami, amma da yake bata son dogon magana sai bata ce wa Abbaa komai ba, har ya gama iya surutunsa ya fice, sai sannan ta ja wani dogon tsaki a fili ta ce, "Matarka bata ƙyaleni ba kuma ba ta ƙyale yarinyata ba a haka zan aure ka? Ai ko auren zan yi ina da wanda nake ƙauna, shi ma ban amince masa ba balle kai, saboda ba auren bane a gabana yanzu, kuma iya shekarun da ka ɗauka kana dakon soyayyata haka Alhaji Mukhtar ya ɗauka ko na ce fiye da haka, dan tun Banafsha bata yi wayo ba ga shi har ta zama budurwa, wa ma ya san ko kai naka na yaudara ne kawai, ni yanzu ba aure ne a gabana ba, aurar da Faɗimatu na shi ne a gabana, Allah kuma ya bata miji nagari..." Haka Mami ta dinga mita da surutu ita kaɗai kaman wacce ke yi da mutum a gefenta, ko kuma wacce aka kunnata, hhh ko da yake Abbaa ne ya kunnata tunda ya taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi.
Banafsha da ta shiga ɗaki sanya pad, tun shigowan Abbaa ta ji, da har tana niyan fitowa amma tun daga kalman Abbaa na Mami ta masa laifi har ya ce criminal case ne, sata ta masa tuni Banafsha ta fahimci me Abbaa ke nufi, mamaki ne da kuma farinciki suka kuma kama Banafsha san da Abbaa ya furta abinda ke zuciyansa, duk da a wani gefe tana tuna Umma da Ya Danish, amma abin ba ƙaramin daɗi ya mata ba, kuma ya ƙara wa Abbaa kima a idonta, Abbaa shekara da shekaru yake maƙwabtaka da Maminta, yasan abinda take aikatawa amma duk da haka yana sonta, kuma bai yi ƙasa a guiwa ba yau ya sanar mata sannan a shirye yake da ya aure Mami akan lokaci, su Abbaa na hiransu amma Banafsha ke musu murmushi ita ɗaya kaman ta buga tsalle, saboda haka kawai ita ta ji Abbaa ya fi kwanta mata akan Alhaji, musamman da za su zama so close again da Umaimatynta, kuma tunda su Ummu sun amince su shikkenan ba komai Allah ya sa Mami ma ta amince...
Tunanin Banafsha na Allah sa Maminta ta amince ne ya staya, sakamakon jin amsan da Mami ke bawa Abbaa, saurin runste ido Banafsha tayi tana jin kaman ita ake sokawa wani abu mara daɗi a kirjinta, gaskiyan Abbaa ne da ya ce duk ɗan Sunna ba ya ƙin aure, kuma a ganin Banafsha ko yana da dalili duk da haka ƙin aure bai kamace sa ba, saboda yanda aka same shi ta Sunna, to bai kamata a ce shi ma bai da wannan burin na samar da wasu ta Sunna ba, menene mastalan Mami kam? Allah ya hore mata baiwan kyawun jiki, fiska, hali da na zuciya, sannan uwa uba abinda wasu sai sun haɗa da boka da malam suke samu, to ita Allah ya hore mata a sauƙi wato farinjini, Mami na da jama'a sosai-sosai, amma Banafsha har yau ta rasa ne ya sa mahaifiyarta ta zaɓi wannan rayuwan, dole tana buƙatan amsa, dole tana buƙatan jin labarin wacece Maminta, asalinta, ƴan uwanta, mijin da take ikirarin ta yi auren farko ta gama, da duk komai ma dangance da tarihin rayuwan baya na Mami, a hankali Banafsha ta lumshe ido ta ce, "Duk a ina zan samo waɗannan amsoshin ya Rabbi, ka iya mini da kanka ya Hayyu ya Ƙayyum" ta faɗa kaman za ta fashe da kuka(ni uwar batoorl na ce ni ke da amsoshin Banafshaty, ki biya kiji komai a_z).🤣
Banafsha dai-daita nistuwanta tayi yanda Mami ba za ta gane ta ji abinda suka tattauna da Abbaa ba, ta shiga palourn da sallama, jikin Mami ta koma ta kwanta tana cewa, "Mamina kaman muryan mutun na ji, amma kamun na fito ban ga kowa ba ke É—aya."
Mami taɓe baki tayi ta ce, "Eh! Abbanku ne ya zo tambayan ya jikinki, na faɗa masa da sauƙi, zan ƙira ki kuma ya ce sauri yake, idan kin ji sauƙi sai ki shiga gidan ki gaishe sa ko."