Sashe 47
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Magiyan duniya su Banafsha sun yi, amma amsa guda Nurses ɗin ke basu, ba'a amsan irin wannan mastalan ba tare da police ba, domin yan da mace-mace ke yawa ana ɗaure likitoci basu ji ba kuma ba su gani ba to dole sai da shedan police, dan ko ma mene ya biyo baya to dai ba za'a ga laifin likita ba balle har a ɗaure sa, Abbaa ransa ne yayi mugun ɓaci, dan haka ya sa Ya Sadeeq ya dubo musu wani likita abokin ya Farooq, Abbaa kuma ya ɗau waya ya ƙira babban yaya ya kuma faɗa masa ya turo musu police tukunna.
Banafsha fa ta ƙulu ta kai wuya cikin karaji da masifa ta fara balbala bala'i, cewa take, "Amma dai wallahi ku kam an yi marassa imani, marassa tausayi, asararru kawai, daman dan uban me kuka yi karatun naku, kuma aka baku daman aiki a asibiti, gomnati ta gina asibiti kuma ta ɗauke ku aiki, take biyanku albashi, ba duk dan al'umma ba? To in Allah ya yarda Mamina ba abinda zai sameta, shegu, munafukai, marassa imani, ƴan uwan fir'auna kawai, kuma nima zan zama likitan nan, aka kawo mamanku duk ni da kai na zan ƙarisa su...." masifa kawai Banafsha ke yi, kaman wacce aka aiko daga sama, Abbaa sai tausanta yake amma ta ƙi yin shiru, kuma a dai-dai lokacin Bunayd da ya ga duk abinda ke faruwa, ya iso wajan rai a ɓace.
ACM Bunayd ko kallon inda Banafsha ke masifanta bai yi ba ya kalli Abbaa, a ɗan daƙile ya ce, "sorry Sir! Za'a dubata yanzu."
Shi da kansa ya tura gadon Mami, sai sauran sojojin suka zo da gudu suka amshi gadon suka tura, likitan da ke duba Abeed ne ya fito, ganin su da wata patient É—in, take ya saka aka kai ta É—akin ba da agajin gaggawa ba tare da ya tambaya ba ko ya ce wani abu.
Abbaa kaman zai rungume Bunayd ya ce, "Allah maka albarka likita, mun gode, Allah saka da alkairi ya rufa asiri duniya da lahira, idan ana samun irinku a likitoci ai ba wanda zai mutu saboda irin haka, sai dai in lokacinsa ne yayi, Mun gode bawan Allah" Abbaa ya faÉ—a dan duk É—aukan sa Bunayd irin likitoci masu taimako da tausayin nan ne.
Bunayd murmushin da ko leɓensa bai kai ba yayi ya ce, "Ba komai Sir, your welcome."
Banafsha tun da aka yi gaba da gadon da Maminta ke kai sai ta kuma ƙaro sabon walaƙanci, duban Nurses ɗin ta yi ta ce, "Munafukan Allah to ahirr ɗin ku za'a duba Mamina, kuma ba ɗan banzan police ɗin da za mu ƙira balle kuma Soja, ƴan baƙin ciki kawai, so suke na zama marainiya gaba da baya ba uwa ba uba, to ta Allah ba ta ku ba..." Masifanta ta ci gaba da yi har ta ƙarisa wajan su Abbaa.
Duk abin da Banafsha ke faɗa a kunnen Bunayd yana ji, surutun nata bai dame sa ba tun da ya saba da na ƙannensa, amma maganganun nata ma dariya yake basa, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai kaman bai kalleta ba yana yastina fiska, ba tare da ta masa godiya ba ta wuce su ta ƙarisa ƙofan ɗakin da ta ga an shigar da Maminta, bata hango kowa a ciki ba sai Maminta, juyawa ta yi kuma kaman za ta yi kuka ta ce, "Abbaa ka ga mugaye, su ma ba dan Allah suka karɓe ta ba, ga shi sun ajiye ta ita kaɗai, so suke ta mutu, wayyoo ba'a ƙaunata ana son Mamina ta mutu."
Abbaa ƙarisowa yayi wajanta ya ce, "ki yi shiru Faɗima, wannan likita mai mutuncin ya sa za'a dubata kin ji."
Banafsha kwaɓe fiska ta yi ta ce, "tun da dai ba zai duba Mamina da kan sa ba, to ba shi da wani mutunci shi ma, shi ɗin banza, to ya duba ta da kansa mana indai da gaske yake yana da imani kuma shi na gari ne ba kaman sauran ba, ni wallahi ba za'a yaudareni a banza ba a bar uwata ta mutu ba, aikin banza daga shi har sauran har Umma duk in Mamina ta mutu sai na yi Shari'a da su, ko kuma na bi rana na kashe su, bin dare ma ai storo ce, ni da ranan Allah ido na kallon ido zan ƙaddamar musu."
Tana rufe baki sai ga likita ya iso wajan da sauri, bai shiga É—akin da Mami ke ciki ba ya wuce inda zai kai sa É—akin da Abeed ya ke, da sauri Bunayd ya stayar da shi, cikin turanci ya masa magana akan tun da sun yi aikin Abeed É—in su duba matar mana kada a rasa ta.
Likita duban Bunayd yayi ya ce, "sorry Oga, an mata abinda ya kamata, raunin nata ba sosai bane, idan muka gama da shi za'a dubata."
Kamun Bunayd ya buɗe bakin ba da amsa, tuni Banafsha ta diro a gaban likita idanuwanta rufe ta ce, "wallahi ƙarya kake, maƙaryacin likitan da bai san aikinsa ba, wuƙa aka yage Mamina da shi, kuma ka ce raunin ba sosai ba ne, kai kasan jinin da ya fita a jikinta ne ma, wa ma ya sani ko har kayan cikinta sun yanyanke, to nima ɗalibar malaman lafiya ce, ina College kuma ina last year, dan haka kada ka wani faɗa mana ƙarya mun san me ne a aikin muka, kuma ba inda za ka tafi idan ba ka shiga ɗakin da aka kwantar da Mamina ka duba ta ba."
Daga likita har Bunayd baki suka sake suna kallon ikon Allah, ganin yanda budurwan ta dage da masifa iya ƙarfinta, likitan ya kasa haƙuri sai da ya dara ya ce, "To masifaffiyar likita, tun da kinsan komai kuma kin kusa gama College sai mu baki kayan aiki ki duba Momin taki ko."
Banafsha sai kuma ta shagwaɓe ta ce, "dan Allah duba Mamina ka ƙyale wancan ɗin, ai shi ma ka duba sa, ka koyo adalci mana likita, ai in ba ka practicing to ba za ka iya riƙe mata biyu ba, kawai Mami ma s dubata tun da shi ma an duba sa."
Bunayd bai kalli Banafsha ba, amma yana sauraranta, ji yake kaman ya kwanta a ƙasa ya ta dariya har cikinsa yayi ciwo, wai ai ta kusa gama College ita ma likita ce, murmushi yayi har sai da haƙoransa suka bayyana, sannan ya kuma magana da turanci ya ce, "ka turo wani likitan ya duba ta, please a yi a gama da Captain namu dan transfer muke so a mana zuwa Kano."
Banafsha ma ta ƙi kallon Bunayd, likitan take kallo ta ce, "wallahi ban yarda ba, ni kai ka mini, kai nake so ka duba Mamina, wani likitan ya je ya duba Captain ɗin nasu, tun da ba mu na Captain namu bane, ni Mamina ce Captain tawa."
Bunayd murmushi ya kuma yi tare da yi wa likitan magana da ido, sai ya juya wajan Abbaa da yayi poster yana ganin ikon Allah, Abbaa bai taɓa sanin haka Banafsha take ba sai yau, Bunayd murmushi yayi ya ce, "ina so za mu yi magana Sir."
Abbaa gefe suna yi da Bunayd, ya ce, "Ina sauraranka likita."
Bunayd kiston kan sa ya shafa ya ce, "Sir ni ba likita ba ne, ni Soja ne, muma mun kawo wani É—an uwanmu ne ya samu hatsari."
Abbaa baki ya buɗe ya ce, "Ai ko na ji, amma dai kai a sojojin ma daban kake, ai ko likitoci ka fi su imani da tausayi, Allah kuma ya basa lafiya, ka yi haƙuri da shirmen Faɗima, ba haka take ba kawai abinda ya samu mahaifiyarta ne ya rikita ta haka."
Bunayd cewa yayi, "Ba komai..", zai yi magana sai ƙira ya shigo wayan Abbaa, haƙuri Abbaa ya bai wa Bunayd sannan yayi picking, "ina cikin asibitin kuna ta ina?" Faɗin Abbaa da ke kare da waya a kunnensa.
Yaya babba ya ce, "Abba ka fito bamu san a ciki ta ina ba."
Abbaa ya ce, "To ganinan", yana faÉ—a ya kashe wayansa, sannan ya dubi Bunayd ya ce, "bawan Allah bari na zo, Yarona ya taho da polisawan ne."
Bunayd gyaÉ—a kai kawai yayi ya juya wajan likitan.
Likita dan dolensa sai da ya shiga É—akin da Mami ke kwance, sannan ya fito ya tafi É—akin da Abeed ya ke, jaraban masifan Banafsha dariya ma yake basa, sai ya ji ta burgesa.
Bunayd bayan ya je office na likitan, bayani ya masa dangane da Abeed, akan sun yi duk abin da ya kamata, gobe ma za su iya ɗaukan sa su tafi Kano ɗin, harbin bai yi muni sosai ba a cinya ne kuma an cire alburushin, sai su ƙarisa jinyan a asibitin Kano, dan zai fi samun kulawa sosai ma, Bunayd hamdala yayi, sannan ya ce, "likita wannan matar fa?"
Murmushi likitan yayi ya ce, "Ni da farko na É—auka ma ai duk tafiyanku guda, sai da masifaffiyar likita ta yi bayani" likita ya faÉ—a yana murmushi.
Bunayd murmushi shi ma yayi dan ya tuna kalaman FaÉ—ima, kaman yan da ya ji sunanta a bakin dattijon É—azu, cewa yayi, "likita, ita ya nata condition É—in? Komai zai tafi dai-dai a nan ko ita ma a sanja mata asibiti, ko da a cikin Yola ne."
Murmushi likitan yayi ya ce, "a'a Oga, ita matar fa kaman yan da na faɗa raunin nata da sauƙi, anyi niyan caka mata wuƙan a ƙirji ne, amma sai ya kauce ya kar ci cikinta, bai ma shiga sosai ba, sai dai daman abin da ya sa muke so a ce sun zo da police saboda maganin samun mastala ne, ya kamata wanda ya mata haka a hukunta sa, dan gaskiya kasheta aka yi niyan yi, amma aka bar ta a nan asibitin ma komai zai tafi dai-dai, in Allah ya yarda za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu muyi duk abinda ya kamata."
Bunayd gyaÉ—a kai yayi ya ce, "good, Allah bata lafiya" yana gama magana ya sallami likitan ya fita, lokacin dare ta yi sosai-sosai.