Sashe 23
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan wani lokaci su Banafsha suka cigaba da zuwa tahfiz, kuma a lokacin hutun boko ya kusa ƙare wa, a haka har sakamakon musabaƙa ya fito, Banafsha ce tazo ta ɗaya, sai Umaima da wata yarinya daga wani makaranta daban suka yi bracket suka zo na biyu, makarantar su Banafsha dai su ne na farko, sai makarantar su ɗaya yarinyan su kuma na biyu, haka dai har wanda suka zo na ƙarshe, kuma an yanke a iya na ɗaya zuwa na biyar ne za'a je na jiha da su nan gaba, dan wannan da aka yi iya na cikin mubi ne, yanzu nan gaba na Adamawa State gaba ɗaya za'a yi kamun kuma aje ga na State da State, wannan nasara ba ƙaramar daɗi ta yiwa malaman su Banafsha ba, kyautar da suka ciyo kuma anbar wa makaranta za'a ƙara gyara abubuwan da ya kamata.
Sai da aka kwashe wata guda Ya Danish bai kuma zuwa weekend ba, wanda ganin haka sai Banafsha ta cigaba da shiga gidan, saboda Abbaa da kansa ya bata haƙuri kuma ya ce kada ta yarda ta ce za ta daina shigowa, ita ma gidansu ne kuma shi mahaifinta ne, Umma dai taƙaici kaman ta kashe kanta, duk da girman Umaima kuwa hakan bai hanata jibganta muddin ta gansu da Banafsha, Ummu abun ya isheta dan haka ta yanke hukunci, ta samu Abbaa ta faɗa masa ita dai a shawaranta tana ganin ya auri Mamin Banafsha kawai, Abbaa ba ƙaramin daɗin shawaran Ummu ya ji ba, tunda ita da kanta tayi maganan to yasan ba za ta kawo masa mastala ba, ya amsa shawaran zai auri Mami ko dan Umma ta gyara halinta, dan yasan tabbas ya auri Mami to Umma za ta dawo hayyacinta, sannan ya faɗa mata shi ma zai ƙira Danish ya fito da mata yayi aure, tunda iskanci yake ji, abin nasa tun daga gida zai fara danne yaran mutane, to bai isa ba gwanda yayi aure kamun ya jajuɓo musu abin kunya, nan ma Ummu tayi na'am da wannan hukuncin, ta bisu da addu'an alkairi a cikin lamarin auren daga na Abbaa har na Danish ɗin, amma tare da Farooq za'a haɗasu su fito da matan auren, tunda daman sa'anni ne su ɗin, wannan hukunci Ummu da Abbaa suka yanke, da yake Ummu matar rufin asiri ce kuma mace ce ta gari fatan samun ko wani namiji, shiyasa take ta daban a wajan Abbaa, ita ya aura daga baya, amma baya jin zai iya samun wata kamarta, sosai Abbaa ke ƙaunar Ummu, kuma halayyanta masu kyau ne suke jawo hakan, yana son Umma Sabeera ma, amma dai halayyanta sai a hankali suna ɓata masa rai.
Mamina cigaba da rayuwanta tayi, wannan ya zo yau gobe kuma wani daban ya zo, ni har mamaki nake yi ma a ina Mamina ke samo wasu mutanen, gata nan dai ba wai mai yawan fita ba ce, amma kuma jama'a ne da ita kaman mai kasa kanta a tire ta fita da shi, Alhaji Mukhtar kuwa har yau bai zo gidanmu ba, kuma wannan karon ne kawai ya jima, dan wata har da sati guda kenan bai zo ba.
Tsakanin yaya babba da matarsa kuwa, mata da miji sai Allah, tuni suka shirya bayan ta gama ginɗaya masa sharuɗan ya fita harkan Banafsha, sannan ta basa haƙuri, shi dai kallonta kawai yake yana murmushin shiririta irin nata, in ba haukan kishi da ya rufe mata ido ba, ai da yana son Banafsha to ba ita zai aura ba, Banafshan zai aura tunda tare ta gansu, kawai ya amsa haƙurin ne ita ma ya bata sun dai-daita, tunda duk sun gaji da fushin da suke yi da juna.
Malam Abbo da Banafsha kuwa yanzu stakaninsu ba'a magana, ɗalibai har sun fara ƙus-ƙus ɗin soyayya Malam Abbo ke yi da Banafsha, Umaima ta samu Banafsha ta mata maganam, amma Banafsha ta nuna mata babu komai tsakaninsu, Umaima ma shiru tayi dai tana kallonsu, Banafsha kuwa duk bata kallon abinda ake nufi, ita ta ɗau hakan shaƙuwa ce kawai, yayinda Malam Abbo ke fama da zuciyarsa, kuma zuwa yanzu yana jin ba zai iya haƙura ba, idan bai bayyana mata ba zuciyarsa akwai mastala, shiri yake kawai gadan-gadan na tunkarar Banafsha ya baje mata sirrin ƙalbinsa.
Bayan sati biyu muka koma boko inda muka fara sabon aji, semester na farko a ajinmu na ƙarshe, in Allah ya yarda mun kusa gama College of health, ranan juma'a mun je school mun dawo ni da Umaima hankali kwance, mashine ya kawo mu har ƙofan gida, muna sauƙa na hangi motan Ya Danish, nice ma na kula da shi da yake na gane motan nasa, amma Umaima bata kula ba sai hira take mini, ina ganin motan naji haushi ta kama ni amma na kawar, muka yi sallama da Umaima ta wuce gidansu, na shige namu gidan, tun da na hangi mota danƙareriya a cikin gidanmu na ce to Alhaji ya samu zuwa kenan, ajiyan zuciya nayi na shige palourn da sallama, samunsa nayi shi kaɗai zaune a palourn yana waya, stugunnawa nayi na gaishesa ya amsa mini da kai kawai yana murmushi, dan da alama waya mai muhimmanci yake yi, miƙewa nayi na shige ɗakina.
Ya Danish da ya kwashe wata guda bai dawo ba, Abbaa ne ya ƙira sa yana buƙatan ganinsa idan bai zo ba zai saɓa masa, shiyasa ma ya zo wannan weekend ɗin, amma ba dan yaso ba, kuma bai haƙura ba shi sai ya koyawa Banafsha hankali.
Bayan na wasta ruwa na huta, fitowa nayi dan na samu abinda zan sakawa hanjaye na, da Mamina muka kusa yin karo tana ƙoƙarin shigowa ɗaki na, murmushi ta sakar mini ta ce, "Ai na ɗauka kin zama Amaryan ƙulle ne, abincinma sai na zo na ce ki ci."
Cunna baki nayi cikin shagwaɓa na ce, "Uhmn! Ai gani nan na fito Mamina."
A gaba Mami ta saka ni har palourn, abincin da ta ɗebo mini ta nuna min na zauna na ci, zama nayi tare da shagwaɓewa na ce, "Mami a bani a baki."
Girgiza kai kawai Mamina tayi ta ɗau cokalin ta fara bani a baki, a haka Alhaji da fitowansa kenan daga ɗakinsa ya same mu, wata dakakkiyar haɗaɗɗiyar shadda ya saka yayi mugun kyau, Mamina tun da ya fito ta ke ta binsa da kallo tana murmushi, nima murmushin nayi kai na a ƙasa, Mami ta ce, "Alhaji kyau haka kaman sabon ango."
Alhaji Mukhtar hannunsa ya zura cikin aljihun garensa ya ce, "Sabon angon ne ma Insha Allahu, nan ba da jimawa ba, angon Ramlatu."
Hararansa Mamina tayi, shi kuma idanuwansa ya mai da kai na, ya ce, "Yarinyata ya kamata yanzu dai ki dinga yi wa Maminki faɗa tunda kin girma, Maminki bata son ta haifa miki ƙanne, ko kema bakya so?"
Girgiza kai nayi a hankali na ce, "Ina son ƙanne."
Mami hararana tayi, Alhaji kuma murmushi yayi ya ce, "To yanzu dai na yi latti kada na rasa sallahn juma'an nan, bari idan na dawo za mu yi magana, ki labarta mini yanda musabaƙan naku ya tafi."
Daga ni har Mami a dawo lafiya kuka masa, sannan ya fice, Mami ta dubeni ta ce, "Faɗima kika ce kina son ƙanne?"
Da sauri na ɗaga kai ina murmushi na ce, "Eh Mamina, ki haifa mini ƙani namiji tukunna, sai ki haifa mini mace na dinga mata kisto, kinga nima na samu waɗanda zan dinga yiwa faɗa ina musu wasa, kuma ina cewa ni auntynsu ce."
Hararana Mami ta yi ta ce, "Da dai maganan ki haifa mini jikoki haka kikayi da ya fi, amma kibar batun ƙanne, ke kaɗai ma da Allah ya bani alhamdulillahi nagode masa, Allah miki albarka ya nuna mini aurenki, Allah stare mini ke ya stare miki mutuncinki."
Wani ɓoyayyen ajiyan zuciya na sauƙe, ina ƙoƙarin kokawa da tunanin da ke son zuwa mini, hamdala nake ta yi a zuciyana ina faɗin, "Ameen."
ââ
CAS Bunayd suna cin abinci amma hankalinsa gaba-ɗaya yana kan waya, General ne yayi gyaran murya ya ce, "My Man za mu ɓata fa."
Sosa ƙeya CAS Bunayd yayi ya rufe wayan, a hankali yake cin abinci cikin yanga kaman mace, sai da suka gama ci duka sannan suka tashi suka koma cikin palourn da ke nan a downstairs, babbar budurwan ce ta masto kusa da Bunayd ta ce, "Yaya yaushe za ka tuna promise da ka mana?"
Ɗagowa Bunayd yayi idanuwansa akan ƙanwar ta sa mai shekaru 19 ya ce, "Wanne alƙawarin fa Ramlah?"
Yarinyar marairaicewa tayi ta ce, "Yaya zuwa Kano fa, ka ce za ka kai mu wajan Majeeder."
Bunayd lumshe idanuwansa yayi, sannan ya buÉ—e su alaman irin ya mance ma da wannan maganan, ba tare da ya kalleta ba ya ce, "banda yanzu sai wani lokacin."
Kaman za ta yi kuka ta fara masa magiya, sauran yaran ma mastowa suka yi, suka saka shi a gaba kaman za su yi kuka, duk sun haÉ—a bakinsu suna cewa, "Please Our Air Force."
Gajiya da ihun nasu da yayi a kunnensa ya sanya shi haÉ—e fuska tare da buga musu wani irin mugun tsawa ya ce, "shut-off!!"
Wani irin zabura dukansu suka yi, suka sha nistojin suka koma gefe suka zauna, duk suna muzurai kaman ba su ke masa shagwaɓa yanzu ba, General da ke zaune a gefe yana kallonsu dariya yayi ya ce, "that's My Man, yaran nan duk basa ji gwanda ma ka daina musu dariya."
Momsee murmushi ta yi ta ce, "da rabon dai za ka sha kunya Dear.."
Bata gama rufe baki ba kuwa, Bunayd ya nunawa yaran gefensa duk suka masto, murmushi ya sakar musu ya ce, "Zan kai ku Insha Allah soon, muna zuwa za mu É—auko Majeeder ita ma ta dawo nan É—in, sai ku daina damun mutane da Majeeder-majeeder."
Dukkansu murmushi suka yi, ƙaramar ciki mai shekaru 14 ta rungume hannunsa ta ce, "Allah bar mana kai Yayanmu, Allah nuna mana matarka da yaranka."
Murmushi yayi ya shafa kanta ya ce, "Ameen Nabeela my love."