Sashe 25
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umaima baccinta take sha hankali kwance, ganin haka kawai na ƙyaleta na fito, ba dan ina sauri banson haɗuwa da ya Danish ba ai da na sola mata dundu na tashe ta, kawai ta ci sa'a ne, faɗawa Ummu nayi tana bacci a bani saƙon kawai na tafi, Ummu ta bani na amsa na musu sai anjima na fice.
Bayan fitan Banafsha a palourn sai Mami ta tashi a inda take zaune ta dawo kujeran da Alhaji ke zaune, kallonta Alhaji yayi yana murmushinsa ya ce, "Amaryata ya aka yi?"
Tura baki Mami tayi da shagwaɓa ta ce, "kaga banaso Alhaji, haka kawai za ka ɓata mini rai, ni bansan ma me yasa nake sonka har haka na kasa rabuwa da kai ba, kuma kullun cikin ɓata mini rai kake yi, yanzu ko so na ka daina kullum faɗa kake nema da ni", ta faɗa tana juyawa wai tayi fushi.
Murmushi Alhaji yayi ya ce, "Allah ne ya ɗaura miki soyayyata kaman yanda nima ya ɗaura mini ƙaunarki da sonki, kuma in Allah ya yarda zan mallakeki, nidai yanzu roƙo na ɗaya ki faɗa mini abu game da danginki, kinƙi bani labarinki kuma kinƙi aminta da aurena, meyasa kike mini haka Ramla? Ina sonki da yawa fa ki taimakeni ki amince da auren nan dan Allah, kar Banafsha ta samu miji a ce za'a yi bikinta kina zaman kanki, sam-sam abin bai yi tsari ba, dan Allah ki amince da maganan auren nan Ramla, wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki na rashin mallakanki, ni ba zan iya ci-gaba da saɓa wa Allah ba balle na kai ga aikata babban zunubi, ita zina bashi ce kayi da mahaifiyar wani sai anyi da taka, ka yi da ƴqar wani sai anyi da taka, kayi da matar wani sai anyi da taka, kayi da ƙanwar wani sai an yi da taka, ni kuma ko ɗaya bana addu'an haka, dan Allah Ramla ki amince mini muyi komai akan Sunna."
Mami ɓata fiska tayi ko kallon Alhaji taƙi yi, Alhaji kaman zai yi kuka ya kamo hannun Mami amma ta ƙwace, riƙo hannunta ya kuma yi ya ce, "Please Ramla say something, dan Allah ki ce kin amince, ko mutum daya a danginki sai mu nema a mana aurenmu, idan bakya so ma sai a ɗaura mana haka al'umman Annabi su zama shaidu da waliyai, dan Allah Ramla, wallahi na miki alƙawarin zamowa uba nagari abin alfahari ga yarinyarki da ma sauran da za ki haifa mini, na miki alƙawarin zamowa miji na gari jajirtacce gare ki, wanda zai tsaya miki a komai ya kuma kula da duk abinda ya shafe ki, sam-sam kada kiji da matata kiyi tunanin ina da mata, banda zafi kam, amma na isa da gidana, dan Allah ki ce kin amince."
Zuwa yanzu Mami ji take kaman ta kwaɗawa Alhaji mari, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, ƙarshe Alhaji kawai sai ya rungumeta ƙam a ƙirjinsa, a take suka sauƙe wani nauyayyen ajiyan zuciya kaman waɗanda suka yi kokawa ko kuma suka yi gudu, Mami lafewa tayi a jikin Alhaji, ba zato ba tsammani yaji hawayenta na ɗiga a kan hannunsa, Alhaji hankalinsa a tashe ya dubeta cikin damuwa ya ce, "Ramla akan aure kike kuka? Dan na ce ki amince ki aure ni? Shikkenan kiyi haƙuri Allah huci zuciyanki, dama kullum idan nayi magana a faɗa muke ƙare wa hakan baya damuna، to faɗa da sauƙi akan hawayenki, hawayenki masu stada ne a gare ni ba zan jure zubansu ba, idan wani yayi sila ma sai inda ƙarfina ya ƙare balle a ce ni da kai na, Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda daga yau na daina miki maganan aure, in Allah ya ƙaddara hakan, to Allah fahimtar da ke da kansa ya tabbatar mana da alkairi, inkuma babu hakan a ƙaddaranmu shi ma Allah zaɓa mana abinda ya fi alkairi, Allah bamu ikon tuba kamun mutuwa, Allah sa mu gama da duniya lafiya muna amintattun bayi salihai", Alhaji na gama magana ya miƙe ya ɗau key na motansa ya fice.
Mami zama tayi a wajan tana risgan kukanta kaman wacce aka aiko wa saƙon mutuwa, a haka har Banafsha ta shigo ta sameta tana kukan, bata ma ji shigowanta ba sai ji tayi muryanta na rawa tana faɗin, "Mamina me ya sameki? Me ya faru?" Haka na ƙarishe maganan nima cikin tashin hankali ganin Mamina na kuka."
Mami ƙoƙari tayi ta stayar da kukan ta ce, "Bakomai Banafsha, ki ɗaura mana abincin dare", tana gama faɗa ta miƙe ta amshi saƙonta ta shige ɗakinta, ni kuma guntun ƙwallan da ya zubo mini na share ina addu'an Allah ya yayewa Mamina damuwan da ke damunta, haka na miƙe na yi sallahn la'asar, sannan na shige kitchen na ɗaura mana tuwon dare, duk da ina cikin damuwan abinda ke damun Mamina, amma na tsaya nayi aiki mai kyau, na yi girki na gama, na share palourn har stakar gidanmu tass, na gyara har ɗakin Alhaji ko ina na gidan ya ɗau kyalli, na kunna turaren wuta ko ta ina, ɗakin Mamina na shiga da sallama, sai lokacin na samu tana nata sallahn, banɗakinta na fara wankewa sannan na share ɗakin na kunna turaren wuta, har na fice tana jan carbi, ɗakina na koma na gyara abuna, sai da na gama na shiga wanka na ɗaura alwala tunda Magrib ya kusa, dogon rigana ƴar kanti na saka ta shan iska, zama nayi ina jan carbi har sai da aka yi sallah nayi nima sannan na shafa addu'a na fice.
Palourn namu shiru har lokacin Mamina bata dawo ba, Alhaji kuma da naji shiru ni na ɗauka ya tafi ma, sai na je ɗakin Mamina da sallama na shiga, samunta nayi yanzu ma akan sallaya, jikina a sanyaye na ƙarisa gabanta na durƙusa na ce, "Mami abincin na gama."
Ba tare da Mamina ta kalleni ba ta ce, "ki É—iba naki ki ci, sai zuwa anjima zan ci, ki sakawa Alhaji a kula."
Amsawa nayi na fice a É—akin, yanda Mami ta ce haka nayi, amma ni ban É—iba ba, ina dai jiran Mamina muci tare.
Alhaji kuwa yana ficewa a gidan ya je hotel ya kama ɗaki, a can har yayi sallahn Magrib da isha'i, har wajan ƙarfe tara yana can, gaba-ɗaya damuwa ta cika shi, lamarin Mami ya fara basa storo, niya yayi ya koma cikin Yola a daren zuwa gobe ya wuce Kano, amma ya kasa baya jin zai iya tafiya bai sanya Ramlatunsa a ido ba, kwana a hotel ɗin ma ba zai iya ba, haka ya tattara wajan ƙarfe goma ya dawo, lokacin kuma dagani har Mamina babu wanda ya saka wani abu a cikinsa, Mami ko fitowa bata yi ba, ni kuma na kasa cin abincin ni kaɗai, sai da Alhaji ya shigo sannan lokacin naji mostin Mamina, har ɗakina ta shigo ta ƙirani muka je muka ci abincin, Alhaji dai taɓawa kawai yayi dan kar masoyiyarsa taji babu daɗi.
Har muka gama cin abinci na musu sai da safe ba wanda ya yiwa wani magana a cikinsu, nidai ina shigewa É—akina na gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan nabi lafiyan gadona na kwanta.
Alhaji ma stame hannunsa yayi ya tashi ya shige ɗakinsa, Mami cikin damuwa ta tattare komai, sannan ta nufi ɗakin Alhaji, lokacin shi kuma ya fito wanka kenan, murmushi Alhaji ya sakar mata ya ce, "Masoyiya je ki wásta ruwa kema ina zuwa."
Mami jiki a sanyaye ta buɗe baki ta ce, "Alhaji ka yi haƙuri idan na ɓata maka rai.."
Dakatar da ita Alhaji yayi yana murmushi ya ce, "kije ki wásta ruwa ina zuwa, kar ki damu kanki ba komai."
Ba musu Mami ta juya, ɗakinta ta koma ta shige wanka kaman yanda Alhaji ya ce, Alhaji Mukhtar kuwa murmushinsa yake yi har ta fice, sannan ya shirya, ƙira ne ya shigo wayansa, yana murmushi ya ɗauka tare da amsa sallaman da aka masa a wayan, cewa yayi, "Allah taimaki General."
General a nasa ɓangaren murmushi yayi ya ce، "Yaya anwuni lafiya ya fama da jama'a?"
"Alhamdulillahi General, ya yaran ya kuma É—an ka mara jin magana?."
General É—an dariya yayi ya ce, "yaya wani rashin ji my Man yayi kuma?"
"Au kana tambaya ne? Tun wuri dai ka faɗa masa yabar ƙirana da Sir idan ba haka ba zan saɓa masa, tunda ya renaka yana faɗa maka General kana amsawa to nidai zan saɓa masa ne, yara ne duk sun mayar da mutane kaman sa'o'insu."
"Ayi haƙuri yaya."
"Haƙurin dama za ka bayar ai na sani, wannan yaron da macece na tabbata kana aurar da shi za'a dawo maka da ɗan ka, duk la bi ka sakalta shi ka shagwaɓa shi, Allah ya so ma Sojan sama ya ke, da na ƙasa ne kam ai nasan ba iyawa zai yi ba, yanzu ma tausayin matar da za ta zauna da Bunayd nake yi."
Dariya General yayi ya ce, "Amma dai yaya ba abinda za mu ce sai godiya, ai in akwai abinda ya fi aikin soja staff my Man zai iya, kuma ai sojojin sama sun fi na ƙasa baiwa, saboda ikon Allah kawai ke sa mutum yana sama kuma ya iya yin yaƙi, sannan duk macen da ta samu Bunayd to ina mai tayata murna ta samu miji nagari."
Girgiza kai Alhaji yayi ya ce, "shi yaron naka ne miji na gari a haka? Allah dai ya haÉ—a sa da wacce za ta iya da shi."
General dariya ya kuma yi ya ce, "Nikam ka tuna mini magananmu da shi ranan ma, ya ce na faÉ—a maka ka nema masa mata wacce za ta dace da shi, ya yarda zai yi auren, kasan yaron nawa da biyayya yake, ga jin magana."
Taɓe baki Alhaji yayi ya ce, "Ni ba zan nemawa Bunayd mata ba ya zo ya sa naji kunya, kai dai da kake ubansa sai ka nema masa, koma mene stakaninku ni nawa kallo, yadai tabbatar ya samu matar dan na gaji da kallonsa haka, mutum na neman kai shekaru arba'in amma ya kasa ajiye mata."