← Book details Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 58

Sashe 2

Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin yanayi na rarràshi ta ƙira sunana ta ce, "Masoyiya Banafshaty."

Jin sunan da ta qira ni da shi sai da na ɗan murmusa dan kuwa Allah ya gani ni da Umaima ba ƙaramin ƙaunar junan mu muke ba, duk irin halayyan mahaifiyata da yacce ake yama-ɗiɗi da ni a gari hakan bai dame ta ba ko kaɗan dan Allah take ƙaunata nima dan Allah nake ƙaunarta, duk gidansu suna ƙaunata illa iyaka yayansu ɗaya da ko giftawa nayi sai yaja staki in kuma ya ganni da Umaima to ranan sai tasha na jaki idan dai ba wai Ummu na gida bane ta gani ta hanasa, gaba ɗaya ya staneni shi da mahaifiyarsa, ba iya su ba kowa a anguwar kallona yake da laifin mahaifiyata kowa ɗauramun laifin da ban taɓa kusantan shi ba yake yi, in ka cire wannan gida to ba gidan da nake shiga a anguwan mu, kuma bayan Umaima ba ni da wata ƙawa ko a makaranta.

Cikin sigan wasa na harari Umaima na ce "Ba wata Masoyiya atou kar ki yaudare ni, kin tashi kin kama hanya kin tafi aiken Ummu ke kaɗai wato salon asa miki albarkan ke kaɗai ba, irin ba amanan nan, shi ne za ki wani ce mini masoyiya to na ƙi", na juya ga Ummu nace "Ummuna ai dai tare za ki raba mana albarkan ko?"

Ummu na murmushi ta ce, "Dai-dai wa dai-da ma kuwa Banafsha 'yar Ummu."

Murmushi nayi, ƙawata Umaima ta riƙe hannuna ta jani har cikin ɗakin su ta zaunar da ni a bakin gado ta ta ce, "Wai yanzu ke ni za ki cewa yaudara amma dai kinsan ƙaunar da nake miki na amanane ko?"

Kukan da nake dannewa ne ya samu nasaran kuɓucemun, sai kawai na rungume Umaima ina kuka mai cin zuciya.
Hankalinta ya tashi ita ma a take idanuwanta suka kawo ruwa sai hawaye kuma, bubbuga bayana take yi cikin sigan rarrashi ta ke cewa "Kiyi haƙuri haka dan Allah masoyiya, kukan da kike yi yana yawa ko so kike hawayenki ya ƙare ne? dan Allah kibar kukan nan bana so please Banafshaty."

Cikin kukan na ce, "Umaima ya zan yi da rayuwa ta? Ya ake so nayi ne? Ni ji nake mutuwa ma tafi mini wannan ƙazantaccen rayuwan, dan Allah ace uwarka ta rasa abun yi sai karuwanci kuma a haka Mami ke cewa sana'a ce wai dama karuwanci sana'a ne? Mami ta ce bata so aci mutunci na ko a lalata mini tarbiya shi ya hanata zama haka ta kama wannan sana'a dan Allah wannan shi ne soyayya Umaima? Ta kwaɓar da mutuncinta sannan ta kwaɓar da nawa, shi fa mutunci Madara ne, a abinda Mamina ke yi wa zai ganta da mutunci idan ba ni da ya zamo mini dole ba?" duk cikin mastanancin kuka nake wannan magana wanda i zuwa yanzu kai na mugun sara mini yake yi kaman na cire kan na huta.

Umaima ta ce "Banafshaty dan Allah ki yi haƙuri haka nan, ni dai mu ci gaba da addu'a komai zai wuce kin ji, kuma Mami na sonki fiye da yanda take faɗa ma dan Allah kiyi haƙuri kina addu'a kina kau da kai kinji" ta faɗa tana sharemun hawayena.

Lumshe ido nayi nace "Umaima in dai wannan ce soyayya to tirr! da soyayya, Allah wadaran soyayya, bana son soyayya, bana ƙaunar soyayya, na tsani soyayyan, Umaima ko na kau da kai kan baya kauduwa domin muddin ina gida wani zai zo wajanta to sai naji zuciyata na tafarfasa zuciya ta kaman ana wastamun ruwan zafi zuciyata kaman ana ƙonemun ita, ji nake kaman na kashe kaina na huta, wallahi ba dan kisan kai zunubi ne babba ba da na jima da kashe kai na dan da wannan rayuwa gwanda na mutu na huta, Umaima imagine wai har YA DANISH shiima zai ce mun 'YAR KARUWA, stana da cin mutuncin ya wuce mutanen waje ya koma har kan mutanen gida suna min wannan wacce iriyar rayuwa ce?"

Fashewa nayi da kuka mai ciwo tuno abinda ya faru É—azu sai na ce, "Umaima kinsan me ya faru É—azu?"

Girgiza kai tayi tana hawaye dan maganan ya Danish ya mata ciwo ita ma sai ta ce, "Banafshaty kar ma ki faɗa min me ya faru kinji, yacce kike shanyewa ki shanye kawai, saboda ciki ba dan tuwo kawai aka yi sa ba ki yi haƙuri za ki ga riban haƙurin da muke cewa kiyi kullum da yardan Allah, babu jimawa za ki ga sakamakon Ubangiji akan jarabtar da ya miki."

Hannunta na riƙo ina hawaye na ce "A'a Umaima, ko kaɗan wani abun ba zai riƙu a ciki ba dan riƙuwan sa tabbas masifa ne, haɗiye wani abun to barazana ce ga lafiyan mutum, kaman kai ne ka samu guba ka cusa a cikinka kuma ka ƙi zuwa asibiti a baka taimako, Umaima idan ban faɗa miki ba bazan ji sanyi a rai na ba wallahi ba abinda zan ɓoye miki a rayuwata indai bai kauce sirrin da Allah ya ce ya zama sirri na ba, wanda wannan nasan babu shi a kai na nikam, Umaima wai ɗazu fa ina kwance a ɗaki na ina bita haddan da ya rage mana kawai naga mutum ya faɗo mini ɗaki daga shi sai ɗan gajeren wando, wai yana tambaya ta ina Mami na ta tafi a hannu yake sauri yake" kuka nake sosai nace "Umaima kiji fa wai har ni ya ke gayawa wannan magana, to wallahi idan ita Uwata na haƙura ban ɗau mataki ba dan Uwata ce to su na kusa fara ɗaukan mataki a kansu in ta kama in kashe mutum in yaso nima a kashe ni, yaro ya zo babba ya zo dattijo ya zo stoho ya zo, Mami har da wanda ta kusa haifa take kulawa wannan wacce rayuwa ce? Haka da safe wani saurayi ya fito ɗakinta ina stugunne ina aiki kawai naji an zame mini ɗan-kwali ɗan iska wai gashina na burgesa irin na mamata", kuka nake sosai idan na tuna wasu abubuwan.

Ƙawata Umaima rarràshi na ta ci-gaba da yi kawai dan ita ma abun sosai yake damun ta, ba ɓata lokaci zazzaɓi ya rufe ni ruf-ruf nan take na fara tari wanda nake ji tamkar zuciyata zan amayo dan azaban da nake ji a ƙirji na, hawaye nake ina tarin, wanda hakan ya storita Umaima, cikin ruɗewa ta fice ta ƙira Ummu suka shigo tare, Ummu ma ta ruɗe amma duk da haka ta mini faɗa na daina saka damuwa a rai na, sai da ta gyara mini kwanciyana ta lulluɓe ni sannan ta fice dan ta ɗauko mini magani, Umaima kuma tana zaune a gefe na tana aikin jero mini sannu tana hawaye.

Ganin tarin yaƙi stayawa sai Umaima ta dube ni cikin tsananin kuka ta ce, "Banafshaty wallahi idan kika ja abu ya same ki ba zan taɓa yafe miki ba" tana gama faɗa kawai ta fashe da kuka mai nuni da tausayina da take ji, ta rungumeni nima kukan nake jikina sai rawa yake yi ga kuma ya ɗau wani azababben zafi kaman garwashi.

Wannan littafi FREE BOOK ne in Allah ya yarda, dan Allah fan's ku nunamin soyayya kaman ko yaushe, sharhinku shi ne ƙwarin guiwa na, bana son tnx Sharhi nake so, ban yi niyan yin sa a paid ba kuma bana so ya koma paid, love U all My fan's ♥️

***
INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM

Ko
07015870735
WhatsApp and call

Ko Gmail nawa
[email protected]

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝

# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
👄'YAR KARUWA👄💅

Officially

𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)

SADAUKARWA NE GARE KI
Baby batoorl (my unborn favorite soul)

TUKUICI NE GARE KA
SIR Abubakar Sadeeq CEO lafazi writer's association (gidan karamci)
Da kuma É—aukacin member's namu.

PAGE NAKU NE

Ƙanwa eclemah (Amarya)
Fatan ayi biki lafiya a gama lafiya, Allah ba da zaman lafiya, ya sa É—akinki ne har mutuwa, congratulations.

My Heartbeat (ukhtynh)
2 month's Anvsy. Allah ya ƙaro zaman lafiya da ƙaunar juna ke da sweet babynki, Allah ya raba lafiya 🤣

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله SAW 🖤🤍

🅿️ 6 _ 10

A Haka Ummu ta shigo ta same mu muna ta aikin kuka, Umaima nayi nima ina yi kuma har yanzu ina fama da tarin da kuma zafin jikin, Ummu ganin haka rai ɓace ta rufe Umaima da faɗa sannan ta ɗaga ni ta bani magani, da ƙyar na haɗiye maganin kaman zan amayo da 'yan hanji na, Ummu koran Umaima a ɗakin tayi ta dinga shafa min kai na ba jimawa bacci yayi gaba da ni ina ta faman ajiyan zuciya, sai da nayi bacci sannan Ummu ta miƙe ta fice tana bina da addu'a.

Umaima taya Ummu aiki ta yi har dai lokaci ya ja, na sha bacci na sosai duk da ba na daɗi ba ne, sai can yamma na farka, kuma a dai-dai lokacin Umaima ta shigo fes da ita dan har ta yi wanka, a kan ta na sauƙe idanuwa na da suka mini mugun nauyi, murmushi ta sakar mini tana tambayan ya jikin nawa, da kai na bata amsa na kuma mayar da idanuwana na lumshe su in ambaton Allah a zuciyana dan har yanzu ba wai naji abinda ke damuna ya tafi duka ba ne.

Muna ɗaki Mamina ta shigo cikin gidan, a palour ta samu Ummu zaune tana waya, Ummu kaste ƙiran tayi ta tari Mami da murmushi suka gaisa, Ummu ko kaɗan bata cewa Mami komai akan abinda ya faru ba dan kuwa in da sabo to an saba da hakan tsakanina da Mamina.

Mami ce ta numfasa tare da cewa, "Ummu ina yarinyar taki ta shiga?"

Ummu na murmushi ta ce, "suna É—aki da mutumiyar ta, da bacci take yi amma ina ji yanzu ta tashi dan na jiyo mostinsu."
Chapter 2 · 0% Book details