← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 58

Sashe 14

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina juyawa kuwa idanuwana karaf a cikin na Ya Danish, wani killer smile na sakar masa tare da cigaba da tafiya na, wannan karon ma ƙwafa Ya Danish yayi, wanda ya sanya su Ya Farooq bin inda yake kallo da idanuwansu, Ya Farooq suna ganin ni ce sai kawai suka yi dariya, daga Ya Farooq har Ya IB sun san za'a rina, Ya Farooq ne ya ƙwala mini ƙira tare da cewa Ya Danish, "Amma dai ka ji jiki wallahi, Allah taro ka Danish, ka saki ranka ka daina haushi da yarinya a banza, ita bata damu da tsabgarka ba amma ka bi ka azalzali yarinya."

Ya Danish kallon banza ya yiwa ya Farooq tare da yin ƙwafa, ni kuwa ganin ya Farooq ne ya ƙira ni sai na taho cikin tafiyana ta nistuwa da ɗaukan hankali, har na iso inda suke zaune, ɗan rusunawa nayi na ce, "Ya Farooq ina wuni, Ya IB barka da yamma."

Ya Farooq da Ya IB duk amsawa suka yi da murmushi, Ya Farooq ya ce, "Daga ina haka da yamman nan sistor?"

Langwaɓar da kai nayi gefe guda tare da kulle idona ina murmushi na ce, "saurayina ne ya zo zance, shi ne na rakasa."

Tun kamun na rufe baki ya Danish ya ja wani dogon tsaki, daman shi kaÉ—ai ya ganni basu ganni da saurayin ba, kuma ga haushin na gaida su ban gaishe sa ba saboda na renasa, Ya Farooq ko kallon Ya Danish bai yi ba duk da yasan yayi tsaki, murmushi ya sakar mini ya ce, "inye! Su sistor har an girma an yi saurayi, daman Umaima ta faÉ—a mini gobe za ku fara exam's, ashe next year ana gama school sai biki kenan?"

Rufe fiskana nayi da tafin hannayena sannan na Jinjina kai alaman eh, Ya IB ne yayi dariya ya ce, "Yaran yanzu ba kunya, har da kai kike É—agawa, shikkenan Allah nuna mana da rai da lafiya, Allah tabbatar da alkairi."

Da "Ameen" na amsa ina yin ƙasa da kai na tare da wasa da yastu na, Ya Danish da ya cika ya gama cika, wani banzan tsawa ya mini ya ce, "Keeeeeeeeeeee! Dallah ɓace ma mutane a kai, 'yar iska kawai, shashasha ƙwaila, mara tarbiyya."

Duk da storon da stawan nasa ya bani amma hakan bai saka na tafi ba sai da na tsaya na sakar masa wani killer smile É—in, na kashe masa ido guda na ce, "ai ba'a É—an iska É—aya, sai dai biyu, kaga kuwa ni kaÉ—ai ba iya yin iskancin da kai na zan yi ba, dole tare da kai nake yi" Ina gama faÉ—an haka na juya na shige gidannasu, hankalina kwance.

Ya Farooq da Ya IB duk dariya suka kama yi, suna faÉ—in ai ga abinda suke guje masa kenan, ga shi tun ina storonsa amma ya saka na daina storonsa balle storon faÉ—a masa magana, na gaishe da kowa amma banda shi, kuma duk shi ya jawo ba kowa ba.

A tsakar gidan na haÉ—u da Umma Sabeera, É—an rusunawa nayi na gaisheta amma ta aika mini da harara ta ce, "Ke dan uwarki karuwa ki fice mana a gida tunda ba gidan ubanki ba ne.."

Kamun ta ƙarisa maganan tuni muryan Abbaa ya dakatar da ita, ta hanyar cewa, "Sabeera ki fita a idanuwana na kulle, ke Faɗima maza zo ki shige inga gidan nawa ne ko nata, idan ta isa ta hana wanda na bari ya shiga gidan."

Kai na a ƙasa ba tare da damuwa ko ɗigo a fiskana ba, na gaishe da Abbaa ya amsa, sannan na miƙe na shige gidan ina magana a zuciyata ni ɗaya, ba dan Umma Sabeera na cin albarkacin Umaima da Abbaa ba, ai da tuni ita ma na fara kasa mata hali na tasan banda sauƙi, ni ɗin do me i do you ce, back to back aradu, kana mini ina ramawa ba barin bashi kuma ba ruwana da girmanka.

Abbaa ya dubi Umma bayan shigewana ya ce, "Sabeera indai kina da kunya to kin ji shi, ƴar cikinki amma kike mata abu kaman sa'arki, yanzu da ta rama zagin fa? Ƙawar ƴar ki ce fa ba wai babbar mace ba ce, ki gyara halinki idan ba haka ba wallahi za ki sa nayi abinda ban yi niya ba, indai akan mahaifiyarta kike wannan abun, to sai na aure ta naga abinda za ki yi, ko kuwa na zama dadironta na ga ƙarshen rashin tunaninki da rashin hankalinki..." haka Abbaa ya dinga yiwa Umma Sabeera faɗa kaman wanda aka aiko sa da wahayin faɗan, ita kuwa Umma wani irin stanata ne ya ƙara rufeta, tana jin za ta iya kasheni ma akan abinda Abbaa ya faɗa, na ya haɗa alaƙa da Mamina.

Ni kuwa ina shigewa ciki na gaishe da Ummu sama-sama, da yake nasan abinda na shuka a waje da wuri na fito na ce Umaima ta zo ta rakani, so nake kamun Abbaa ya fita na gudu gida, idan ta Ya Danish ne banda mastala zan iya tsayuwa mu daku ma, amma kuma Umma ita nake shakka saboda mijinta da 'yar ta, kada ta ce za ta taɓa ni kuma ba iya ƙyalewa zan yi ba.

Umaima sai mita take daga zuwana zan tafi, ko labarta mata yanda muka yi da Malam Abbo ban yi ba, haka dai na yafito ta muka fito, Allah ya taimaka lokacin Umma ta shige ɗakin Abbaa da ke ta cikin gidan, hamdala nayi muka nufi waje, muna ficewa a gidan kuwa muka kusa yin karo da Ya Danish, wani mugun kallo ya aikawa Umaima amma ta kawar da kai kaman bata ga ni ba, tsawa ya daka mata da mugun ƙarfi ya ce, "kin juya kin koma gida ne ko sai na iso wajan na ɓaɓɓallaki? Ban hanaki haɗa hanya da yarinyar nan ba?"

Kamun mu yi wani mosti sai muka kuma jiyo muryan Abbaa, ashe yana bayanmu bai fita ba, dan-ƙwalo ya aika wa Ya Danish, sannan ya ce, "ke Umaima wuce ku tafi, idan kun je ki kwana a can, sai naga ko akwai wanda ya haifa mini ke, da zai mini iko da yarinya."

Fakan idon Abbaa nayi na murguÉ—a wa ya Danish baki tare da gwalo, na kuma masa magana da ido wanda na tabbata ya fahimci abinda nake nufi, daga kallon da ya mini, jan hannun Umaima nayi muka yi wa Abbaa sai da safe muka wuce gidanmu, shi kuma ya Danish fasa shiga gidan yayi daga wajan ya shige motansa yayi gaba saboda Ya Danish akwai zuciya, Abbaa ma wucews inda zai tafi yayi.

Malam Abbo tun da ya juya ya tafi babu abinda yake tinanowa sai murmushin da Banafsha ke sakar masa, da kuma kallon da take masa, tuni ya ƙara matowa a kanta, nan ya ci alwashin ya kusa bayyanar mata da saƙon zuciyarsa.

Muna shiga gidanmu Umaima ta dinga dariya kaman ba lafiya ba, kallonta nayi na ce, "an fara sanyi kuma ai, hauka ta fara mostawa."

Tana dariyan ta ce, "Masoyiya ba za ki fahimta ba, ni ba haukar ce ta mosta ba, abinda Abbaa yayi ne ya mini sweet, ga shi Ya Danish ya ja an ce na kwana anan, wayyo mi farinciki kashe ni, yau za mu kwana karatu saboda peppernmu na gobe, Allah ya yiwa Ya Danish albarka, Allah ya sa watarana Umma ma tayi a gaban Abbaa, ya ce ya bawa Maminmu ni kyauta, heee!hu!hu!"

Hararan Umaima kawai na yi muka shige palourn namu, ban sanar mata abinda ya faru stakanina da Umma ba ɗazu, domin duk son da Umaima ke mini to fa uwa-uwace, kuma wannan ba baƙon abu bane, hantara daga wajan Umma da Ya Danish ba sabo bane a wajena.

Da sallama muka shiga palourn amma ba kowa shiru, É—akina muka wuce direct muka yi alwala tare da yin sallah, mun idar muka fito palour muka samu Mamina zaune tana cin abinci, ganina da Umaima bata yi mamaki ba, kuma bata tambaya ba, domin ba wannan ne karo na farko da Umaima ke kwana a gidanmu ba, ni ce kawai Mamina bata barina na kwana a gidan su Umaima saboda wai gidanmu ya mata girma ita kaÉ—ai, ta fi son tana jin mostina.

Mami ta sani na ɗebo mana namu abincin, muka ci muna kallo hankali kwance, hira muka ɗan taɓa da Mami sannan nake faɗa mata ma yanda muka yi da Malam Abbo akan maganan musabaƙa da hukuncin makaranta, da mamaki dai na kalli Umaima hankalinta kwance bata tashi hankali ba, Mami ce dai ta nuna ɗan damuwanta sannan ta mana faɗa sosai akan mu dage mu mayar da hankali, ta kuma ƙara mana da nafilfilu da kuma addu'oe da za muyi saboda exam's da za mu fara gobe da yardan Allah, ba mu wani jima ba na tashi na shige ɗaki bayan na yiwa Mamina sai da safe, ina shigewa Mami ta dubi Umaima ta ce, "yarinyar Mami kada ki sanar da ita gaskiyan abinda ake ciki, ki ƙyaleta dai ku dage ku mayar da hankali, kinga yanzu ta saki ranta, nasan idan ba ta haka aka ɓullo aka mata wayo ba, to Banafsha ta dinga cin rai kenan."

Murmushi Umaima tayi ta ce, "Insha Allah! Mami ba zan sanar mata ba, zan dai nuna mata nima na damu mu ƙara mayar da hankali."

"Yauwa ƴar kirki, Allah muku albarka duka ya ba ku sa'a ku ciyo na ɗaya a musabaƙa, flying color result a boko" cewan Mami tana murmushi.

Umaima amsawa ta yi da, "Ameen" sannan ta yiwa Mami sai da safe ta shige É—akin Banafsha, Mami ma hamdala tayi sannan ta kashe kayan kallon ta koma nata É—akin, sai da ta gabatar da shafa'i da wuturi da wasu nafilfilun sannan ta kwanta.

Na fito wanka ina ƙoƙarin shumfiɗa darduma Umaima ta shigo, kallon yanayin fiskanta ya sa na tambayeta ki lafiya, cikin damuwa Umaima ta ce, "Masoyiya maganan musabaƙan nan ne ya dame ni."
Chapter 14 · 0% Book details