← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 58

Sashe 5

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hararansa Mami tayi ta fice a ɗakin, shima bin ta yayi dan yasan suka tsaya sai su ɓatawa Banafsha lokaci akan maganansu, har bakin motan ta raka sa ya shiga ta saka masa hulansa tana masa murmushinta mai zautar da shi ta ce, "Allah stare hanya ya kai ka lafiya, Allah karemun kai, a gaida Hajiya da yaranmu."

Alhaji ji yake tamkar ya É—auke ta yanzu ya kai ta gidan sa, a matsayin matar sa amma ba hali, murmushi kawai yayi ya ce, "Ameen Mamin yara sai kuma kin ganni."

Mami ta buÉ—e masa madaidaicin gate namu ya fito, sanda taga shiga na da tashin motan sannan ta kulle ta koma cikin gidan.

Tafiya muke sautin qira'an Alqur'ani mai girma na tashi a cikin motan, wanda da alama karatun musabaƙa ne dan daga yanayin karatun na gane.

Alhaji juyowa yayi ya kalle ni ganin ina bin karatun ya ce, "Karatun ya miki daÉ—i kema ko daughter?"

ÆŠaga kai nayi kawai alaman eh dan duk da kuwa sonda yake nuna mini, da kulawa tamkar yarinyar cikin sa hakan baya hanani jin haushin sa, tunda shi ma biyewa mahaifiyata yake yi suna zubar da girmansu.

Yana murmushi ya ce, "Yarinyata ce wacce ba zata wuce sa'anki ba suka yi musabaƙan, sannan ta zo ta biyu, yanzu haka tana ƙoƙarin haɗa haddan ta, sunanta Hauwa'u amma muna qiranta da Majeederh."

"Allah ya ƙara basira ya albarkaci karatu" iya abinda na furta kenan dai-dai muna shiga babban gate na makarantar mu College of health Mubi, inda nake a shekara ta biyu, ina karantan CHEW, muna a semestern ƙarshe.

Faɗa yamin na ƙara mai da hankali, sannan ya miƙa min kuɗi nayi na mashine amma naƙi karɓa, juyin duniya yayi da ni amma sam naƙi, ganin haka sai ya mayar da abinsa aljihu, ni kuma na sauƙa tare da masa addu'an a isa lafiya, shi kuma yaja motansa ya tafi.

Ajinmu na ƙarisa inda na tarar har malami ya shiga wanda ke ɗaukan mu environmental care, nan na samu waje na zauna ina sauraran karatu, sai da muka share hour guda har da ɗori kamun malamin ya juya ya fice, ina ƙoƙarin miƙewa naji mutum ya zauna gefe na, juyawa nayi ganin Umaima ce sai na haɗa fiska na wuce na fice a ajin, ina tafiya ta sha gabana ta kama kunne tana cewa, "Haba masoyiya ta Banafshaty, kiyi haƙuri mana."

Ko kallon ta naƙi yi, na juya zan ci gaba da tafiya kawai sai ta rungume ni ta ce, "Wallahi masoyiya ba laifi na bane, Ya DANISH ne ya hanani zuwa gidanku ya ce shi zai kai ni makaranta, kuma kema kinsan halinsa in naƙi zai bulale ni ne, ni bansan jaraban da ya saka shi dawowa jiya Alhamis dare-dare ba, mutumin da juma'a ma sai yamma yake dawowa."

Cikin gamsuwa da magananta na ce, "Shikkenan Umaima ya wuce, shi kuma mai niyan raba mutunci da soyayya Allah ya shirya sa, nima yau Alhajin da nake gaya miki inajin haushinsa sosai shi ya kawo ni."

Nan muka wuce ƙasan wani bishiya muka zauna, har na bata labarin kyautan da ya kawo mini da kuma labarin yarinyar sa da ya bani.

Murmushi Umaima tayi ta ce, "Allah kuwa Banafsha wannan bawan Allahn kaman dan Allah yake son Mami."

"Hmmn! Umaima kenan, in da gaske yake sonta ai sai ya aure ta, amma yake biyo ta har ya dinga kwana a gidanmu, na faÉ—a miki duk cikin masu zuwa wajanta shi kawai ke yin kwana har fin 1 wataran fa sai ya kai kwana huÉ—u har da É—aki É—ayan can nasa ne, ni ban ma san shi kuma me yake cewa matan sa ba da har yake kwanaki a gidanmu, Allah na tsani mutumin sosai."

Ganin raina na ƙoƙarin ɓaci sai Umaima ta kawar da maganan muka kama wani, har muka koma class aka ci-gaba da lecture, mu ne bamu tashi ba sai ƙarfe ɗaya ciff na rana, inda ana tashi ni da Umaima muka fito muka nemi mashine muka yi gida ba ɓata lokaci.

***
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja , a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM

07015870735
WhatsApp ko call

Ko Gmail nawa
[email protected]

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

My Queen (Aunty Mairo tawa)
My Dearest (real mum batoorl)
Hafsat Umar
Surryh baby

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 11 _ 15

Sanin halin ƴan anguwanmu iyayen sa ido sai muka roƙi mai nafen ya kai mu har ƙofan gida, hakan kuwa aka yi kaman yanda muka buƙata, muna sauƙa muka yi sallama, Umaima ta juya ta nufi gidansu, ni kuma na shige gidanmu.

Ashe mu bamu san tun sauƙanmu a mashine ya Danish dake staye a ƙofan gidansu yana kallon mu ba, Umaima ta zo shigewa gida kenan, kaman daga sama cikin stawa aka ce mata, "Keeee! me ya haɗa hanyar ki da na yarinya mara tarbiyan can?"

A razane ta juyo jin muryan ya Danish, ita duk stammaninta ya koma Camaroon É—azu, ashe yana gida, tuni hanjayen cikin Umaima suka É—uri ruwa ganin irin kallon da yake jifanta da shi.

Ya Danish kenan, saurayi chocolate color kyakkyawan gaske, wanda kana ganinsa kaga Fulanin Camaroon dan hatta dogon gashin su shi ma ya bari, idan kaga kansa sai ka ce na wata mace mai tsayin gashi ce, mutum ne mai zafin hali ga kuma ji da kai baya son reni ko kaÉ—an, ba shi ne babba a gidan ba amma za ka ranste shi ne babban su saboda halinsa.

Umaima kaman za tayi kuka ta ƙaraso gabansa ta stugunna tana cewa, "Kayi haƙuri yaya ba zan ƙara ba."

Wani mugun kallo ya aika mata kaman zai kifa mata mari, cikin ɗaga murya ya ce , "Idiotttt! ɓace mun a gani kamun na ɓalla ki, kina haɗa hanya da ita salon ace kema ba ki da tarbiya ko? kina son ki ɓata mana sunan gida."

Miƙewa Umaima tayi da mugun gudu, bata jira ya gama faɗan abinda zai faɗa ba ta shige gidannasu tana haki.

UMMU-KHULTUM ALIYU MUHAMMAD YAWONDE!
Shi ne asalin sunan ƙawata Umaima wacce ta kasance ƴar Auta a ɗakin Umma Sabeera.

Matan Abbansu Umaima, Alhaji Aliyu Muhammad yawonde biyu ne, Umma Sabeera da Ummu-khultum wacce ƙawata Umaima take takwararta, Ummu ta kasance mace mai fara'a da sanyin hali, ga sanin ya kamata ga kuma haƙuri ba ruwanta haka yaranta ma ba ruwan su, saɓanin Umma Sabeera da take masifaffiya ba haƙuri kuma bata ƙaunar kowa sai nata bata son reni amma yaranta basu iyo halinta ba.

Umma Sabeera ita ce Uwar gida, yaran ta huɗu, Yaya kabeer wanda muke qira da Yaya babba, sai ya Danish, sai Ya mus'ab sai Autar su ƙawata Umaima, duka yaran Umma Sabeera sanyin hali ne gare su tamkar Ummu ce mahaifiyar su ba Umma ba, musamman dai Umaima takwara ga Ummu wacce kamun awa Ummu takwarar ma sai da aka sha daru da Umma Sabeera akan ta ya za'a sanya wa yarinyarta sunan kishiyar ta.

Ya Danish shi ne kusan ya ɗauko rabin halin Umma Sabeera amma dai ba duka halin nata ya ɗauko ba, dan shi yana da haƙuri kawai ya cika faɗa ne da kuma rashin son reni.

Ummu kuma yaranta uku 3 ne, Yaya Farooq wanda yake babban yaronta sai kuma Yaya sadeeq sai kuma Æ´ar Autar ta Balkisu wacce ake qira da NANA

Yaran Ummu ba ruwan su kaman Ummu haka suma suke da sanyin hali, idan ka shigo gidan za ka ɗauka duka yaran gidan yaranta ne, dan ba ruwan Ummu da banbanci ko wani abun, duk da Umaima ta girmi Nana, amma duk abinda za ta yiwa Nana sai ta yiwa ƙawata Umaima, wani lokacin ma sai ta saya ma Umaima abu ba tare da ta saya wa yarinyar ta ba.

Tun da na taso a anguwan nan na ganmu kuma naga Ummu kan shigo gidanmu lokaci zuwa lokaci inda har ƙawance ya shiga tsakanina da Umaima tun muna yara har Allah yasa muka girma, amma Umma Sabeera da ya Danish kwata-kwata basu son ganin Umaima tare da ni, ita kuma Umaima ƙaunata take dan Allah soyayya ce da aminta stakaninmu ba kaɗan ba, tun daga primary school har secondary har zuwa yanzu da muke matakin gaba da secondary duka makaranta ɗaya muke yi kuma aji guda, haka a ɓangaren Arabic ma makaranta guda muke, ƙawata Umaima na da ƙwaƙwalwa nima hakan shiyasa ko a makaranta kullum mune a gaba.

Duk gidan nasu kyawawa ne dan Abba suka ɗauko amma kyawun ya Danish ya fita daban dan shi kaman ya haɗa dangi da baƙaƙen larabawa amma bafulatanin Camaroon ne su gaba da baya, Abba da Umma Sabeera ƴan camaroon ne Ummu ce kawai ƴar Nigeria anan cikin Mubi amma ita ma bafulatana ce.

Kowa na sona a gidan su ƙawata Umaima, banda Umma Sabeera da kuma ya Danish wanda su biyun nan har ƙirana da sunan da nafi stana a rayuwata suke yi, wato ƴar karuwa.
Chapter 5 · 0% Book details