Sashe 15
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwantar mata da hankali nayi, na ce mu dage da addu'a da kuma karatu, sannan in Allah ya yarda ni ma daga yau ba zan sake irin wannan dena zuwa makarantar ba, da ƙyar na shawo kan Umaima ta shige wanka, tana fitowa ta saka kayana muka yi nafilfilunmu da addu'oe sosai, sannan muka kwanta, da asuba kuwa muka tashi muka hau karatu saboda exam's.
Ya Danish taƙaici da ya cika sa ya masa dama-dama, ko gidan bai koma ba daga nan ya yiwa motansa key ya wuce wajan aikinsa da ke Camaroon, idan ya koma Sunday da yamma sai Friday da yamma yake zuwa, weekend kawai yake zuwa yi a mubi.
# Hareeyh
# 09161720046
# 07015870735
# ð˜¾ð™¤ð™¢ð™¢ð™šð™£ð™©
# ð™‡ð™žð™ 𙚠&
# ð™¨ð™ð™–ð™§ð™š
👄'YAR KARUWA👄💅
Officially
ð˜½ð™®
Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)
SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)
TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.
PAGE NAKU NE
Habiba muhammad Yusuf
Æingel kabi
My Heartbeat
Masoyiya bealky
اللهم صلى Ùˆ سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤ðŸ¤
ðŸ…¿ï¸ 31 _ 35
Washe-gari Abbaa da kansa ya saka Nana ta kawo wa Umaima uniform nata gidanmu, Umma sai cin rai take yi tana ta fushi akan Umaima ta kwana a gidanmu, amma Abbaa ko a jikinsa, Umma haushi kaman ya kasheta ga shi Ya Danish ba ya gida, kuma babban yaya ba ruwansa, ya mus'ab da ke Camaroon ma ko yana nan ba ruwansa, Ya Danish ne daman mai biye mata.
Mun yi wanka mun shirya tsaff muka fito, abin karyawanmu da komai muka samu Mami ta jera mana a kan centre carpet na palourn, zama muka yi muka cika cikinmu yanda ya kamata, sannan muka yiwa Mami sallama ta ba mu kuÉ—in mashine da na kashewa muka fice, cikin sa'a muka samu mashine kuwa da wuri, ya ajiye mu a makaranta muka shige hall na exam.
Haka rayuwa ta dinga tafiya da daɗi da babu daɗi dai sai haƙuri, mastalolin rayuwa da ƙalubalen rayuwa gare ni kullum ƙara gaba suke yi, saboda daga halayyan Mamina babu wanda ya canja kullum gaba-gaba abun yake yi, ni a tunanina abinda wancan stohon ya mini zai sanya Mamina gyara kura-kuranta, amma ina Mamina ci-gaba tayi da harkokinta, sam-sam Mamina bata jin ƙira dan ta riga da tayi nisa, kullum dai magana guda ne, idan na ce ta dena wannan rayuwa, sai ta mammakeni kuma ta ce sana'a ce dan ta rufa mana asiri,nidai wannan sana'a banga alfanunta ba, sai dai ban da yacce zan yi idan ba addu'a ba.
Maganan makaranta kuwa na dage sosai na mayar da hankali muna exam's namu hankali kwance, sannan a tahfiz ma ina ƙoƙari yanda ya kamata, tsakanina da Malam Abbo kuwa yanzu ya zama kaman yayana dan yana yawan mini faɗa da nasiha, sannan wani irin shaƙuwa na neman shigowa tsakaninmu wanda ni dai ban farga da hakan ba sai da shaƙuwan tayi nisa.
Sati biyu muka kwashe muna exam's, sai ranan Alhamis muka kammala, daga ranan kuma muka yi wa makaranta bye-bye, saboda musabaƙan namu week da za'a shiga ne.
Kaman ko wanne weekend, yau ma da yake Saturday da wuri muka je tahfiz muka dawo, tun daga compound na gidanmu da na shigo na ga wata dalleliyar haɗɗaɗɗiyar Mota, lumshe ido nayi kawai ina ambaton sunan Allah dan nasan ba zai wuce wani baƙon Mamina tayi ba, taɓe baki nayi ina faɗin ko wani jarababben ne da sanyin safiya haka oho, sai da na seta zuciyata na shanye taƙaicin da zan tarar a ciki tun ban shiga ba, sannan na tura ƙofan palourn na shiga da sallama, daga muryan wanda ya amsa mini sallaman na sheda baƙon da Mami ta yi da sassafen.
Ƙarisa shiga palourn nayi kai na a sunkuye, durƙusawa nayi har ƙasa na ce, "Sannu da zuwa Alhaji."
Alhaji Mukhtar na washe baki ya ce, "Sannu Æ´ar albarka, sannunku da dawowa ko."
Amsawa na yi har yanzu ban ɗago ba balle mu haɗa ido, a haka na gaishe sa ya amsa, ya ce na je na huta na karya zuwa anjuma zai ji karatun nawa, ba musu na amsa na miƙe na shige ɗakina, ina shiga na faɗa kan gado tare da ɗaga hannayena sama na ce, "Ya Rabbi ga bayinka nan, ka fi ni sanin abinda suke ciki, ya Rabbi ka shirya su ka gyara rayuwansu, ya Rabbi kada ka kama zuri'arsu da laifin da basu ji ba, ba su gani ba, don kuwa ƙur'ani mai girma ya ce "az- zina dailun (zina bashi ce)", Allah ka shiryamu duka, ka shiga stakaninmu da biyan bashin da ba mu ci ba", ina ƙarishe addu'ana na miƙe na cire uniform nawa, ina ƙoƙarin fita sai Mamina ta shigo, murmushi ta sakar mini ta ce, "Sayyada Faɗimah a zo a karya, kada ulcer ta kama mini 'yar fari, 'yar auta."
Murmushin nima na yiwa Mamina ban ce komai ba, na bi bayanta muka fice, abin karyawa na samu ta zubo mana ni da ita, zama nayi amma na kasa cin abincin, kasancewan Alhaji Mukhtar na palourn duk da dai hankalinsa na kan wayansa ne, Mamina ganin naƙi ci sai ta gusturo sinasir ɗin ta kai mini baki, ni kuma na buɗe bakina a hankali ina karɓa, a haka ta dinga bani a baki har na ƙoshi, sannan ta cigaba da cin nata, Alhaji Mukhtar da ke kallonmu sai yayi murmushi ya ce, "Lallai Ramlah kin shagwaɓa mini yarinya da yawa, budurwa da ita kina mai da ta 'yar goye, yarinyar kirki kar ki biyewa Maminki fa, ke babba ce yanzu."
Ƙasa nayi da kai na ina murmushi, Mamina kuwa kallon soyaya ta yiwa Alhajin nata ta ce, "wannan jaririyar ce babba? Banafsha ta wuce na sa zani n goya ta ne Alhaji? Ita ce fa 'yar fari kuma 'yar autan Maminta."
Alhaji Mukhtar ma yana murmushin ya ce, "Amma dai wasa kike yi, Banafsha kar ki yarda fa ta ce miki auta, ƙannenki na zuwa."
Mamina ta ce, "bayan ita ba kowa, daga ita ba ƙari, tal ɗin Maminta, shalele gudan stokar miya."
Alhaji idanuwansa akan wayansa ya ce, "yarinya É—aya bata ishe mu ba, dole ki haifo mini wasu."
Kai na a ƙasa ina sauraran maganan su Mamina, jin abinda Alhaji ya ce sai nayi saurin ɗagowa dan na kalli yanayin Mamina, a tunanina zan ga tayi murmushi dan ita ma tana son haifa mini ƙanne, amma sai saɓanin hakan na gani, Mamina ta haɗe fiskanta ta yi kicin-kicin da shi, Alhaji Mukhtar kuwa hankalinsa kwance yana lasta wayarsa sai ma murmushin da yake yi, dan yasan ya stokano masoyiyarsa Mami kuma shi daman burinsa kenan, saboda wani shiri da yake yi na daban.
Mamina ganin ma yana murmushinsa ya manna mata hauka, sai ta miƙe ta wuce ɗakinta, ni kuma na tattare kwanukan na mayar kitchen, har da wanda Alhaji ya ci abinci a ciki, na Juyo zan shige ɗaki sai Alhaji ya dakatar da ni ya ce na zo, dawowa nayi na samu waje a nesa da shi na zauna a ƙasa, yana murmushi ya ce, "Yarinyata Banafsha ya karatun? Fatan kun gama exam's lafiya?"
Kai na a ƙasa na ce, "Lafiya Alhamdulillahi, Alhaji."
"To Masha Allah! Allah sa result tayi kyau, Ya karatun musabaƙan kuma? Yaushe za ku yi?"
Kai na a ƙasa har yanzu na basa amsa da ranan da za mu yi, jinjina kai yayi ya ce, "To shikkenan, zuwa dare Insha Allah za mu duba karatun, yanzu je ki huta, zuwa anjima za mu je anguwa Insha Allah."
Miƙewa nayi na masa a huta gajiya na shige ɗaki na, shi ma miƙewa yayi ya shige ɗaya ɗakin, ruwa ya wasta ya kwanta tare da jawo wayansa yayi dialing wani number da sunan "My Son" ya ke ɓaro-ɓato, ba jimawa aka ɗauka, Alhaji Mukhtar yana murmushi ya ce, "Chief of the air staff."
Wani haÉ—aÉ—É—en murya ne ya murmusa yanda sai da sound na murmushin ya fito, sannan cikin yanga ya ce, " morning Sir."
Alhaji Mukhtar murmushi yayi tare da girgiza kai ya ce, "BUNAYD Allah ya shiryeka."
A hankali kaman mai raÉ—a ya ce, "Ameen Papi."
"Ya General?"
"General yana gidansa Sir."
Girgiza kai Alhaji ya kuma yi ya ce, "zan saɓa maka Bunayd, ina ubanka kana ce mini wani Sir."
Murmushi ya kuma yi ya ce, "sorry Sir!"
Alhaji ya ce, "Ubanka General ne Sir, yaushe za ka shigo Kano?"
"Soon zan shigo, kasan za'a yi bikin Abeed in next 3 months."
Alhaji ya ce, "Masha Allah! Ya fi masa ai yayi aurensa, kada ya biyewa duniya wai sai yayi iyayi, yanzu mutuwa araha take, kar mutum yaga kullum yana sama kaman stunstu ya ɗauka shi ba mutuwan zai yi ba, to azara'ilu ko a duniyar wata kake lokacinka na cika zai zare ranka, balle jirgi da nawa aka yi, idan akwai mai ƙararren kwana a ciki ai hastari jirgi ke yi, to gwanda tun wuri kasan abinda ka adana kamun ka wuce babu masu maka addu'a."
Bunayd a ɗaya ɓangaren murmushi yayi bai ce komai ba dan yasan da shi Papi ke yi, Alhaji ya kuma cewa, "ko ka fito da mata ko kuma daga kai har ubanka General ku ji anbada ka sadaka, sadaka yalla zan ba da kai a masallaci, in ana ƙiran macen sadaka ta Annabi, to kai za ka zama na Annabi, bari lokacin da na ɗiba maka su cika."
"Byee Sir, my regards to Adamawa" yana gama faɗa kitt ya daste ƙiran.
Alhaji murmushi yayi tare da cewa, "Allah ya muku albarka" yana gama faÉ—a ya gyara kwanciyansa ba jimawa bacci tayi gaba da shi.
Æangaren Mami ma tana barin palourn ta bi lafiyar gado ta koma baccinta, cike da taÆ™aicin Alhaji Mukhtar, maganansa ya wuce stakaninsu ga shi har a gaban yarinyarta yana faÉ—a mata maganan aure, ita kuma ga shi duk abinda zai mata ta kasa rabuwa da shi, a rayuwanta gaba-É—aya wannan ne karo na biyu da taji tana matuÆ™ar son wani har tana jin ba za ta iya rabuwa da shi ha, Alhaji Mukhtar na cin albarkacin wannan soyayyan idan ba haka ba, da tuni ba wannan maganan ake yi ba.