Sashe 6
Yar Karuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya DANISH ko kallo na yayi sai ya harare ni ko kaɗan baya ko son ganin ina shiga gidansu, shiyasa wani lokacin Mamina ke hanani amma Abbansu yakan stawatar masa shi da Ummansa akan su daina tsangwamata, amma Umma Sabeera in ta tashi sai ta kaada baki ta ce ai Abba so yake shima yabi karuwar Uwata, shiyasa yake haɗani da yarinyanta dan haka ba da ita ba sai tasa Ya Danish ya dinga dukan Umaima akan ta daina kula ni, amma Umaima ko me zai mata sai ta shigo gidanmu kuma sai dai in bata ganni ba sai ta mini magana, ran da aka ci sa'a Ummu na gida to ko me Umma Sabeera za ta ce bata bari ya Danish ya taɓa Umaima, dan tana sonta sosai wanda Umma Sabeera ke faɗin, wai soyayyan na munafurci ne.
Ya Danish mutum ne da bai damu da yawan magana ba, kawai dai in har ya ƙi abu to ya ƙi sa ne ko hanya baya son haɗawa da shi, wanda kuma abinda bai sani ba shine nikam ba iya shi na tsana ba gaba-ɗaya maza na tsane su a rayuwata, da ya kwantar da hankalinsa da stangwamata da yafi masa dan nima na stane shi fiye da tunanin mai tunani tun ranar da ya fara cemun ƴar karuwa, tun ranan ya fice mini a rai.
Ummu ganin Umaima ta shigo gida da ghdu kaman an biyo ta, sai leƙa bayan Umaima take yi dan taga wa ya biyo ta amma bata ga kowa ba, kallonta tayi ta ce, "Umaima lafiyanki kuwa? Ke da wa da gudu haka?"
Umaima na haki ta ce, "Ummu wallahi ya Danish ne ya biyo ni."
KaÉ—a kai kawai Ummu tayi ta ce, "Nasan za'a rina, wai an saci zanin mahaukaciya, to Allah ya kyauta kawai, Danish ko kaÉ—an baya ji bansan me Banafsha ta ci masa ba, dan nasan ba zai wuce dan ita ya biyo ki ba, wuce kije ki huta ki É—iba abinci a kitchen ki ci, shi kuma zai shigo ya same ni."
Amsawa Umaima tayi ta wuce cikin É—akinsu ta sauya kaya ta watsa ruwa tayi sallah sannan ta É—ibo abinci ta dawo palourn tana ci tana kallo sai ga Nana ta shigo, kallonta tayi ta ce, "Ke kuma daga ina?"
"Tayani tambayan ta dai", faÉ—in Ummu da ke zaune ita ma tana kallon.
Nana tura baki tayi ta ce, "Daga gidan babban yaya nake", tana faÉ—a ta wuce É—akin su.
Ni kuwa ina shiga gidamu na tarar Mamina tana shanya kaya na da ta gama wanke wa, rungumeta nayi na ce, "Sannu da aiki Mamina, maimakon ki bari idan na dawo nayi ko da gobe ne tunda bamu da class."
"Parrot daga dawowa sai surutu wuce ciki ai na gama wankin" faÉ—in Mamina tana min murmushinta mai stada.
Nima murmushin nayi na shige ciki ina jin farin ciki haka kawai bansan dalili ba, Uniform nawa na cire sannan na fito palourn namu na tarar komai a gyare staff ko ina sai tashin ƙamshi yake kawai, "Uhmn! Mamina kenan ga tsafta ga son ƙamshi, ga kuma kyau Allah barmun ke Uwata ya kuma dai-daita rayuwarmu", abinda na faɗa kenan na wuce kitchen namu, abinci na ɗibo shinkafa da miya da ya ji ice-fish ga coslow a gefe, ɗan kaɗan na ɗibo kaman an roƙo, wanda ko yaro aka bawa zai cinye tass bai ƙoshi ba, na dawo palour na zauna ina addu'an kar Mamina ta shigo ban fara ci ba ta gane ban ɗibo da yawa ba.
Nasa cokali zan fara ci sai kawai Mami ta shigo, rau-rau nayi da idanuwa na kana gani kaga na mara gaskiya, kallo É—aya Mami tamini da ni da plate É—in dake gabana ta girgiza kai ta wuce É—akin ta bata ce komai ba, ganin ta shiga É—aki da mugun sauri nima nayi nawa dakin, naci abincin na sha ruwa sannan na tashi na É—auro alwala nayi sallahn azahar.
Kyautan da Alhaji ya kawo min na jida na kai wa Mamina, nan ta dinga jin daɗi tana masa addu'a, sai ta ce, "Yauwa BANAFSHA kinga ma kin tuno min, dama ya ce na tambaya makarantar ku ana musabaƙa ne ko kuwa ba kwa yi, in bakwa yi sai a sanja miki wai dan musabaƙa na ƙara sa yaro zama mai hazaƙa da ƙoƙari."
"Uhmn! Mami nifa ban cika son musabaƙan nan bane, dan ana ce masa wai karatun riya ko kuma gasar karatu wanda aka maida shi tamkar abin jan fitina, a makarantar mu ana yi nice kawai bana so dan kwanaki ma Umaima ta ce mu yi naƙi, duk da kuwa malaman na zaɓan mu, amma sai mu bada uzuri."
Murmushi Mami tayi ta ce, "Eh tom kinga dai cewa kika yi wasu ne suke faɗin hakan, ba wai duka mutanen duniya ke faɗa ba, amma yanzu ke a me kika ɗauki musabaƙa akan ra'ayinki?"
"Ni Mami na ɗauke sa tamkar dai wata hanya da dama da ake bawa ɗalibi dan ganin yan inganta karatunsa, a zahiri za kayi karatu ne dan kar ka faɗi amma a ainafin niyar abun an saka shi ne dan ka ƙara mai da hankali akan karatu."
"Yauwa yarinyar kirki Nana Faɗima batoorler, kin fahimta da kyau haka nake so dama ako da yaushe tunanin ki yasha ban-ban da na sauran mutane, ta ko wacce siga ki kasance kin ɗauko halayyan mai sunanki, abinda nake so ki ƙara akan wannan tunanin naki shi ne ki ɗauko hadisi na farko a cikin arba'una Hadith ki ƙara a kai."
Kallon Mamina nayi na ce, "Mami hadisin na nufin dai komai ana yin sa ne da niya kuma komai kayi yana tafiya ne da niyan ka."
"Good girl! Kinga kuwa ashe in kika ƙuduri naki niyan daban ba dan riya ba ko gasa kinga ke daban saura daban, Allah subhanahu wata'ala yace "muna duba ne zuwa ga zuqatan ku ba jikkunanku ba" kinga kuwa abinda ka ƙudurta a zuciyanka shi ne abu na musamman da Allah zai tuhume ka akai."
Murmushi nayi cikin gamsuwa da zancen Mami na na ce, "Shikkenan Mami, na fahimta in Allah ya yarda zan gyara niya na."
"Yauwa ina so wani musabaƙan ya zama da ke aciki, sannan ki dage ta yanda al'umman Annabi SAW za suyi alfahari da haihuwanki, ki kulle idonki ki toshe kunnenki kawai ki fuskanci abinda kika sa a gaba inhar dai bai saɓawa mahaliccin ki ba, ki kula sosai a ko ina ki riƙe mutuncin kanki dan shi ne ƙimarki da darajarki a gidan mijinki, Allah ya miki albarka ya albarkaci dukkan rayuwanki FAƊIMAH."
Duk maganan da Mamina ke yi idanuwa na kan ta ina kallon ta ina mamaki a zuciyata da lamarin Mamina, anya lafiya? Mamina tana da ilimin boko da Arabic fiye da tunani na, Mami tasan hukuncin ko wanni laifi da ayar da aka sauƙe hukuncin barin ma dai Zina, amma me yasa Mami na ta zaɓi rayuwar karuwanci? Me yasa ta zaɓi take sanin ta? Me yasa ta kauda kai akan ayar Allah? Ta zaɓi zubar mana da mutunci akan adana mana shi, sannan sai tace na riqe mutunci na, koma dai menene addu'a ita ce maganin ko wacce iriyar cuta da musiban rayuwa, in Allah ya yarda ni kuma zan dage da kai kukana ga Allah na dage da addu'a...
Maganan da Mamina ke yi shi ya dawar da ni daga duniyan zancen-zuci zuci da na faÉ—a, "Banafsha me kike tunani haka? Cewar Mamina idanuwanta a kai na.
BuÉ—e baki na yi da niyan faÉ—a mata amma sai na kasa kawai na ce, "Mami ina tunanin assignment da aka bamu ne gashi hangout na yana wajan Umaima."
"To maza tashi kije ki karɓo daga nan ki gaida min Ummun ku."
Miƙewa nayi na tafi ɗakina dan saka hijab amma ina shiga ganin mayafin dogon rigan material dake jikina sai na fasa ɗaukan hijab, na ɗau mayafin tunda dai gidan su Umaima kawai zan je.
Ina fitowa Mami ta kalle ni ganin mayafi na saka ba hijab ba sai tace "Banafsha ke kuma ina za ki da mayafi ba hijabi?"
"Mami Allah ba inda zan je, iyakaci na gidan su Umaima kuma ina karɓa zan dawo."
Mamina ta ce, "Amma dai kinsan gidan su Umaima ba su kaÉ—ai bane ko, kinsan akwai maza ba iya mata ba ne, kuma ba muharramanki ba, yanzu ko muharraminka ma ba ko wani irin shiga ake so ka yi ya gani ba balle wanda ba muharraminka ba, maza koma ki sako hijabinki bana son shirme, yarinya ta girma bata san ya girma ba."
Marairaicewa nayi na ce, "Allah yanzun nan zan dawo Mamina."
"Tom maza kiyi sauri ki dawo, kinsan ba son fitanki da mayafi nake ba tunda kema kinsan ƙirar da Allah ya miki yarinyar fuk-fuk kaman kazar gona."
Murmushi nayi kawai na fice tun da dai ta barni na tafi hakan, amma inajin kunya dan nasan nufin Mami, Allah ya wadata ni da arziqin mazaunai wanda kaga ƙuguna ka ranste nasan maza, ƙirji na kuwa Masha Allah dan suma Allah ya azurta ni da su, shiyasa Mamina idan ta tashi take cemun kazar gona (brolas) fuk-fuk, ga shi idan ina tafiya komai na jikina mostawa yake, kuma dai ba rigima nake ba haka Allah yayo ni.
Da sallama na tura ƙofan gidan na shiga, kaina a qasa na tunkari hanyan shiga babban palourn gidan, ban ankare ba kawai na ji ni nayi karo da mutum, nayi baya zan faɗi haka wanda muka yi karon nan ko ya hanani faɗuwan ta hanyan tare ni, sai da na zauna da ɗuwawuna daɓass a ƙasa.
Ƴar ƙaramar ƙara na saki na ce, "Washh! Wayyo Allah!! Mamina mazaunaina sun yi targaɗe."