← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 58

Sashe 18

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKI NE

Hafsat Umar

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 36 _ 40

⭐
KANO STATE
A babban filin sauƙan jirgi na garin Kano, jirgin su Alhaji Mukhtar yayi landing, yana sauƙa ya samu already driver na jiransa, yana isowa wajan motan sai driver ya buɗe masa gidan baya ya shiga, sannan ya kulle ya koma ya shige ya ja motan suka nufi Railway estate, anguwan manyan ƙwari kenan a Kano, daga sunan kunsan ba wajan cin miyan lami bane.

A gaban wani katafaren, shirgegen, haɗaɗɗen gida wacce ke ɗauke da wata arniyar gate ga sojoji ko ta ina, driver na horn aka buɗe musu suka danna hancin motan cikin gidan, subhanallahi! Wata munafukar estate ce, upstairs guda biyu, sai haɗaɗɗun plat guda biyu su ma, ga motoci sun kai goma manya-manya masu shegun kuɗi, upstairs na farko Alhaji Mukhtar ya nufa fiskansa ɗauke da murmushi, yana tura ƙofan ya shiga da sallama, da wata kyakkyawar matashiyar budurwa wacce ba za ta wuce sa'ar Banafsha ba ya fara karo, murmushi ya sakar mata tana masa oyoyo, hugging nata yayi ya ce, "Maman babanta sannu ko."

Murmushi budurwan ta saki ta ce, "Papi staraban Adamawa."

Alhaji shafa kan 'yar budurwan yayi ya ce, "Majeeder tun ban huta ba?"

Murmushi kawai tayi, Alhaji ya riƙo hannunta suka ƙarisa shigewa palourn, har suka haura sama da yake part na Alhaji, suna haurawa kuwa sai ga wata hamshaƙiyar mata kyakkyawa, wacce kana ganinta kasan ita ce mahaifiyar Majeeder, Hajiya Sa'adatu kenan uwargida ga Alhaji Mukhtar, harara Hajiya ta bi Majeeder da shi ta ce, "Jeedderh ban aike ki ba ne, me kika tsaya yi?"

Majeeder tura baki tayi ta juya, Alhaji Mukhtar murmushi kawai yayi bai ce komai ba, shi ne ya ce, "Hajiya Barka da gida."

A gadarance Hajiya ta ce, "Sannu da dawowa Alhaji."

Amsawa yayi kawai ya shigeta ya wuce ɗakinsa, sai da ya rage kayan jikinsa ya zauna bakin gado tare da sakin murmushi ya ce, "Allah Sarki duniya, ba dole mu bi mata ba, ai dole maza su nemi matan banza, mace ce a gidan sunna wai bata san yanda za ta kula da mijinta ba, sai ka je wani wajan sai a dinga tarairayarka, ga shi dai saɓon Allah ne a wajen, Astagfirullah! Allah na tuba, Allah ka mallaka mini Ramlah idan ita alkairi ce a gare ni, ba dan halina ba ya Rabbi."

Yana gama magana ya miƙe ya shige toilet ya wasta ruwa sannan ya zo yayi sallolinsa ya jawo system nasa ya fara duba ayyukansa, yana gamawa ya bi lafiyan gado ya kwanta, yana son ya huta saboda nan da kwana biyu zai tafi Russia akan business nasa da wani abun gaggawa ya taso.

Hajiya Sa'adatu tana ganin Alhaji ya shiga É—akinsa ta juya ta koma nata, tare da fidda waya tana ta magana akan nata business É—in ita ma.

Mata mu gyara, abun haushi da iya matan masu kuɗi ke kasa kula da mazajensu, saboda boko ta jiƙa su ko issuen harkokinsu to da sauƙi, amma baiwar Allah kina salamatu 'yar malam muhammadu ke ba juya dubu ba balle ya koma dollar, aikin me kike da za ki kasa kula da miji ki tarairayesa? Maza dai ƴan haƙuri ne, balle ma a wannan zamani da muke ciki suke ganin mun fi su yawa, to ki kula ƴar uwa, aure ya fi gaban wasa, idan mijinki ya bi matan banza ke kika nema, idan mijinki ya miki kishiya babu niya wannan ma ke kika jajuɓo ma kanki, Aradu mata iyayenmu da mu kanmu da kuma ƙannenmu kowa ya gyara halinsa.

Majeeder tana tura baki ta shige ɗakinta da ke nan a ƙasa ta sanya after dress ta fito, mota guda ta ɗauka da kanta ba driver tayi driving ta je ta amsawo Hajiya saƙonta, hankali kwance duk da tasan Papi ya hanata driving da kanta, Majeeder HAUWA'U MUKHTAR SULE KWALLI, ɗiya ta biyu kuma 'yar Auta ga Hajiya Sa'adatu, da Alhaji Mukhtar, Majeeder kyakkyawar gaske ce, bata da haske sosai, tana nan kalar stamiya haka, tana da hanci mai stayi da ƙaramin lip's nata ja da shi, tana da idanuwa 'yan dai-dai, bata da stayi sosai haka ma jiki, ƴar dai-dai ce ita, tana da gashinta mai tsayin gaske baƙi wuluk da shi.

Tana dawowa ta hauro sama ta kawo wa Hajiya Sa'adatu aikanta, sannan Hajiya ta ce ta koma ta cewa masu aiki a ɗaura girki kamun Alhaji ya tashi a bacci, a haka ta juya ta kuma faɗa musu, sannan ta shige ɗakinta ta cire kayan jikinta ta wasto ruwa ta zo ta ɗau wayanta tana lastawa, Majeeder maƙura ce a kyau da kuma sura.

Alhaji sai da ya huta sosai sannan ya tashi ya wasta ruwa, palourn ƙasa ya dawo ya zauna yana kallon labarai, ƙiran layin Mami yayi suka sha firansu, yana gamawa Hajiya ta shigo palourn, waje ta samu ta zauna ta ce, "Alhaji ka faɗawa yaronka ya cire layina a blacklist, ya ɗau ƙirana ko na saɓa masa, yaro kaman ba nice uwarsa ba duk an bi an kanainaye sa, baya girmamani balle mutunta ni ko yaji tausayina."

Alhaji Mukhtar murmushi yayi ya ce, "Hajiya ke É—in ce kika nuna masa haka ai, yanzu ma idan ba ki daina wasu yawo-yawon nan ba, zan tattara Majeeder ita ma na mayar da ita gidan General tun da shi matarsa mai zama ce, tasan mutuncin aure, ko kuwa na auro wata sai ki ci-gaba da halinki."

Baki na kumfa Hajiya ta yunƙuro cikin haushi da kishi ta ce, "Babu ubanda ya isa ya ɗauka mini yarinya, idan wancan nayi shiru to wannan ba zan yi ba, kuma ba'a haifi uwar shegiyar da za ta haifa mini kishiya ba, baka isa ba, kuma ni halina lafiya lau yake atou."

Murmushi kawai Alhaji yayi ya ci-gaba da kallonsa, shi Alhaji haka yanayinsa yake, shi mutum ne da kamun kaga fushi a fiskansa to za'a É—au dogon zango, yanayinsa ke sanya Hajiya Sa'adatu yaudaran kan ta tana tunanin ko ta mallakesa ne.

Hajiya kuma cigaba da yin nata surutun tayi kaman wacce aka kunnata, har dai ta gama ta gaji tayi shiru, Hajiya Sa'adatu irin matan nan ne masu kuɗi, marassa mutunci, masu wulaƙanci, ita ko yaranta ba su da lokacinta balle mijinta, gaba-ɗaya tunaninta akan business nata ne, kuma saboda haka ne ta stayar da haihuwanta wai yara biyu sun ishe su, kada ta stufe ko su hanata kula da harkokinta, karshe ma zuwa tayi aka cire mata mahaifa Alhaji bai sani ba

Kwana biyu tsakani, Alhaji ya shirya ya tafi Russia kuma zai yi sati biyu kamun ya dawo, yana tafiya washe-gari Hajiya Sa'adatu ta ɗaga ƙafafuwanta ta tafi Dubai, sai da ta yi kwana uku sannan ta dawo, kuma bata sanar da Alhaji ba, Majeeder dai tana gida, daga ɗaki sai ɗaki, sai kuma driver ya kai ta makaranta idan ta dawo ya kuma kai ta islamiyya, inda a can ne ma suka yi musabaƙa, har Alhaji Mukhtar ke bawa Banafsha labari lokacin da ya kai ta school.

Alhaji sai da ya kwashe sati biyu casss, sannan ya dawo, ranan ya samu Hajiya Sa'adatu sun fita da wata ƙawarta, Hajiya bushira sun je akan batun siyasar da Hajiya bushira ke ƙoƙarin stayawa takara, Alhaji ya riga ya saba da halin abarsa, shiyasa kawai ya share ya zauna, ko da ta dawo bai ce mata komai ba.

⭐⭐
LAGOS
Banana island
Anguwa ne na shegun ƙasa, manyan a ƙasa ba iya Lagos ba, anguwan sai wane da wance, ba ko wani laga-lagan me kuɗi ke mallakan gida a wajan ba, sai wanda ya cika cikakken babban ƙusa, fili mai araha a wajan, iya fili babu gini, arahansa shi ne 10billion, a hakanma da ne lokacin da duniya ke zaune shiru ba yanzu da komai ya tsaya da ƙafafuwansa ba.
Wani gida ne wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa, kusan a street ɗin babu irinsa wajan haɗewa, Arnen haɗaɗɗen gida ne na gani na faɗa, kana ganin gidan kasan da starinsa da komai daga ƙasar waje ne, sai dai masu ginawan dole yan Nija ne, domin idan ana neman 'yan baiwa waɗanda suka san kan gini duk iya staruwansa to sai baƙaƙen fata, turawa masu jan kunne barsu dai kawai da iyayi, Nigeria my country.

Tsayawa tsara yanda wannan haɗaɗɗen Arnen gidan yake, to tabbas ɓata baki ne da cin lokaci, dan sai mu cinye page's a abu ɗaya, tun daga wajen gidan har ciki sojoji ne kaman wanda gidan barikin sojijine ba gidan mutum ba, kai kawo sojojin ke yi kaman masu yin Safa da Marwa, Uwar batoorl ta nufi cikin haɗaɗɗen ginin dan kwaso labari sai taji iska na neman ka da alƙalaminta, a ɗari ta ɗago, da mamaki nake kallon jirgi ne na sojoji ke shawagi a saman gidan, can kuma sai ga wani ya fito a jirgin kaman zai diro, amma hannunsa riƙe da igiya har sai da ya sauƙa a cikin gidan, sannan ya sake igiyan, masu jirgin suka janye suka yi gaba, wannan bawan Allah na juyowa sai da Uwar batoorl tayi suman wucen gadi.

Starki da godiya su tabbata ga Ubangijin kowa da komai, wanda ba ya gyangyaɗi balle barci, Sarkin da mutuwa ta koru gare sa, Sarki mai stara halittan bawa yanda ya so, Wani haɗaɗɗen guy ne wanda a ƙalla zai kai shekaru 34 da haihuwa, kyawunsa har ya wuce misali, idan aka ƙirasa kyakkyawa ma to an mai da sa baya ne, saboda irin haɗuwansa, gaskiya Allah yayi halitta a wajan.
Chapter 18 · 0% Book details