← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 58

Sashe 10

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuma a take naji raina ya ɓaci, sai naji gidan ya gundure ni ma, miƙewa nayi zan fice ba tare da na kuma yin ko tari ba, sai Umaima ta tashi ta riƙo hannuna kamun ta buɗe baki ta yi magana, Umma ta rigata ta ce, "Umaima kika kuskura kika ƙara taka ƙafanki kin ji waallahi to sai nayi mugun saɓa miki, shashasha kawai mara zuciya."

Umaima tura baki ta yi, da yake shagwaɓaɓɓiya ce sosai har da ɗan buga ƙafanta ta ce, "Masoyiya kiyi haƙuri kinji, ki dawo mu zauna."

Kallonta nayi da idanuwana da har sun tara ƙwalla na ce, "A'a Umaima, ki ji maganan Umma, nima gida zan tafi dare tayi", ina gama faɗan haka na juya ina danne hawayena.
Umaima biyo ni tayi ban sani ba, muna zuwa dai-dai bakin ƙofa kawai na ji sauƙan mari, ina ɗagowa naga Umaima ta dafe fiskanta, cikin ranaza duka muka kalli wanda ya mare ta, ashe ya Danish tare da su Umma ya shigo, duk abinda ya faru akan idonsa, daman yana staye a bakin ƙofan yana jin mu, haushinsa da tausayin Umaima ne ya rufe ni, na ƙwace hannuna a riƙon da Umaima ta mini, na fice da gudu dan muddin na staya to zan iya ramawa Umaima ko da kuwa kashe ni Ya Danish zai yi.

Umma tsaki taja ta ce, "Ka mini dai-dai Danish, Allah ya maka albarka, ke kuma dan ubanki wuce ciki tun da ita ba ƙanwar uwarki ba ce, munafukan yarinya sai liƙewa ƴar karuwa mara tarbiyya take yi, dan son zubarwa mutane mutunci, shashashar yarinya kawai."

Da gudu Umaima ta wuce É—akinsu tana kuka, Umma ganin ya Danish ya fice sai ta wuce nata É—akin ita ma, tana hararan É—akin Ummu.

Ya Danish kuwa ashe bin bayana yayi, amma ya tarar na jima da shigewa gidanmu, sai guntun tsakin da yaja ya ce, "Wallahi da na kama ki cikin daren nan zan gwada miki digiri na a iskanci, ni É—in babban É—an iska ne, amma babu komai, muddin kura na yawo zabo na yawo to watarana za'a haÉ—u, sai na tabbatar na gyara miki zama."

Ina shiga gidanmu na share hawayena na kuma seta kai na, ba tare da na ƙarewa palourn kallo ba na wuce cikin ɗakina, dan bana ƙaunar ƙara wani mummunan ganin irin na ɗazu.

Washegari da ya kama asabar da sassafe na gama duk ayyukan da zan yi, ganin Mami bata fito ba cikin taƙaici na fice a gidan ban tunkari ɗakinta ba, dan nasan rashin fitowan ta ba zai wuce tana tare da yaron da na gansu tare jiya ba.

Ina fitowa na nufi gidan su Umaima dan mu wuce Tahfiz, amma sai na haɗu da Abbaa a ƙofa yana ƙoƙarin fitowa, ganinsa sai na tsugunna na ce, "Ina kwana Abbaa."

Abba na murmushi ya ce, "lafiya Alhamdulillahi FaÉ—imah, ina kika tsaya haka baki tafi makaranta ba har yanzu?"

"Uhmm! Abbaa na tsaya aiki ne, kuma na biyowa Umaima mu tafi tare ne."

Abbaa murmushi yayi ya ce, "Ai Ummul-khultum ta jima a makaranta FaÉ—ima, ina ji Mamana ma yanzu ta fitaba jimawa."

Miƙewa nayi na ce, "To Abbaa sai mun dawo."

"A dawo lafiya FaÉ—ima, Allah ya taimaka ya ba da sa'a."

Da "Ameen" na amsa na wuce cikin sauri, dan ina storon dukan latti.

Ban bi kan kwalta ba sai nabi ta cikin anguwa duk da kuwa nasan da sassafen nan kam iyayen sa ido basu zauna ba, tunda tukunna yanzu safiya ne, ina isa makaranta na hangi Nana tana shiga ajinsu, nima ajinmu na wuce na shiga da sallama inda na tarar ko malam bai shigo ba, hamdala nayi sannan na nufi kujeran da muke zama da Umaima na samawa kai na mazauni, na dubi Umaima na ce, "Sabahul khair ya Aminiyaty."

Murmushi tayi ta rungumeni ta ce, "Masoyiya yau kuma Æ´ar larabci ne tun malam bai shigo ba?"

"Na'am yau larabce malam za muyi, me yasa kika taho kika barni amma?" Na faÉ—a ina hararanta da manyan idanuwa na.

"Banafshaty wallahi ke dai kin sani, labarin gizo ba ya wuce na ƙoƙi, in dai ya Danish na gari to fa sai dai haƙuri za muyi, Umma ce ta sanya ya sako ni gaba dan kar na biya miki, to da muka zo gada ya juya nima sai na juya aikam muka ci karo da shi, nan ya rakoni a guje na ƙariso har cikin makarantar nan" faɗin Umaima tana tura baki kaman ya Danish ɗin ko Umma wani yana kallonta.

Na buÉ—e baki zan yi magana sai malam ya shigo, nan muka dinga gaishe sa shi cikin harshen larabci shima yana amsa mana da larabcin.

Malam Abbo nan ya sa muka yi muraja'a aka fara karɓan hadda, kusan sai da rabin ajin suka bada hadda kamun aka iso kan mu, Umaima ce ta fara rero nata karatun cikin zazzaƙar muryanta har ta idar ita ma ba ɓata ko ɗaya, sai kabbara kawai ake yi, tana gamawa malam ya dube ni ya ce, "Bismillah malama Faɗimah Sufyan."

Sanin idan an ƙira sunan mutum an iso kan sa kenan, sai na gyara zama na nayi ƙasa da kai na, na fara rero haddan Suratul Taubah, karatu nake cikin muryana mai sanyawa mai sauraro nistuwa inda ba iya ƴan ajin ba hatta Malamin namu in dai zan yi karatu to idanuwan sa na kai na, sai da na kai ayaa sannan na share hawayen dake idanuwana dan ayoyin cikin Suratul Taubah in kasan fassaran su to dole jikinka yayi sanyi duk da wani sashin nata akan kafirai masu munafurtan Addinin Allah suke, wani gefen kuma akan yaƙin Manzon Allah SAW ne.

Malam Abbo har nayi shiru idanuwan sa na kaina, sannan ya cigaba da ƙiran sunan sauran ana bada hadda har dai muka gama karatun.

Bayan ya ƙara mana mun maimaita sai ya fita, nan malamin Tauhidi ya shigo, bayan ya fita shi ma malamin da ke ɗaukan mu Hadith ya shigo.

Tun ƙarfe 6:30am da muka je makaranta mu ne ba'a tashemu ba sai ƙarfe 10:30am.

Ana tashi ni da Umaima sai bamu tafi ba muka nufi office na Malam Abbo, sallama muka yi da neman izinin shiga sannan ya umurce mu da mu shigo, durƙusawa muka yi duka, amma sai ya mana nuni da kujera nan muka zauna, sai da ya gama haɗa litattafan gabansa kamun ya ɗago ya kallemu, da larabci ya ce, "lafia kuwa?"

Ƙasa nayi da kai na sannan na fara koro masa bayani akan musabaƙa, kallona yayi ya ce, "Faɗimah ai kun makara sai dai na gaba kuma, tun farko kun nuna ba za kuyi ba wanda dama dan na saka baki shiyasa aka barku a makarantar ba'a kore ku ba, sai dai ku bari na wani shekaran, domin waɗanda suka yi yanzu, su za'a je na gari da gari da su."

Marairaice wa nayi kaman zan yi kuka, nan muka dinga basa haƙuri, dan munsan Malam Abbo in yayi magana dole a saka mu a masu yi, ba wani babba ba ne shi amma kuma ana ji da shi a malaman makarantan saboda iliminsa, numfasawa yayi ya ce, "Shikkenan zan yi iya ƙoƙarina naga anyi da ku in Allah ya yarda, amma fa sai kun ƙara dagewa da muraja'a, dan an jima da yin nisa a karatun da ya shafi musabaƙan, muddin kuna buƙatan a yi da ku to sai kun dage dan a maye gurbin waɗanda ba sa mayar da hankali da ku."

Nan muka dinga godiya muka tabbatar masa da in Allah ya yarda za mu dage, ba za mu basa kunya ba, sannan ya sallamemu muka tashi muka fito a office ɗin, gaba ɗaya makarantar muka bari muna farin ciki dan duk mun saka rai akan wannan musabaƙa, sai addu'a muke kwarara wa malam Abbo.

Malam Abbo bin bayan su yayi da kallo yana murmushi, dan ya rasa dalili baya iya yiwa wannan yarinya musu in za ta faÉ—i abu ko kuma idan abu ya shafe ta..., shigowan wani Malami ne ya dakatar da shi daga tunanin da yake yi, yana murmushi.

Zama a kujeran dake kallon sa matashin malamin yayi ya ce, "Haydar na fa raba ka da maganan yarinyar nan, kasan dai wacece mahaifiyar ta da kuma sana'ar ta ko?"

Malam Abbo na murmushi ya ce, "Zubair ko me na ce maka ba zaka fahimta ba, amma ina tausayin yarinyar nan akan jarabawan rayuwa da suke ciki da mahaifiyar ta, kuma tsakani da Allah da aure nake ƙaunar ta, sai dai a yanzu tana ɗalibata banjin zan iya furta mata, amma in Allah ya yarda muna yaye su tunda ba zai wuce shekara guda ba zan bayyana mata komai a yi bikinmu akan lokaci da yardan Allah."

"Hmmn! haydar kenan, kana tunanin wannan yarinya ta dace da zamowa uwa ga yaranka? Kasan fa ance zina bashi ce to baka tunanin laifin kaka ya shafi jikokinta?"

Malam Abbo hallau murmushin ya kuma yi ya ce, "Zubair ina sonta, ina ƙaunarta a haka, kuma in Allah ya yarda ba wannan abu da kake fata, ita ma mahaifiyar nata Allah ya dai-daita al'amuranta ya shirya ta, in Allah yasa Faɗimah rabon Aliyu haidar ce, kuma alkairi gare ni to Allah Ubangiji ya mallaka mini ita, ya rabamu da sharrin masu sharri da masu mugayen magana irinka" ya ƙarishe maganan yana mai da kansa kan takardun gabansa yana murmushi.

Malam Zubair taɓe baki yayi ya ce, "kayi nisa baka jin ƙira, kuma koma menene kai za ka jiyo."

"Sosaima in dai akan soyayyan Faɗimah-batoola ne, to bana jin komai ba ma iya ƙira ba, ban da mastala da Ummi da kuma Malam duk nasan za su amince dan haka ma na fasa sai ta kammala makaranta, dan a bari ya huce shi yake kawo rabon wani, dan haka ana kammala musabaƙa zan fito da buƙatata in Allah ya yarda, kuma Insha Allahu zan samu karɓuwa."

Malam Zubair miƙewa yayi ya fice a office ɗin bai ce komai ba dan yana cike da haushin abokin nasa da ya kasa fahimtar sa.
Chapter 10 · 0% Book details